A cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawari idan mutanen Nijeriya su ka sake zaben sa a wani karon a 2019, za su ga gagarumin canji a fadin kasar nan.
Shugaban kasar ya nuna cewa Nijeriya za ta canza muddin aka sake ba sa wani daman a zabn 2019. Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga ‘Yan siyasan kasar da su yi yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Buhari ya bayyana wannan ne lokacin da yake jawabi game da sabon tsarin Jam’iyyar APC da manufar su na 2019 mai taken ‘Next Level’.
Shugaban kasar ya yi wannan kawabi ne a wani katafaren daki da ke fadar Shugaban kasa na Villa.
Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa shekaru 4 masu zuwa, su na da matukar tasiri kan tattalin arzikin kasar nan. Buhari yace Gwamnatin sa za ta bunkasa tattalin arziki ta kuma yi wa jama’a aiki idan har ya zarce a kan karagar mulkin kasar.
0 Comments:
إرسال تعليق