السبت، 15 ديسمبر 2018




Rundunar Sojin Najeriya ta yi amai ta lashe a kan UNICEF

Home Rundunar Sojin Najeriya ta yi amai ta lashe a kan UNICEF

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Rundunar sojin Najeriya ta soke matakin dakatar da ayyukan asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF a arewa maso gabashin kasar kamar yadda ta sanar da farko.

Rundunar dai ta zargi UNICEF da zagon-kasa ga kokarin da sojoji ke yi na yaki da Boko Haram ta hanyar horarwa da kuma tura 'yan leken asirin Boko Haram.

Sai dai a yanzu kusan ana iya cewa rundunar ta yi amai ta lashe, bayan wani taron gaggawa da ta ce ta gudanar da wakilan UNICEF.Wata sanawar dauke da sa hannu mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar, Kanar Onyema Nwachukwu, ta ce a lokacin tattaunawar, sun shaida wa hukumar ta agaji kar ta kuskura ta yi kafar ungulu ga ayyukan sojin a arewa maso gabashin kasar.Haka nan kuma an umarci wakilan UNICEF da su ringa sanar da mahukunta a duk lokacin da za su bai wa sabbin ma'aikatansu horo.

Da fari dai, rundunar ta fitar da sanarwar da ke zargin UNICEF da yin zagon-kasa a yakin da ake da Boko Haram ta hanyar yada labaran karya ko marasa sahihanci.

Wannan ba shi ne karon farko da rundunar ke kwan-gaba kwan-baya a kan matakin da suke dauka kan UNICEF ba.

Ko a wata Afrilu, ta bayyana wasu ma'aikatan hukumar uku da ta ce ba a bukatar aikinsu a kasar, sakamakon zargin cin zarafi ta hanyar lalata da aka kwarmata a kan sojojin Najeriya.

Sai dai daga baya rundunar ta sauya shawara tare da janye kalamanta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: