Wannan Jarumi an Haifeshi a Kabul dake Afghanistan a 22 ga watan October, shekara ta 1937 Sunan Mahaifinsa Abdul Rahman Khan Ya fito daga Kandahar Ita Kuma Mahaifiyarsa Iqbal Begum Daga Balochistan Daga Pakistan Sannan yana da yan uwa guda uku Shams ur Rehman, Fazal Rehman da kuma Habib ur Rehman.
Kader khan ya kasance Jarumi, Marubucin Labari da Maganganu kuma yana bada umarni Sannan yana Barkwanci.
Kader khan ya kasance Mahaddacin Alqur'ani ne Hakan ne yasa Da ya tsinci kansa a Harkar Bollywood ya zama Fasihin Marubucin Zababbun maganganu masu Hikima (Dialogues)
Ya fito a Fina-Finai Sama da 300 sannan ya rubuta dailogues na fina-finai Sama da 250.
Yafi fitowa da Jarumai irinsu Rajesh Khanna , Jeetendra ,
Feroz Khan, Amitabh Bachchan, Anil Kapoor ,Govinda.
Wadanda Suka fi yi masa Films Sune kamar K.Raghavendra Rao , K. Bapaiah , Narayana Rao Dasari, David Dhawan.
Ya kan fito tare da masu Barkwanci Musamman Asrani , Shakti Kapoor da kuma Johnny Lever.
Sannan yana yawan fitowa tare da Amrish Puri, Prem Chopra da Anumpha Kher.
Yana yawan fitowa a matakai Daban daban musamman matsayin Me taimakawa Jarumi Kamar Mahaifi, Kawu, Dan Uwa, Mugu Sannan a me Barkwanci.
a wasu Films din da ya taka karamar rawa watau be samu dama sosai ba sune Dil Diwana, Goonj, Umar Qaid, Mukti, Chor Sipahee, Muqaddar Ka Sikander
Sannan a wadanda yafi taka rawa ya fito tare da Rajesh Khanna Irin su Mahachor, Chailla Babu, Fiffty Fiffty, Maqsad, Naya Kadam da Nasihat.
Ya fito a mugu watau me yiwa Jarumi da baibayi ya hanashi Sakat a irin su Parvarish, Dhan Dhaulat, Lootmaar, Qurbani, Bulundi, Meri Awaaz Suno, Sanam Teri Kasam, Naseeb da Naukar Biwi Ka.
a fina-finan da ya fito a me Barkwanci sun hada. Sikka, Kishen Kanhaiya, Hum, Ghar Parivaar, Bol Radha Bol Duk wadannan a wajen 80s ne amma ya dora a 90s da wasu films irin su Aankhen, Taqdeerwala, Main Khiladi Tu Anari, Dulhe Raja, Coolie No.1, Saajan Chale Sasural, Sooryavamsham, Judaai, Aunty No.1 da Bade Miyan Chote Miyan, Raja Babu, Khudaar, Chote Sarkar, Judaai, Aunty No. 1, Gharwali Baharwali, Hero Hindustani, Sirf Tum, Anari No.1. Haka a 2000s ya ci gaba da irin su Akhiyon Se Goli Maare, Chalo Ishq Ladaaye, Suno Sasurjee, Yeh Hai Jalwa da Mujhse Shaadi Karogi.
Ya Rubuta Dialogues acikin Fina-Finai da Akayi Nasara dasu irinsu Meri Awaaz Suno, Angaar, Jail Yatra, Satte Pe Satta, Katilon Ke Kaatil, Waqt Ki Awaz, Coolie No. 1 , Main Khiladi Tu Anari , Kanoon Apna Apna , Karma ,
Sultanat, Baap Numbri Beta Dus Numbri, Humshakal,Saajan Chale Sasuraal, Hero Hindustani, Aunty No.1 Da Rajaji.
Haka ya Rubutawa Babban Tauraro na Lokacin watau Rakesh Roshan Dialogues a wasu Films dinsa Kamar Khoon Bhari Maang, Kala Bazaar, Khudgarz.
Fina-Finansa na karshe Tevar (2015), Lucky: No Time for Love (2006) da Family: Ties of Blood (2006).
Ya Samu Kyautar Filmfare Guda Uku:-
1982: Filmfare Award for Best Dialogue for
Meri Awaaz Suno
1991: Filmfare Best Comedian Award for
Baap Numbri Beta Dus Numbri
1993: Filmfare Award for Best Dialogue for
Angaar.
Yana da Yan Uwa a kasar Netherlands da Canada inda yake yake da yara gudu uku Sarfaraz Khan, Shahnawaz Khan Na ukun Shine yake zaune a Canada.
Wannan Kadan Daga Tarihin Wannan Jarumi.
By AbbaIndiaDala
0 Comments:
إرسال تعليق