الاثنين، 7 يناير 2019




Sojoji sun hambarar da gwamnatin Ali Bongo a Gabon

Home Sojoji sun hambarar da gwamnatin Ali Bongo a Gabon

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Sojoji a Gabon sun ce sun hambarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo, wanda iyalan gidansa suka shafe shekara 50 suna mulkin kasar mai arzikin man fetur.

Sojojin kasar da ke yankin yammacin gabar tekun Afirka ta tsakiya sun ce sun kaddamar da juyin mulki ne "domin dawo da demokradiyya".

Su karbe iko a babbar tashar talabijin ta kasar da karfe 4 na asuba agogon kasar (Karfe 3 GMT), kuma sun karanta wata gajeriyar sanarwa da ta bayyana cewa sun kafa "Majalisar Ceton Kasa".Shugaba Ali Bongo ya dare bisa karagar mulki a 2009 kuma ya shaf fiye da wata biyu yana jinya a wajen kasar.

Rahotanni na cewa Shugaba Bongo ya sami matsalar shanyewar wani bangare na jikinsa ne a Oktoba kuma yana karbar magani a kasar Maroko.

A sakonsa na sabuwar shekara shugaban ya yi wa al'ummar kasar jawabi ta kafofin watsa labarai domin gamsar da su inda ya ce yana samun sauki.

Sojojin sun ce jawabin nasa bai gamsar da su ba, inda suka ce "wannan wani kokari ne na kankamewa ga mulki".

Tashar Radio France Internationale ta ruwaito sojojin da suka yi juyin mulkin na ba takwarorinsu umarni da su karbe ikon sarrafa harkokin sufuri na kasar da rumbunan ajiye makamai da filayen jirgin sama na kasar "domin amfanin kasar".

Share this


Author: verified_user

0 Comments: