الخميس، 21 فبراير 2019




Babu Wanda Zai Mani Kawanya Idan Na Hau Kujerar Shugaban Kasa - Atiku

Home Babu Wanda Zai Mani Kawanya Idan Na Hau Kujerar Shugaban Kasa - Atiku

غير معرف

Ku Tura A Social Media
Dan takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai bari wasu mutane da ake kira da ‘cabal’ su mulki gwamnatinsa ba idan har ya lashe zaben ran Asabar, 23 ga watan Fabrairu.
Atiku, wanda ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 23 na jihar Kaduba, yace gaba daya juya gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu ke yi, inda yayi zargin cewa hakan ne ya sanya kasar cikin kangin wahala da wuya da take ciki a yanzu.
Atiku yace ko kadan PDP ba za ta yarda da sace akwatunan zabe ba kuma ba za ta dauki kowani mataki da ya saba doka ba, inda yace bayar da umurnin kashe duk wanda ya sace akwatin zabe ba damokradiyya bane.
Tsohon mataimakin Shugaban kasar yace idan har aka zabe shi a ranar Asabar mai zuwa toh zai siyar da NNPC domin samar da Karin ci gaba, inda yace a yanzu mutane kalilan ne ke amfana daga ayyukan kadarorin kasar maimakon yan Najeriya baki daya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: