A jihar Kebbi, wasu matasa sun dukufa da kirga Buhun Gero domin gano yawan tsabar dake cikin sa.
Wadannan matasa sun fara musunne kamar wasa kan yanda wani ya furta cewa Adadin mutanen Nijeriya da motocin dake Nijeriya basu kai yawan tsabar buhun Gero guda ba, sauran kuma suka rantse Mutanen Nijeriya, sunfi Buhun Gero yawa nesa ba kusa ba.
A karshe dai aka cimma matsayar a kawo Buhun Geron a ajiye a kirga. A halin yanzu matasa suna ta karuwa wajen taimakawa a gano adadin tsabar da ke cikin Buhun Gero, sai ayi amfani da tsohuwar kidaya (Census) a, fayyace wanda yafi yawa tsakanin mutanen Nijeriya, da motocin su da kuma Buhun Gero a ga wanda zai yi rinjaye,
Ko wanne suna ya kamata a kira wannan Matasar?
0 Comments:
إرسال تعليق