الخميس، 4 يناير 2018




Dandalin Kannywood: Babban buri na shine inyi aure, in zama uwa - Rahma Sadau

Home Dandalin Kannywood: Babban buri na shine inyi aure, in zama uwa - Rahma Sadau

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Fitacciyar jarumar nan dake yin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau ta bayyana wa duniya babban burin ta a rayuwa a halin yanzu.

Jarumar dai ta bayyana cewa ita yanzu bata da burin da ya wuce tayi aure sannan ta kuma haihu ta zama uwa.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne lokacin da take bayar da ansa ga masoyan ta da ta damar yi mata tambaya a shafin ta na dandalin zumuntar zamani na Instagram a kwanan baya.

An tambayeta wanda ya koyamata rawa?


Ta amsa cewa “Ali Nuhu.”

Me ta fi jin tsoro a duniya?

Ta ce “mutuwa.”

Yaushe za ta yi aure?

Ta ce “kwanannan,” amma bata bayyana ko wanene saurayin nata ba.

Shin za ta iya daina fim?

Ta ce “a’a.”

Dan wasan da ya fi birgeta a masana’antar fina-finan Hausa

Ta ce “Sadiq Sani Sadiq.”

Fim din da ta yi wanda ta fi so, ya fi birgeta

Ta ce fim din turanci na “Sons of the Caliphate”

An tambayeta ko shekarunta nawa?

Ta ce, “24.”

Share this


Author: verified_user

0 Comments: