Sai dai jarumin ya bayyana wani abun al'ajabi da ya taba cin karo da shi a dalilin sana'ar sa inda ya ce wata tsohuwa ta taba tsine masa saboda rawar da yake takawa a fina-finan sa.
Arewatop.com ta samu cewa jarumin ya bayar da wannan labarin ne a cikin zantawar da yayi da wata mujallar dake kawo rahotannin lamurran Kannywood din.
Jarumin ya bayyana cewa akwai wani lokacin da suke daukar shirin su na fim inda wata tsohuwa ta tsine masa albarka.
Ya kara da cewa a lokacin kuma da ya tambayeta ko menene dalilin hakan sai 'yar da ke tare da tsohuwar ta ce masa saboda ya cutar da jaruma Hadiza Gabon a cikin fim din 'Daga Ni Sai Ke'.
0 Comments:
إرسال تعليق