Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi.
Tayin da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kammala kacaccala jihar zuwa masarautu biyar, sai gashi diyar Sarkin Kano, Fulani Siddika ta yiwa gwamnan raddi akan abinda ya yiwa mahaifinta
Bayan kaddamar da karin masarautun yanka guda hudu a Kano da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi, 'yar gidan Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ta yi wani raddi a shafinta na Instagram.
A bayanin da ta yi, duk da yake an goge, amma 'yar uwarta Fulani Siddika, ta sake sanyawa, inda ta bayyana gwamnan Kano Ganduje a matsayin "Bala'i da Allah ya kawowa mutanen Kano".
'Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi
Ga abinda ta ce a shafin nata:
"Idan kuna so ku ga me rashin asali ke jawo wa ku duba ku ga abinda Ganduje yake yi a Kano. Mutumin da bashi da wata daraja, amma yana kokarin ya ja da mutanen da suke da daraja. Ina addu'ar Allah yasa kada mahaifiyata ta ce na goge wannan bayanin a shafina. Ganduje shi ne bala'in da yafi komai a jihar Kano. Abinda yake yi a gwamnatinsa, son rai ne kawai a ciki. Bamu kamaci gwamnati irin wannan ba. Allah ya raba mu da masifar Ganduje dan kuwa mutanen da basu da asali sune suke bata masu asali.
Bugu da kari, Shahida ta kara rubuta cewa, Da zarar Sarki ya tsorata da rasa kujerar sa, abinda yake yi shine ya sauke kansa,
Babu shakka a cikin bayanin da ta yi a shafin nata Fulani Siddika, ta rubuta cewa
Ba ni da wani abu da zan cegaskiya!" 'Yar'uwata ce ta fada duka.
Sources:hausaloaded
السبت، 11 مايو 2019
Author: غير معرف verified_user
RELATED STORIES
Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi.Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi
Rabi,u sheriff usman baba Allah yayi masa rasuwa a yau hudu ga watan ramadan.Rabi,u sheriff usman baba Allah yayi masa rasuwa
CJN, Mohammed ya yi rantsuwa a cikin shugabanni 250, mambobi ne na Kotun Tsarin MulkiCJN, Mohammed ya yi rantsuwa a cikin shugabanni 2
House of Reps ya ci gaba da karantawa na biyu na
Littafin Mijin Ummata Kashi Na Shida Zuwa Kashi Na Gwoma😍📚 MIJIN UMMATA littafi Na SHIDA 😘📖% Yana cik
Gwamnatin ganduje ne ta fara kammala ayyukan da ta gada Gwamnatin mai girma Dakta AbdullahiUmar Ganduje O
0 Comments:
إرسال تعليق