الجمعة، 5 أبريل 2019




An ayyana dokar ta baci kan mummunar gobarar daji a Koriya Ta Kudu

Home › › An ayyana dokar ta baci kan mummunar gobarar daji a Koriya Ta Kudu

غير معرف

Ku Tura A Social Media

 

 

 

A kalla mutum daya ne ya mutu, yayin da aka ceto fiye da mutum 40,000.

 

Koriya Ta Kudu ta ayyana dokar ta baci don shawo kan wata mummunar gobarar daji mafi muni a tarihin kasar.
A kalla mutum daya ne ya mutu, yayin da aka ceto fiye da mutum 40,000.
Dubban sojoji ne ke taimaka wa 'yan kwana-kwana daga fadin kasar don kashe gobarar da ke ci a yankin arewa maso gabashin kasar mai yawan tsaunuka, da ke kusa da kan iyakar kasar da Koriya Ta Arewa.
Duk da cewa an shawo kan gobarar daga ainihin inda ta fara ci, har yanzu ana faman kasha sauran wuraren da ta kama, kamar yadda jami'ai suka ce.
An yi amannar cewa gobarar, wacce ta tashi ranar Alhamis da dare, ta fara ne daga tartsatsin wuta da wata taransufoma ta yi kusa da Goseong da gundumar Gangwon, arewa maso gabashin babban birnin kasar Seoul.


Daruruwan gidaje ne wutar ta kone 

 

Iska mai karfi ta taimaka wajen rura wutar, inda ta yi saurin yaduwa a yankin tsaunukan inda a nan ne aka yi Gasar Wasannin Olympics ta hunturu a bara, da kuma biranen Sokcho da Gangneung, a cewar jami'ai.
Fiye da injinan kashe gobara 800 aka kai daga fadin kasar don kashe gobarar, yayin da wutar ta lalata daruruwan gine-gine a gundumar.
Shugaba Moon Jae-in ya yi taron gaggawa tare da kiran jami'ai su kai dukkan abubuwan da ake bukata don shawo kan lamarin.
Ministan tsaro na kasar ya ce an kai sojoji 16,500 da helikwaftan sojoji 32 da manyan motoci na kashe gobara 26.
"An yi matukar sa'a an shawo kan wutar daga inda ta fara tashi," a cewar gwamnan yankin Choi Moon-soon, wanda ya fadi hakan a wata hira da ya yi da wani gidan rediyo, amma ya kara da cewa har yanzu wutar na ci a wasu wuraren.
Gwamnati ta ce tuni aka shawo kan gobarar a yankin Sokcho, yayin da aka shawo kan kashi 50% cikin %100 na wutar a yankin Gangneung.

 

 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: