السبت، 15 ديسمبر 2018




Shinkafa tayi sanidiyyar mutuwan mutane a wajrn bauta

Home Shinkafa tayi sanidiyyar mutuwan mutane a wajrn bauta

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Yan sanda a kasar Indiya sun ce mutane 11 sun mutu, yayin da wasu da dama kuma ke ke kwance a asibiti bayan sun ci shinkafa a yayin wani taro da aka yi a wani wajen bauta.

Kusan mutum 70 yanzu haka ke kwance a asibiti bayan sun ci shinkafar.

Wani mai magana da yawun 'yan sandan, ya shaida wa BBC cewa akwai mutum 11 da ke ke halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai.

An dai kama mutum biyu bayan afkuwar lamarin, kuma wani jami'in lafiya ya shaida wa kafoffin yada labaran kasar cewa akwai yi wu war an gurbata abincin ne.Wani da ya halarci taron da aka yi a wajen bautar, ya shiada wa manema labarai cewa an ba su shinkafa da miya mai wari ne.

Ya ce, wadanda suka zubar da abincin ba su ci ba, ba bu abinda ya same su, amma duk wanda ya ci wannan shinkafar ya yi amai da ciwon ciki.

Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Jumma'a a wajen bauta da ke gundumar Chamarajanagar inda ake gudanar da biki na musamman.

Rahotanni sun ce an raba shinkafar ne a matsayin kamar wata kyauta ta musamman ko sadaka bayan kammala taron.

Mutane da dama daga makwabtan kauyen da aka gudanar da wannan taron ne suka halarci wajen, wanda kuma ywancinsu yanzu haka suna kwance asibiti, wasu kuma sun mutu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: