الجمعة، 21 ديسمبر 2018




ZAFAFAN LABARAN DUNIYA

Home ZAFAFAN LABARAN DUNIYA

غير معرف

Ku Tura A Social Media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar sauka da tashin jirage ta duniya a filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja. Aikin wannan tasha na daga cikin tashoshi 4 da ka kulla yarjejeniyar gina su da lamunin dala miliyan 500 daga bankin EXIM na kasar Sin inda gwamnatin Najeriya ta ba da kason dala miliyan 100.

Tashar dai da a k ace ita ce mafi girma a Afurka, ta yamma,za ta iya daukar bakuncin akalla fasinjoji miliyan 15 a shekara. Tun bara dai a ka gudanar da inganra titin saukar jiragen sama na Abuja da hakan ya sanya kaura na dan lokaci zuwa filin jirgin sama na Kaduna.

A na kara samun bayanai yadda miyagun iri ‘yan fashi da makami kan aukawa matafiya daidai wata kwana a kauyen Gitata da ke jihar Nassarawa biyo bayan kashe tsohon babban hafsan rundunonin tsaron Najeriya AIR MARSHAL Alex Badeh.
Hanya daga Keffi zuwa Gitata hark an kwanar Bade a jihar Kaduna na ramuka da hakan kan hana direbobi ware mota sosai don gudun fasa taya. Gyara hanya daga Bade zuwa Gidan Waya zamanin gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi ya sanya matafiya daga Abuja zuwa Filato da can arewa maso gabas zabar hanyar da barin bin hanyar Keffi zuwa Akwanga zuwa FOREST har Hawan Kibo.
Gitata dai na tsakanin wasu madakatun binciken sojoji biyu da kuma can gaba akwai babban barikin sojoji na Shitu Alao da ke Keffi. Rahotanni dai sun nuna ‘yan fashin kan faki lokacin da sojoji ba sa nan sais u fito su bude wuta kan motocin matafiya kuma in mutum ya tsaya su yi awun gaba da shi.
Marigayi Alex Badeh a mota kirar Tundra ya gamu da ajali ne lokacin da ya ke dawowa daga gona inda miyagun iri su ka bude wuta kan motar sa da farfasa gilasan ta inda kuma albarushi ya same shi a ciki.*
*Gonar Badeh dai tafi kusa da anguwar Mararaba amma don rashin kyawun hanya a kan zaga ta kauyen Panda dab da Gitata da ke da madakatar binciken motoci ta soja. Sai daga bisani mutane su ka gano wanda a ka kashe Alex Badeh ne.

Biyu daga ‘yan takarar shugaban kasa na sauran jam’iyyu da ba APC ko PDP ba, sun yi muhawara a zauren tattaunawa da babban editan sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustapha ya shirya a Abuja.

Yan takarar Shittu Muhammad Kabir na jam’iyyar APDA da Yunusa Tanko na jam’iyyar NCP na da bambancin ra’ayi kan rashin sanya hannu kan dokar zabe daga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.*
*Shittu Kabir wanda duk da haka ya ce da gaske ya ke takarar, amma ya goyi bayan rashin sanya hannu a dokar da nuna hakan ka iya dagula lamuran zabe. A na sa bangare Ynusa Tanko na NCP ya ce bai ga dalilin rashin sanya hannun ba don APC ta amfana da yanayin tsarin a 2015 ta kada PDP.
Dukkan ‘yan takarar biyu sun shaidawa Aliyu Mustapha cewa ba su yarda a kira su ‘yan takarar kananan jam’iyyu ba, don su ma masu rejista ne daidai da APC da PDP da sauran su.

Kawayen Amurka sun ce da sauran aiki wajen tunkarar ‘yan tawayen DAESH a kasar Sham bayan shugaba Donald Trump ya dau matakin janye sojojin Amurka a kasar. Trump dai ya ce ba aikin Amurka ne ta zama ‘yar sandan yankin gabar ta tsakiya ba.
Trump dai a sakon TWITTER ya ce ba daidai ne Amurka ta yi ta kashe miliyoyin dala wajen kare kasashen da ba sa godewa wannan aiki ba. Nan take dai Burtaniya ta nuna har yanzu akwai sauran aikin gabanin aiyana kammala kawar da ‘yan DAESH.
Shi ma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce an samu nasarar rage karfin DAESH amma ba a kawar da kungiyar ba gaba daya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: