Nafisa Abdullahi, ta fayyace dalilin da ya sa ta daina soyayyya da abokin sana'arta, jarumi Adam A. Zango, bayan daukar tsawon lokaci ba sa tare
- Nafisa ta ce Allah ne ya kawo karshen soyayyar tasu kamar yadda dama shi ne ya hadasu, zama ne kawai ya zo karshe
- A baya dai an sha zargin alakar soyayya tsakanin Nafisa da Adam Zango inda aka sha ganinsu tare a bainar jama'a da kuma fina-finai masu yawa
Nafisa Abdullahi, shahararriyar jarumar fina-finan Hausa a masana'antar fim ta Kannywood, ta fayyace dalilin da ya sa ta daina soyayyya da abokin sana'arta, jarumi Adam A. Zango, bayan daukar tsawon lokaci ba sa tare.
Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da BBC, inda ta kara da cewa dama Allah ne ya hada su kuma yanzu ya raba su.Komai yana faruwa ne cikin tsari da hukunci na ubangiji, kusan shekaru hudu yanzu ke nan ko zuwa biyar ba ma tare. Allah ne ya kawo karshen soyayyar tamu kamar yadda dama shi ne ya hadamu. Zama ne kawai ya zo karshe," cewar Nafisa.
Nafisa Abdullahi: Dalilin da ya sa na daina soyayya da Adam A ZangoNafisa Abdullahi: Dalilin da ya sa na daina soyayya da Adam A Zango
Source: UGC
Har ila yau an tambaye ta ko yaya yanayin alaka yake yanzu a tsakaninta da shi. Sai cewa ta yi: "A yanzu babu wata alakar soyayya a tsakaninmu, abokin aikina ne kawai. Idan bamu hadu a wani wuri ba, to zamu hadu a wani duk da cewa mun fi yin aiki tare a baya kuma an fi ganinmu tare, amma yanzu abubuwa da dama sun sauya."
A baya dai an sha zargin alakar soyayya tsakanin Nafisa da Adam Zango inda aka sha ganinsu tare a bainar jama'a da kuma fina-finai masu yawa da suka taka rawa tare a matsayin jarumai.




0 Comments:
إرسال تعليق