الجمعة، 12 أكتوبر 2018




Labarai › Ziyarar Da Na Kaiwa Obasonjo Koyarwar Manzon Allah Ne — Sheik Gumi

Home Labarai › Ziyarar Da Na Kaiwa Obasonjo Koyarwar Manzon Allah Ne — Sheik Gumi

غير معرف

Ku Tura A Social Media


Malamin addinin Musuluncin nan mazauni Kaduna, Sheik Ahmad Gumi ya yi karin haske kan ziyarar da ya kaiwa Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasonjo inda ya nuna cewa ziyarar na daga irin koyarwar Manzon Allah.

Sheik Gumi ya ce Manzon Allah ya taba cewa yana matukar maraba da duk wata gayyata na yin sulhu ko da tsakanin wanda ba Musulmi ba ne. Ya kara da cewa idan har shugabanni na cikin zaman lafiya, to ana sa ran kasa ma za ta kasance cikin zaman lafiya.

Ya ce ya zama dole ya je domin ganin an wanzar da zaman lafiya a fadin kasar. Ya jadadda cewa shi bai ce a zabi wani ba kawai sulhu ya je. 

Malamin ya kara da cewa ko gobe aka kira shi yin sulhu zai je. Ya jadadda cewa masu fadin cewa an bashi dala, kage ne cewa babu wanda ya bashi kudi shi saboda Allah yayi. Ga cikakken biyon bayanin nasa a kasa: 


Share this


Author: verified_user

0 Comments: