A yau Laraba ne ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019 ga yan majalisar dokoki.
Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin ne kasa da wata bakwai bayan ya sanya hannu a kasafin kudin 2018.
Dan majalisar dattawa, Sanata Kabiru Gaya, ya shaida wa majiyar BBC cewa suna sa ran kasafin da shugaban zai gabatar zai zarta na 2018, wato naira tirilyan 9.12.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta aiwatar da fiye da rabi na kasafin kudin da ya gabata, musamman a fannin ayyuka.
An sha kai ruwa rana tsakanin 'yan majalisar dokokin da shugaban kasa game da kasafin kudin shekarun da suka gabata.
Shugaba Buhari ya dade yana zargin 'yan majalisar da sanya ayyuka na son rai a kasafin kudin da yake gabatar musu, ko da yake su ma sun ce aikinsu ne tsefe kundin kasafin domin ganin an yi wa kowanne bangare na kasar adalci.
Wannan dai shi ne kasafin kudi na karshe da Shugaba Buhari zai gabatar wa 'yan majalisar gabanin babban zaben kasar da za a yi a watan Fabrairu.
0 Comments:
إرسال تعليق