الثلاثاء، 7 أغسطس 2018




Yanzu yanzu: Mukaddashin shugaban kasa ya tsige shugaban hukumar DSS

Home Yanzu yanzu: Mukaddashin shugaban kasa ya tsige shugaban hukumar DSS

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Rahoton da muke samu da dumi duminsa shine mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsige shugaban hukumar tsaro ta sirri, wato DSS, Malam Lawal Daura daga mukaminsa biyo bayan farmakin da jami’an hukumar suka kai majalisar dokokin Najeriya da safiyar ranar Talata 7 ga watan Agusta.

NAIJ.com ta ruwaito Kaakakin mataimakin shugaban kasa Osinbajo, Laolu Akande ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 7 ga watan Agusta.

Haka zalika hadimin shugaban kasa Buhari akan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya tabbatar da fatattakar Lawal Daura daga aiki.

Bugu da kari, Farfesa Osinbajo ya umarci Lawal Daura ya mika ragamar tafiyar da hukumar ga jami’I mafi girma a hukumar, har sai baba ta ji.

Lawal Daura

Idan za’a tuna, da safiyar yau ne jami’an DSS suka tare kofar shiga majalisar dokokin Najeriya, inda suka hana wasu Sanatocin jam’iyyar PDP shiga farfajiyar majalisar, duk da cewa majalisar na hutu, har sai watan Satumba za’a bude ta.

Sai daga daga bisani bayan yan majalisun sun matsa, jami’an sun bude musu hanya, wannan tataburza da aka sha tsakanin Sanatoci da Jami’an DSS ya biyo bayan jita jitan da ake yadawa na cewa wai Sanatocin APC zasu tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: