الخميس، 6 ديسمبر 2018




Karanta Kaji: Babban Dalilin da yasa aka Naɗa Nazir M. Ahmad Sarautar Sarkin Wakar Sarkin Kano Sanusi II

Home Karanta Kaji: Babban Dalilin da yasa aka Naɗa Nazir M. Ahmad Sarautar Sarkin Wakar Sarkin Kano Sanusi II

غير معرف

Ku Tura A Social Media
Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya nada Nazir M. Ahmad a matsayin sarkin wakarsa.


Danburan Kano ne ya tabbatar wa Nazir da wannan sarautar a cikin wata takarda daga fadar sarki Sanusi, kamar yadda Aminu Saira yayan Nazir ya tabbatar wa majiyarmu.

Aminu Saira ya ce takardar na kunshe ne da sakon godiya ga Nazir da kuma tabbatar ma sa da sarautar Sarkin wakar Sarkin Kano.

"Mai martaba ya umurce ni da na yi maka godiya bisa biyayya da soyayya da kake masa tun yana Dan Majen Kano har Allah ya sa ya zama Sarkin Kano wannan abin a yaba maka ne," in ji Danburan a cikin takardar.

Ya kara da cewa. "bisa haka mai martaba ya umurce ni da na sanar da kai cewa ya ba ka sarautar sarkin wakar sarkin Kano.

Sanarwar ta kara da cewa za a yi nadin sarautar ne a ranar Alhamis 27 ga watan disamba a fadar mai martaba sarkin Kano.

Ana ganin dai wannan sabuwar sarauta ce da ba a ta taba yi ba a masarautar Kano, inda Sarki ne ya ga ya dace a kirkiro da sarautar kuma a ba Nazir M. Ahmad.

Nazir M. Ahmad ya rera wa Sarkin Kano wakoki da dama, kuma an dade ana kiransa da Sarkin waka tun kafin tabbatar da wannan sarautar daga Sarkin Kano saboda basira da baiwar waka da Allah Ya ba shi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: BBC HAUSA

Share this


Author: verified_user

0 Comments: