Shugaban Jam'iyar PDP na Kasa yayi kira da shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmoud Yakub da na 'Yan sanda Ibrahim Idris, su yi sauka daga kan mukaman su, saboda zargin da yake musu na cewa baza su yi musu adalci ba a zaben 2019.
WASHINGTON D.C. —
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya tayi kira ga shugaban hukumar zaben kasar wato INEC Farfesa Mahmoud Yakubu, da yayi murabus, da yake jawabi yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasar karkashin tutar Jam'iyyar Alhaji Atiku Abubakar, Shugaban PDP na kasa Uche Secondus, yace basu gamsu da take taken shugaban hukumar Zaben ba.
Sannan ya ce basu da kwarin gwiwar samun zabe na adalci daga shugaban hukumar zaben, shi yasa su ke neman ya sauka daga mukaminsa. Haka zalika shugaban na PDP ya nemi babban sufeton 'yan sandan kasar ya yi murabus bisa abinda su ka kira rashin yin aiki bisa ka’ida.
PDP tace tun daga jamhuriya ta farko ya zuwa mulkin soja, ba a taba samun yadda ake amfani da 'yan sanda wajen kuntatawa talakawa ba kamar a wannan lokacin.
Amma cikin martanin da ya mayar kakakin hukumar zaben ta kasa Aliyu Bello, yace babu abin da ya hada su da siyasa, domin a cewarsa ai zabukan da akai kowace jam'iyya ta sami nasara a matakai daban daban, al'amarin dake nuna cewa anyi zabe na gaskiya.
Shima mai magana da yawun shugaban 'yan sandan Najeriya, Bala Ibrahim, ya ce indai har wani nada korafi akan 'yan sandan to ya garzaya kotu don bin kadinsa, ya na mai cewa babban Sufeton 'yan sandan ba zai shiga tataburza da 'yan siyasa ba.
0 Comments:
إرسال تعليق