الأحد، 2 ديسمبر 2018




Gaskiyar lamari gameda auren maryan booth da sadeeq zazzabin waka

Home Gaskiyar lamari gameda auren maryan booth da sadeeq zazzabin waka

غير معرف

Ku Tura A Social Media

Ana ce-ce-ku-ce kan wasu hotuna da fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Maryam Booth ta wallafa na bikin aure.

Jarumar ta wallafa hotunanta tare da Sadiq Zazzabi mawakin Hausa kamar ango da amarya, hotunan da ke nuna kauna da soyayya.

Hotunan sun ja hankalin mabiyanta da ma'abota fina-finan Hausa.

An ta yada hutunan a shafukan sada zumunta na intanet cewa Maryam Booth za ta yi aure.
Tsallake Instagram wallafa daga officialmaryambooth

Karshen Instagram wallafa daga officialmaryambooth

Wasu na tunanin a fim ne, yayin da wasu ke cewa da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi ganin cewa mawaki ne da ba ya fitowa a fim.

BBC ta tuntubi Maryam Booth domin tabbatar da ko da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi.

"Ban yi aure ba, a wani fim ne da ake kan shirya wa," in ji ta.

Ta kara da cewa an dauki hotunan ne a wani fim mai suna Gidan Biki na hudu da suka fito tare da mawakin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: