السبت، 12 يناير 2019




Alkalan Alakalan NAGERIA zai gurfana agaban kotu

Home › › Alkalan Alakalan NAGERIA zai gurfana agaban kotu

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Gwamnatin Najeriya ta bukaci Alkalin alkalan kasar mai sharia Walter Onnoghen ya dakatar da aikinsa kan zargin da ya shafi kin bayyana kadarorin da ya mallaka.
Wata sanarwa daga kotun da'ar ma'aikata, ta ce a ranar Litinin 14 ga watan Janairu, Alkalin alkalan zai gurfana gabanta a wani mataki da ake ganin na kokarin tube shi daga mukaminsa.

Jami'in hulda da jama'a na kotun da'ar ma'aikata Ibraheem Al-Hassan, ya tabbatar wa da BBC da shari'ar da za a soma ta Alkalin alkalan.
Ana sa ran kotun da zai gurfana ita ce za ta tube shi daga mukaminsa domin kada ya yi katsalandan ga shari'ar.

Laifuka shida ake tuhumarsa, dukkaninsu da suka shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.
Gwamnatin tarayya dai na zarginsa ne da saba wa dokar hukumar tabbatar da da'a ta Code of Conduct Bureau.


Rahotanni sun ce tun a ranar Juma'a aka sanar da shi kan laifukan da ake zarginsa da kuma bukatar ya gurfana gaban kotu a ranar Litinin.

A ranar 10 ga watan Nuwamban 2016 ne shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Walter Onnoghen a matsayin alkalin alkalai na riko kafin tabbatar da shi.

Wannan dai zai kasance shi ne karon farko da alkalin alkalan Najeriya zai gurfana gaban kotu kan zarginsa da aikata laifi.

A 2015 ne dai alkalin kotun da'ar ma'aikata mai shari'a Danladi Umar wanda ake sa ran zai jagoranci shari'ar mai sharia Onnoghen, ya yi watsi da tuhume-tuhume kan shugaban Majalisa dattawa Bukola Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: