Tun a jiyan sakamako su ka fara fitowa daga mazabu daban-daban da ke fadin kasar nan. Sai dai har yanzu hukumar zabe ta kasa (INEC) ba ta fara fitar da sakamako a hukumance ba.
Zaben dai ya fi jan hankali ne a matakin kujerar shugaban kasa tsakanin manyn ‘yan takara; shugaba Buhari a jam’iyyar APC da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP.
Manema labarai da ‘yan jarida sun fi mayar da hankali a kan sakamakon mazabun manyan ‘yan siyasa da ke goyon bayan ‘yan takarar biyu.
Wata majiyar mu daga jihar Jigawa ta sanar da mu cewar tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sule Lamido, ya fita kunyar jam’iyyar PDP da dukkan ‘yan takarar ta na kujerar shugaban kasa da na majalisar tarraya.
Tsohon gwamnan ya kada kuri’ar sa a mazabar sa ta Bamaina ‘C’ da ke garin Bamaina a karamar hukumar Birnin Kudu.
A matakin kujerar shugaban kasa jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 259 yayin da APC ta samu kuri’u 20.
0 Comments:
إرسال تعليق