Showing posts with label Kalaman Soyayyar Hausawa da Fulani. Show all posts
Showing posts with label Kalaman Soyayyar Hausawa da Fulani. Show all posts

Thursday, 31 January 2019

KARANTA KAJI: SHAWARA GA SAMARI ‘YAN SOYAYYA.

KARANTA KAJI: SHAWARA GA SAMARI ‘YAN SOYAYYA.

Yi ammafani da kalaman soyayya masu dadi da inganci a lokacin da kake gwagwarmayar samun amincewar zuciyar dukkan wata yarinya da ka gani kana son mallakarta.

Kasance mai lissafawa tare da tauna dukkan wata magana kafin ka furta ta ga masoyiyarka bayan ta nuna maka amincewarta a soyayyarka.

Karda ka kasance mai takura wa tare da matsantawa a kan dole sai ta yi wani abu da ta nuna maka bata son yi a zahiri ko ta nuna maka alamun hakan, domin kuwa hakan zai sanya ta fara gajiya tare da kosawa da kai.

A dukkan lokacin da kake son ta yi maka wani abu to ka gabatar mata da bukatar ka cikin siyasa da zolaya amma idan ka nuna mata dole to kuwa ba zaka samu yadda kake so ba idan ka samu an yi ma kenan.

Kasance mai yin dukkan wani abu da ka san zai faranta mata ka kuma guji yin dukkan wani abu da ka san zai kuntata mata. Yi mata kyauta a lokacin da bata zaton samun hakan daga wajen ka, yin hakan zai sanya ka burgeta zai kuma kara sanya soyayyar ka a cikin zuciyar ta.

Karda ka cika yi mata kyautar kudi ko bata wasu abubuwa barkatai domin kuwa yawan yin hakan zai sanya ka kasa banbance cewa soyayyar gaskiya take yi maka ko kuma kudin ka take so.

Mace bata son takura bata son ka fiya maimaita mata abu daya, ba kuma ta son ka cika kushe wani ko wata a gaban ta, bata son kuma a lokacin da kuke tare kake nuna kulawa ko fifiko ko nuna wata ta fita kyau ko wani abu makamancin haka. Mata suna son kake yabon kyawun su.

Ka kasance mai bayyana mata cewa ita kyakkyawa ce a duk lokacin da kuka yi waya ko kuma kuke tare, ka ke bayyana mata cewa muryarta na da dad’i sosai kana samun nutsuwa a duk lokacin da ka ji sautin muryar ta, ka nuna mata cewa ta iya kwalliya kuma tana da tsafta.

A duk lokacin da kuka hadu ko a waya ko a zahiri ko kuma sako ka tura mata to ka bayyana mata kana sonta kafin ku rabu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Sunday, 6 January 2019

KARANTA KAJI: ME NE NE SO DA KAUNA?

KARANTA KAJI: ME NE NE SO DA KAUNA?

So da kauna, wani shauki/hali ne wanda ke kama da juna wurin tantancesa a ilimance, haka kuma a aikace .

 Ka santuwar cewa ba kowa ke sanin abunda yake aikatawa ba a tsakanin mu, ko kuma, me masoyina masoyiyata ke yi man daga cikin wannan halaye. Kowannen anayinsu ne ba tare da mutum yasan me yake aikatawa ba, kasancewar baya iya tantancewa tsakanin biyun nan me suke nufi.

Ko wannen su aikatasu halal ne a addinin muslumci, saidai wani yafi wani, daraja a idan shari'a kasancewar muhimmancin sa da amfaninsa tsakanin masoya. Hmm nasan wasu zasuyi mamaki akan cewar me ya hada addini da soyayya, tirqashi... 

To ka sani Madarar da zumur ilimin soyayya tatacce daga addinin muslunci, yake. Haka kuma duk wanda yabi tsarin soyayya a muslumci, ba shakka zai yi soyayya wacce take tatatta, kuma amintatta. Wacce babu yaurada ko ha'incin juna tsakanin masoya.

Menene Kauna?

= Kauna tamkar SO take sai daifa tafi So aminci, domin ita kauna bata canzawa, kuma ita kauna ba’a amutu akanta, ma’ana ba’acewa lallai sai an auri wanda ake Kauna ko sai an kasance tare dashi, in hakan bata yuwuba za’ai tashin hankali, ko a fara zargin shi abin kaunar, ita kauna ba haka takeba, ko anyi nasarar samun abin kaunar ko ba’ayiba, ana cigaba da masa fatan alheri kamar yadda kake masa a baya. Kuma ita kauna bata kwaranyewa, rashin haduwa tsawan zamani bai kwaranyar da ita.
Galibi abinda ke kawo kauna dabi’une, wato halaiyan abin kaunar suke janyo zuciya zuwa ga kaunarshi.

Me ne ne So a Takaice?

1. SO ne sinadarin dake sanyaya zuciya kamar yadda freezer ke sanyaya zazzafan ruwa zuwa kankara.

2. SO ne tsuntsun dake kaikawo tsakanin zukata mabanbanta daga karshe har sai ya sami zuciyar da zai gina shekarsa.

3. SO ne dausayin farin ciki mai haddasa ruruwar farin ciki mara misali.

4. SO ne siffar samin ingantacciyar rayuwa mai alfanu.

5. SO ne tsaunin rahama mai sanya masoya magagi gami da shantakewa a bisa tagwayen manufofi.

6. SO ne fitilar dake haskaka zuci yayinda ta fada cikin duhu matsananci.

7. SO ne tekun dake gudana tsakanin zukata mabanbanta.

8. SO ne asalin rayuwa, sannan kuma abin dake sarrafa ragamar dokin rayuwa a bisa hanya managarciya.

9. SO ne mafarar kauna, sai so ya sami kyakkyawan mazauni a zuci kafin kauna ta biyo bayansa.

10. SO ne bishiyar dake tsirowa a dausayin zuci, mai fitar da furanni kyawawa masu kyawun gani.

11. SO ne sadaukin zuci, mai ingiza zuciya filin dagar kauna, har sai ya kafa tutarsa a bainar zuciya.

12. SO ne ginshiki, sannan kuma tubalin kauna sai an kafa tubalin so a zuci kafin ginin kauna ya tabbata a matabbatar ruhi.

13. SO ne tekun dake gangarowa daga ruhi zuwa sassa daban-daban na jiki, wanda ke fesar da shauki a nahiyar kalbi.

14. SO ne maganin dake warkar da zuciyar data shiga garari.

15. SO ne guguwar dake daukar, masoya, idan guguwar so ta dauki masoya takan makantar da idanuwansu har su rasa ganin laifin juna.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Thursday, 29 November 2018

KARANTA KAJI: YADDA ZAKA ZAUNA LAFIYA IDAN KANA DA BUDURWA BAHAUSHIYA

KARANTA KAJI: YADDA ZAKA ZAUNA LAFIYA IDAN KANA DA BUDURWA BAHAUSHIYA

YADDA ZAKA ZAUNA LAFIYA IDAN KANA DA BUDURWA BAHAUSHIYA.

1. Karka taɓa tsammanin zata kira ka awaya idan ba haka ba zaka mutu kana jira.

2. Ka sani idan kace mata "I love you" ko ina sonki nagode kawai zata ce amma girman kai bazai barta tace maka I love you ba.

3. Karka taɓa tsammani zata fara maka magana idan tana online.

4. Idan ka tura mata love messages kar kayi tsammanin zata yi maka reply.

5. Kasani kai ke sonta, kuma kai zaka kula da ita, ita bazata iya yi maka komai ba.

6. Ko yaushe zata iya rabuwa da kai idan ta samu wanda yafi ka kuɗi.

7. Kasani cewa bakai kaɗai bane saurayinta.

Haƙiƙa idan kayi haka zaka zauna lafiya da budurwar ka bahaushiya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Thursday, 8 November 2018

KARANTA KAJI: KADAN DAGA CIKIN ALAMOMIN GANE MASOYIYA TA GASKIYA

KARANTA KAJI: KADAN DAGA CIKIN ALAMOMIN GANE MASOYIYA TA GASKIYA

A lokacin da kake ‘ko’karin gano matsayinka a zuciyar budurwarka shin tana son ka ko akasin haka da akwai bu’katar ka nazarci wasu abubuwa wad’anda wasu sun kasance waiwaye ne wasu kuma suna kan faruwa.

FARKON HA’DUWAR KU.

YANAYINTA DA KUMA HALAYYARTA.

FARKON HA’DUWAR KU

A yayin gabatar da soyayyarka gare ta ka yi amfani da salo ne mai karsashi wato sai da ka gama jan hankalinta da ra’ayinta a kan ka sannan ka bayyana a gareta da lamari na soyayya?

Furta kalaman amince wa na soyayya ga wanda suke so abu ne da mata suke jin kunyar furta wa a karon farko ga samarin na su, sai dai duk da haka zata ke nuna maka alamun tana son ka kuma zata ke nuna maka wasu alamomi da suke nuni da SO.

Salon da kake bi wajen gudanar da soyayyar ta ku shi ne sikelin auna ci-gaba ko ci-bayan soyayyar ta ku, misali a lokacin da kuke tsaka da soyayya sai ta samu wani da ya fika iya kalaman soyayya da barkwanci da rashin yawan mita da dai duk wani salo mai burge wa to babu shakka ko kafi ‘karuna dukiya zai iya d’auke hankalinta da ga kan ka, sai dai ta tsaya da kai dan kud’inka.

A saboda haka akwai bu’katar ka kasance mai sabunta salonka na soyayya tun daga kan kalamai da yanayin yadda kake bata kulawa da sauran su lokaci bayan lokaci.

A dukkan lokacin da ka bu’kaci mace ta baka amsar amince wa tana son ka sai ka ga ta yi murmushi ko ta kasa furta hakan a karo na farko to hakan yana daga cikin alamu na SO domin kuwa wanda ake so ake jin kunya.

Karda ka damu da sai ta furta maka kalmar tana son ka kai dai lura da wad’annan abubuwa kamar haka;

Sau nawa kake kira kafin ta amsa?

Idan har da so zata amsa a kira na farko idan kuma bata amsa ba zata amsa a kira na biyu har ta baka uzurin da zaka gamsu na dalilin rashin amsa kiran, idan har bata amsa a kira na biyu ba sai ka bar kiranta haka idan har da so zata kira ka da zarar ta ga kiranka da ta rasa har ta baka uzurin kare kai.

Matu’kar tana son ka za ta kasance mai kar’bar shawarar da duk ka bata kuma za ta kasance mai son abun da kake so.

A duk lokacin da ka je wajen ta zance za ta fito cikin farin ciki kuma ba zata nuna ‘kosawa da jin firarka ba matukar ka iya zance har zuwa lokacin da za ku yi sallama.

Idan har ka saba kiran ta a waya matu’kar ta damu da kai idan ka kwana biyu baka kira ta ba to za ta kira ka ta ji ko lafiya, idan ma bata kira ba saboda wani dalili bayan ka kira za ta yi kalamai na nuna ta yi kewar ka.

Idan har tana son ka a kullum za ta ke ‘ko’karin yin abun da zai faranta ranka, za ta ke ‘ko’karin guje wa abun da zai sa ka yi fushi.

A lokacin da soyayyarku ta yi nisa zata iya bayyana maka wasu sirrikanta da suka shafe ta.

A lokacin da ka nuna ‘bacin ranka a kan wani abu da ta aikata da ba dai-dai ba, a yayin baka ha’kuri da shawo kan ka za ta iya zubar da hawaye.

Zata ke ‘ko’karin bayyana ka ga ‘kawaye da kuma ‘yan gidansu.

Zata ke ‘ko’karin turo maka da kalamai na soyayya.

Zata kasance mai tambaya a dangane da ‘yan uwa da kuma abokanka da ma dai duk wani da ta san kuna a tare.

Za ta ke damuwa da damuwarka.

Irin wad’annan abubuwa da sauran ire-iren su duk zai kasance ta na nuna maka su.

YANAYINTA DA KUMA HALAYYARTA.

Akwai bu’katar ka fahimci yaya yanayinta da kuma halayyarta suke,
Shin tana da jan aji ne da yawa?

Wanda hakan ka iya sawa ko tana son ka ba zata amince da kai a karon farko ba har ma za ta iya yin wasu abubuwa da zaka iya tinanin wula’kanci ta yi maka, amma da sannu matu’kar ka iya allonka za ka wanke.

Tana da kunya ne? ta yadda ba za ta iya sakin jiki da kai ba a karon farko kuma bayan tana son ka, idan ka yi ha’kuri da sannu soyayyarka za ta cire mata wannan kunyar da take ji a kan ka domin kuwa idan aka juri zuwa rafi da sannu tulu yake fashe wa.

Koda a ce bata da son kud’i farkon soyayyar ku sai ya kasance ka fara yi mata kyaututtuka to da sannu idan ka matsa da yi mata kyauta son abun hannunka zai rinjayi son da take yi maka na gaskiya, an dai kuma ce kyauta tana ‘kara soyayya, amma kuma komai ya yi yawa to zai kawo matsala.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Sunday, 28 October 2018

Karanta Kaji: Aure Ko Zina?

Karanta Kaji: Aure Ko Zina?

A yau idan ka ce za ka yi aure, daga ranar da ka fara fafutuka, zuwa ranar aurenka, in ba kai wasa ba sai wando ya daina zama a qugunka saboda tsadar aure tun daga sadaki, kayan lefe da kudin gaisuwar uwa da uba da sauran su.

Marubuci: Mal. Muhammad Nazifi Hashim Samaru Zaria.

Wannan ya sa samari da dama suka kasa yin aure.

Amma a yau idan ka yi niyyar yin zini a rana daya (in dai za ka iya yi) da mata 20 ko sama da haka za ka iya yi. Sannan kuma kudin da za ka kashe ba zai taka kara ba ballantana ya karya shi. Kai wasu ma ko sisi ba sa kashewa, kyauta sukeyi saboda yan matan gasu nan kamar jamfa a Jos, kuma suna bukatar auren amma samari ba kudi, iyaye kuma sai mai kudin suke so.

Wannan ya sa aka taru aka hada karfi da karfe tsakanin samari da yan mata da kuma iyaye ake ta sabawa Allah kullum.

Na daga cikin abubuwan da za su kawo karshen zinace-zinace shi ne farashin aure ya fado kasa warwas!, Domin babban abun
bukata a aure shi ne sadaki, shi ma
idan babu shi ana iya badawa bashi, duk fa Musulunci ya yi haka ne domin a rage fasadi a doron kasa.

A haqiqanin gaskiya tun da na tashi ban taba gani ko jin labarin an daura aure bashi ba. Kai hasali makowacce shekara farashin aure qara tashi sama yake kamar gwauran zabo.

Sai dai nasan farashin sadaki yana yin tsada ne bisa dalilin talauci da ake fama da shi. Sakamakon wasu iyayen suna karawa kudin yawa nedomin suyi wa yarsu kayan daki dan a fita kunya.

Ita kuma kunya ana so a fice ta ne a gurin yan gutsiri-tsoma, wadanda idan ba a yi wa yarinya kayan a zo a gani ba za su bi unguwa suna gulmace-gulmace, karshe ya koma gori wajen amarya da iyayenta.

Wannan yasa iyaye ke tsauwala kudin sadaki da abubuwa makamanta wannan.

To amma, sai suka manta cewa ita
kunya ta Ubangiji ake gudu, ba ta
wani ba.

Domin idan diyarka tayi cikin shege a gidanka sai ka fi kowa jin kunya a duniya, kuma wannan shi ne abin kunya da ake gudu, amma ba kunyar kayan lefe ko sadaki ba.

Kalli abinda waɗannan 'yam mata da samarin su aikata kalla kasha mamaki...

DOWNLOAD VIDEO HERE

Muryar Hausa24 Allah ya kare mana zuri'ar mu baki ɗaya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Friday, 12 October 2018

KARANTA KAJI: TONAN SILILI ZUWA GA MAZAN FACEBOOK SAKO  DAGA FADILA H ALIYU KURFI

KARANTA KAJI: TONAN SILILI ZUWA GA MAZAN FACEBOOK SAKO DAGA FADILA H ALIYU KURFI

Zuwa ga mazan Facebook YA ISA HAKA, laifin Maryam Sanda ya tsaya kanta ita daya, kuna aibanta mata kuna zaginmu kan laifin wata wanda ko wurin ubangiji ita kadai zai hukunta ba mata duka ba, wacce bata da goyon baya daga gare mu mata .

Mace nawa ce rungume da mijinta sai dai mutuwa ta raba, da dadi ko kuma akasinsa, a cikin ciwo ko lfy, karamin misali duba mahaifiyarka ko yan uwanka mata sun kashe mazansu?

Maryam Sanda ta wakilci kanta ne ba mata ba, wasu don wuce makadi da rawa wai ba za su auri mai suna Maryam ba sbd wata Maryam da ta kashe mijinta, wani gwani na gwanayen ma dauko wani shirmen reference dinsa ya yi wai Maryam hudu ya sa ni wacce ta kashe mijinta, to ya lissafa dubban Maryam din da ya sa ni zaune lafiya a dakinta.

