Wasu mukarraban shugaban Najeriya sun mayar da martani dangane da matakin da hadakar jam'iyyun hamayya suka zartar na goyawa dan takarar babbar jam'iyyar hamayya ta kasar wato PDP, Atiku Abubakar baya a zaben 2019 da ke tafe a kasar.
Tun a watan Yulin da ya gabata ne jam'iyyun su fiye da arba'in suka hade tare da babbar jam'iyyar hamayyar ta PDP da zummar kwace ragamar mulki daga Shugaba Muhammadu Buhari na APC.
A makon da ya gabata shugaban bangaren da ke ikirarin shi ne na jam'iyyar APC ta gaskiya, wato rAPC, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa sun yanke shawarar marawa Atiku Abubakar baya ne saboda Shugaba Buhari ya gasa aiwatar da abin da aka zabe shi a kai.
Sai dai kalaman na Buba Galadima ya fuskanci taron dangi daga wasu 'ya'yan Jam'iyyarta APC da ke cewa matakin da hadakar jam'iyyun ta dauka ko kadan bai girgizasu ba.
A tattaunwarsa da BBC, ministan wasanni da harkokin matasa, Barrister Solomon Dalung, ya bayyana gamayyar jam'iyyun da taron guda ba zai iya huda fata ba.
Abin da ya sa nake yi wa PDP aiki - Buba Galadima
Buhari 'yana son yin watsi da kudirin dokar zabe'
Dalilan PDP na kaddamar da kamfen Atiku a Sokoto
Barrister Solomin ya kuma yi watsi da zarge-zargen da wasu ke yi cewa dan takarar Jam'iyyar adawa ta PDPn ya razana su.
Ya ce su hakarsu ce ta cimma ruwa, don wannan dama ce ta Atiku ya fito ya yi wa 'yan kasar bayani tasirin da ya yi a shekaru takwas da ya yi wa tsohon shugaba Olesugun Obasanjo mataimaki.
Ministan ya ambato wasu muhimman kadarori da aka sayar a zamanin mulkin tsohon shugaba Obasanjo wanda a cewarsa Atikun aka bai wa damar ya lura da hukumar tattalin arzikin Najeriya.
Ya kuma kara da cewa ga masu fargabar tarihi zai maimaita kansa su sauya tunani, domin Atiku Abubakar ko kadan ba zai iya kayar da su a zabe ba.
Akasarin wadanda suka fice daga Jam'iyyar APC halayensu ne ya kora su, don haka babu wani batun nuna kiyaya ko rashin nuna goyon-bayan da zai daga musu hankali, in ji min
0 Comments:
إرسال تعليق