الأحد، 2 ديسمبر 2018




Shugaban kasa muhammad buhari ya karyata jita jitanda akeyi akanshi

Home Shugaban kasa muhammad buhari ya karyata jita jitanda akeyi akanshi

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a ganawar da ya yi da al'ummar Najeriya mazauna kasar Poland a birnin Krakow a ziyarar da ya kai kasar domin halartar taron sauyin yanayi na Majalisar dinkin duniya.

Wani dan Najeriya ne ya yi masa tambaya a kan cewa shin da gaske ne cewa shi ne Buhari da aka sani ko kuma wani ne ke kwaikwaiyon sa da ake kira Jibril daga Sudan.

Sai dai shugaba Buhari ya soki masu yada wannan jita-jita, da wadanda "ba su san ya kamata ba, kuma abu ne da ya sab awa koyarwar duk wani addini

"Mutane da dama sun dauka cewa zan mutu a lokacin da na yi rashin lafiya. Wasu daga cikin su sun rika zuwa wurin mataimakin shugaban kasa suna kamun kafa domin ya ba su mukamin mataimakin shugaban kasa saboda sun dauka na riga na mutu".

Wannan ya sa mataimakin shugaban kasa ya rika jin wani iri, kuma sai da ya ziyarce ni a birnin Landan. Amma ina son na tababbatar ma ku da cewa ni din ne dai, in ji shugaba Buhari.

Shugaban na Najeriya ya ce fatansa shi ne ya gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa a ranar 17 ga watan Disamba, lokacin da zai cika shekara 76 da haihuwa.

"Ina son na tabbatar ma ku da cewa ni ne kuma nan ba da jimawa ba zan yi bikin cika shekara 76 da haihuwa, kuma har yanzu da sauran karfi na."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: