الأحد، 24 فبراير 2019




Buhari Ya Yi Nasara A Mazabar Lamidon Adamawa : 2019

Home Buhari Ya Yi Nasara A Mazabar Lamidon Adamawa : 2019

غير معرف

Ku Tura A Social Media
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yiwa Wazirin Adamawa kuma dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, mugunyar kayi a rumfar zabe ta mazabar fadar Lamidon Adamawa da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.
Alkalin zaben, Idris Yunusa, yayin bayyana wannan sanarwa ya zayyana yadda shugaba Buhari dan takara na jam'iyyar APC ya lashe kuri'u 228 yayin da Atiku na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 138 a rumfar zabe ta 10 dake unguwar Mbamoi.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito, baya ga samun nasara a mazabar sa ta Sarkin Yara da ke garin Daura a jihar Katsina, shugaban kasa Buhari ya kuma lallasa Atiku a mazabar sa ta unguwar Ajiya da ke birnin Yola.
A jiya mun kawo muku cewar Atiku ya gaza kawo akwatin sa yayin da shugaba Buhari ya lallasa shi da kuri'u 186, inda shi kuma ya tashi da kuri'u 167.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: