الأحد، 23 ديسمبر 2018




Kundin Tarihin Duniya: Kyakyawar Budurwa Da Gemu Kamar Namiji!

Home Kundin Tarihin Duniya: Kyakyawar Budurwa Da Gemu Kamar Namiji!

غير معرف

Ku Tura A Social Media

A wani sabon rahoton hukumar ajiyar
abubuwan tarihi a duniya “Guinness World Records” a bana
sun bayyanar da wata matashiya mai shekaru ashirin da hudu
24, a duniya, a matsayin waddda ta lashe kambun shekarar
2017.



Harnaam Kaur, ‘yar asalin kasar Birtaniya, wadda take da
yawan gashin fuska "Gemu" kamar namiji. Ta bayyanar da
labarin ta, a matsayin wani abun da ta sha wahala, domin
kuwa idan aka ganta da gemu da gashin baki, sai a dinga
tsokalanta. Haka yasa ta shiga cikin damuwa, amma daga
bisani ta dauki cewar, wannan wata baiwa ce da Allah yayi
mata.




Tun tana ‘yar shekara goma sha biyu 12, ta fara gemu, a
wannan lokacin ne aka duba lafiyar ta, aka gano cewar, jikin
ta yana dauke da wani sinadari dake hana fitowar gashi a jikin
mata, ita nata yana da karfi, don haka gashi zai dinga fitowa
a jikin ta kamar namiji.




Tun dai a wannan lokacin ne ta daina yanke gashin fuskar ta,
yanzu haka dai gashin nata yakai tsawon zira’I ko a ce inci
shida 6. A yayin wani bukin nuna kawar kaya, Harnaam, ta
gabatar da kanta a matsayin mace da tafi yawan gashi a
tsakanin mata, hakan ya jawo hankalin mutane da dama a
kasar Ingila.




Ta bayyanar da cewar, wannan baiwace da ga Allah, don haka
kada wani ko wata su raina irin baiwar da Allah yayi musu a
rayuwa. Hasalima sai su gode mishi, domin yanzu gashi ta
shiga cikin tarihin duniya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: