Kwamitin nan na musamman da Shugaba Buhari ya kafa domin kwato kadarorin gwamnati dake a hannun ma'aikatan gwamnati ya ce ya samu nasarar kwato akalla Naira biliyan 4, dala miliyan 7 daga hannun barayin gwamnati.
Shugaban kwamitin da aka dorawa alhakin kwato kadarorin, Mista Okoi Obono-Obla shine ya sanar da hakan ga manema labarai a ofishin sa a garin Abuja.
A cewar sa, kimanin dalar Amurka miliyan 7 ce aka samu a cikin wani asusun ajiya na bankin Heritage da wani tsohon jami'in gwamnati ya boye wadanda kuma kudin na haram ne. Ya kara da cewa sauran kudaden suma an gano su ne a sauran bankunan kasar wanda tuni har an soma bin hanyar da ta dace wajen maida su inda ya kamata. A wani labarin kuma, Sarkin masarautar Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi kaca-kaca da gwamnonin Arewacin Najeriya game da daukar dukiyar al'umma da sukeyi suna anfani da ita wajen biyawa wasu tsiraru kujerar Makka duk shekara.
Sarkin yayi wannan tsokacin ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron bita na lalubo hanyoyin da za'a rage yawan yaran da basu zuwa makaranta a yankin na Arewacin Najeriya da aka kammala a ranar Alhamis.

0 Comments:
إرسال تعليق