الاثنين، 11 فبراير 2019




Kungiyar Tijjaniyya Movement Ta Yi Kira A Zabi Buhari

Home Kungiyar Tijjaniyya Movement Ta Yi Kira A Zabi Buhari

غير معرف

Ku Tura A Social Media
Kungiyar Tijjaniyya SUFI Movement ta yi kira ga mabiyanta a duk fadin Nijeriya cewa a sake zabar Buhari karo na biyu, domin an gwada shi an ga kuma nagartarsa.
A jawabin da kungiyar ta fitar ga manema labarai, shugaban kungiyar na kasa , Timasaniyu Ahmed-Rufai, ya ce sake zabar Buhari a Nijeriya alheri ne bisa ayyukan alkairan da ya shinfidawa kasar nan.
Kungiyar ta kuma lissafo dalilanta na tsayar da Buhari a matsayin dan takarar da za su zaba saboda ayyukan hanya da na ci gaban al'umma da aka yi karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: