الأربعاء، 3 أبريل 2019




An yi wa Buhari ca kan nuna alhinin wanda aka kashe a Lagos

Home › › An yi wa Buhari ca kan nuna alhinin wanda aka kashe a Lagos

غير معرف

Ku Tura A Social Media

An yi wa Buhari ca kan nuna alhinin wanda aka kashe a Lagos

 

'Yan Najeriya da dama sun yi caa da suka kan Shugaba Muhammadu Buhari, kan alhinin da ya nuna na mutuwar wani mutum a Legas, suna masu zargin shugaban da cewa ya yi buris da halin da al'ummar jihar Zamfara ke ciki na kashe su da ake yi a kusan kowace rana.
Shugaban Buhari dai ya jajanta wa iyalai da abokan arzikin Mista Kolade Yusuf da ake zargin 'yan sanda ne suka kashe a Legas a ranar Lahadi.
A wani sako da fadar shugaban kasar ta wallafa a Twitter ranar Litinin, ta bayyana cewa wadanda ake zargi da kisan an kama su kuma suna fuskantar tuhuma kan lamarin.


Sai dai wannan sakon jajen na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotanni na kisan gilla da 'yan fashi ke yi a Zamfara da kuma wasu sassa a Najeriya, tare kuma da sace mutane don neman kudin fansa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Bayan da fadar shugaban kasa ta wallafa wannan sako a shafinta naTwitter, jama'a da dama sun ta kawo suka kan zargin bambancin da shugaban ke nunawa.









Akasarinsu sun bayyana cewa an yi kashe-kashe a Zamfara da wasu wurare amma shugaban bai jajanta ba ko da a shafukan sada zumunta.
Sai dai BBC ta yi kokarin jin ta bakin fadar shugaban kasar kan korafin na jama'a amma abin ya ci tura.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: