Yar takarar mataimakiyar shugaban kasa a jam'iyyar ANN, Khadija Abdullahi, ta ce sam bata gamsu da tambayoyin da masu shirya muhawarar da aka yi tsakanin manyan 'yan takarar mataimakin shugaban kasa a Najeriya suka yi ba a ranar Jumma'ar data shude.
Khadija Abdullahi, ta shaida wa BBC cewa, a cikin tambayoyin da aka yi wa 'yan takarar mataimakan shugaban kasar a yayin muhawarar, ba a tabo wasu muhimman batutuwa ba.
Ta ce batutuwan da suka shafi ilimi da Boko Haram da dai sauransu, duk ba a tabo su ba, sai batun tattalin arziki kawai.Yar takarar ta jam'iyyar ANN, ta ce batun tattalin arziki batu ne mai kyau, amma kuma ba shi ne kadai ne ya damu 'yan Najeriya ba.A ranar Jumma'a 14 ga watan Disambar 2018 ne, aka yi muhawara a tsakanin manyan 'yan takarar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.
'Yan takarar da suka halarci muhawarar sun hadar da Ganiyu Galadima na jam'iyyar ACPN, da Khadija Abdullahi ta jam'iyyar ANN da kuma Yomi Osinbajo na Jam'iyyar APC.
Sauran sune Peter Obi na Jam'iyyar PDP da kuma Umma Abdullahi Getso ta jam'iyyar YPP.
'Yan takarar sun kwashe kusan sa'o'i uku a tsaye suna amsa tambayoyi kan batutuwa daban daban da suka jibanci tattalin arziki da samar da ayyukkan yi,da ababen more rayuwa, da manufofinsu na hulda da kasashen wajen da kuma matsayin mataimakin shugaban kasa a siyasar Najeriya da dai sauransu.
Sai dai a yayin da ake daf da soma muhawar wasu magoya bayan jam'iyyar AAC ta Omoyele Sowore, sun yi zanga-zanga a kofar zauren da aka yi taron kan rashin zaben dan takararta a cikin wadanda za a yi muhawarar.
Mr. Jude Eya, jagoran masu zanga-zangar ya ce ba sun je fada ba ne ko ta da hankali, sun zo ne su shaida wa duniya cewa an yi musu rashin adalci da kin saka su a cikin wannan muhawarar.
To sai dai shugaban kungiyar da ta shirya muhawarar Eddie Emessiri, ya ce zaben wadanda za su shiga muhawarar shi ne abu mafi wahala a cikin tsare-tsaren shiryata.
Amma in ji shi an yi zaben ne a kimiyance kuma bisa adalci da gaskiya.
Wannan muhawarar dai share fage ce ga wadda za a yi tsakanin manyan 'yan takarar shugabancin kasar wadda za a yi ranar 19 ga watan Janairun shekara mai kamawa.
0 Comments:
إرسال تعليق