السبت، 22 ديسمبر 2018




Tarihin Umar M Sharif Mawakin Hausa Film “Full History Kanny Musician”

Home Tarihin Umar M Sharif Mawakin Hausa Film “Full History Kanny Musician”

غير معرف

Ku Tura A Social Media


Assalamu alaikum, sunana Umar Muhammad Sharif,
an haife ni a Rigasa da ke Jihar Kaduna a shekarar
1987. Na yi makarantar firamare da sakandare duk a
Rigasa.


Dalilin da ya sa na zabi sana’ar waka
Waka ta fado mini kwatsam da rana tsaka ne, amma
a gaskiya ban taba tunanin zan yi sana’ar waka ba,
saboda tun tasowata ni dalibi ne, ina karatun boko da
na addini, na ma fi ba da karfi a bangaren addini.
Silar fara waka kuwa ita ce akwai wata budurwa da
nake matukar so da kauna, amma na kasa sanar da
ita abin da ke zuciyata.


A gaskiya jin nauyin abin shi ne ya hana ni sanar da
ita. Nakan je har kofar gidansu, na aika a yi mini
sallama da ita, amma inda gizo ke sakar shi ne da
zarar ta fito don ganin wanda ke neman ta, sai na
buya, ta gama dube-dubenta daga nan idan ba ta ga
kowa ba sai ta koma gida.


To na yi hakan kusan har sau uku ba tare da samun
damar tsayawa da ita ba. Daga nan wata rana sai na
yi ta maza na ce zan ga abin da zai ture wa buzu
nadi.

Da na je sai na aika kamar yadda na saba amma sai a
wannan karon ba ta fito ba. Na yi ta jira amma shiru
kake ji.

To daga nan ne fa kamar wasa sai na fara yin waka a
kan halin da na samu kaina ciki. Daga kofar gidansu
na fara waka har na isa gida ban daina ba. Haka na yi
tayi duk lokacin na tuna da wannan baiwar Allah.


A cikin wannan halin ne sai na samu biro da takarda
na rubuta wakar. Akwai wani mawaki Ibrahim
Suleiman “Zaki” wanda ya kasance abokin yayana ne.
Kamar wasa da ya ga wakar kuma ya umarce na rera
ta. Bayan ya saurari wakar sai ya yaba kuma ya yi min
wasu gyararraki, kana ya karantar da ni kabli da
ba’adin waka. Daga nan ne fa na fara waka gadan-
gadan.


Kalubale
A Rauwata
Da farko na fuskanci kalubale daga gida, daga bisani
muka fahimtar da iyayenmu. Bayan ba su ga canji
daga irin tarbiyyar da suka yi mana ba, sai suka fara
sa mana albarka da fatan alheri. Shakka babu
addu’o’insu na tasirin sosai a kan nasarorin da muke
ci gaba da samu.

Wakokin da na yi

A kalla wakokina za su kai 700
Kundin Waka Gasu Kamar Haka
Akwai su kamar haka: ‘Duniya Ce’ da ‘Nadiya’ da
‘Shahuda’ da ‘Madubi’ ‘Mai Atamfa’ ‘Babbar Yarinya’
‘Wacece’ ‘Kalaman Bakina’ ‘Bako’ Da dai sauran su,
Bakandamiyat Wakokina
Ina fitowa a film, sannan nakan shirya nawa. Fina-
finan da na fito sun hada da: ‘Mahaifiyata’ da ‘Nas’.
Fina-finan da na shirya sun hada da: ‘Ba Zan Barki Ba’
’Ka So A So ka’ da ’Jinin Jikina ’ Sannan Akwai Wani
Film Dana Fito A Cikin sa a wannan shekarar Mai
suna Mansoor.


Burina

Ba ni da wani burina saboda ko yanzu kasuwa ta
watse dan koli ya ci riba. Sunana ya kai duk inda ba
ka zato, saboda na sha samun kira ta waya daga
Amurka da sauran kasashen duniya, wanda jama’a ne
masu sauraren wakokinmu ke yaba mana.
Iyali
Ina da mata daya Maryam Da Yaro Daya ana kiransa
Da Aliyu Ina Rokon Allah Ya Rayamanin Su Bisa Ga
Sunnah.. ameeen
Ku Dannah Kan Alamar Share Zuwa Ga Abukanku Na
Fabebook Ko Instagram Mungode…..

Share this


Author: verified_user

0 Comments: