Wasu 'yan bindiga da ake tunanin 'yan Boko Haram ne sun sace 'yan mata 15 a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar.
An sace 'yan matan ne a garin Toumour da ke kan iyaka da Najeriya a ranar Asabar, kamar yadda magajin garin na Toumour ya tabbatar wa kamfanin dillacin labaru na Reuters.
Boukar Mani Orthe ya ce 'yan bindiga sama da 50 ne suka abka garin suka yi awon gaba da 'yan matan.
Ko a ranar Alhamis wasu 'yan bindiga sun kai hari a Toumour inda suka kashe mutane takwas ma'aikatan wani kamfanin Faransa da ke aikin hako rijiyoyin burtsatse ga 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram.
Yankin Diffa a Nijar ya sha fama da hare-haren 'yan Boko Haram, tun watan Fabrairun 2015 da aka fara kai hari a yankin.
A watan Janairu sojojin Nijar bakwai aka kashe a wani hari da 'yan Boko Haram suka kai a Toumou
0 Comments:
إرسال تعليق