Idan kuma duk zuriyarsu babu wata Maryam da take zaman aure lami lafiya bari na baka misali da kakata, "Maryam ko ace mata Mairo ko da fillaci ace Bingel kyakkyawar bafullata nake wacce ta yi zamani a lokacinta, jikin mai boye tsufa ne, ta rasu tana da shekara kusan casa'in da doriya, amma har ta rasu furfurar kanta kadan ce kanta duk bakin gashine, Kamar lokacin zafi tsofaffi na shan iska basa saka riga amma ban ita sbd kirar da Allah ya bata kamar budurwa 'yar shekara sha biyar, duk wanda ya kalleta sai ya kara duk da tsufanta, mijinta ya rasu tun tana da kuruciyarta bata wuce aure ba kuma tana da tarin masoya sbd da kaunarsa bata kuma aure ba, ita burinta shine ita ma ta mutu a matsayin matarsa kamar yanda ya mutu a matsayin mijinta rungume akan kafarta, kasan labarinta? Amsar a'a sbd ita alkhairi ta yi, ku kuma baku yada shi.

Idan Maryam Sanda ta bata maka har kana condemning duk wata Maryam ya zaka yi da hakkin wasu Maryamomin, ina Nana Maryama mahaifiyar Annabi Isa, thousands of Maryama suna gidan mazajensu.

Ke nan kai da ma su tunani irin naka kun yi condemning mai asalin sunan Nana Maryama baiwar Allah. Da sauran bayin Allah masu irin sunan da su ka yi dedicating life dinsu ga aure da rayuwar yaransu, simply don sunan Mom dinka ko yar uwarka ba Maryam ba ne, wani ma bincike ya hau yi wai ma su sunan Maryam hudu suka ta6a kashe mazajensu. Wani sunansa Abubakar sunan shugaban 'yan boko haram, ke nan sai mu ce ba mu kuma auren mai irin sunan sbd ya mayar da dubban mutane marayu.

Wani kuma ma " Wai matan Arewa abin tsoro ne bari mu guje ku" sai me? Ku guje mu mana! Kamar iyayenmu mata su ba 'yan Arewar ba ne, kuma ba su yanke mana iyayenmu maza ba, duk millions of matan arewar da su ke zaune lafiya a gidajensu su ba mata bane, sai Maryam Sanda, maza nawa ne suka kashe matansu? Kun san adadi? Mu fasa auren mu ka yi?

Kai maza! Abin da Maryam ta yi is very wrong, dole ta fuskanci hukunci, abin da ta yi ba kishi bane rashin imani ne, ba soyayya bace akasinta ce, duk wanda kake so da gaskiya baka iya jurar ganin jininsa na gudana yana neman taimako kuma taimakonka ka saka masa idanu,ka kashe shi da kanka, idan kun kira wannan kishi ko soyayya to akwai gyara, kuma mata basa bayanta abar dora mana laifi. A yanke ma Maryam hukunci, RAI A BAKIN RAI NE, Bilya mace fa ta haife shi, shin baku tunanin mata na jin kuna da takaicin kasan gilla ma dan su.

Mace miliyan nawa ke aure sai don wasu tsiraru wakilin shedan sun yi laifi a rika mana kudin goro, ni fa a Facebook kamar na hunce mu daku da wasu sbd abin haushi, ku zagi Maryam ko kuma ku cigaba da tsinar mata iyayenmu. Wurin ai banta mata mutun ya rika kokari keta haddin mahaifiyarsa tunda ita ma ai mace ce.

Da za a turo Maryam gaban mata sai sun yi gutsi-gutsi da ita, mun tsine mata mun ai bantata amma still zunubinta na kokarin shafar mata, to ko wurin Allah laifinta baya shafarmu, duk wanda ya zagi mace wlh bai yi tunani ba, masu mummunan kishi wakilan shedan ne, kara kishiya Allah ya halasta ma maza, babu wacce ta isa ta hana, ranar da Maryam ta yenke Bilya ranar an yo ma wata kishiya kuma bata so amma dole ta hakura.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Saturday, 29 September 2018

KARANTA KAJI: DALILAI 9 DAKE JEFA MATA A KARUWANCI DA YAWON BANZA

KARANTA KAJI: DALILAI 9 DAKE JEFA MATA A KARUWANCI DA YAWON BANZA

WASU DAGA CIKIN DALILAN DAKE
JEFA MATA A
KARUWANCI DA YAWON
BANZA.

A yau shafin Muryar Hausa24 zamu mai da hankali akan kaɗan daga cikin dalilan da suke jefa 'ya'ya Mata Karuwanci.

Ga Dalilai Kamar Haka:

1. MARAICI :- Wasu marayu ne
basu da masu
daukar nauyinsu wanda ya dace
su lura da
tarbiyarsu sun gaza sai kansu da
Yayansu suka sani.

2. DANNIYA :- wasu
zaka samu
zaluntarsu
akayi, akan marayune akan cinye
masu gadon
su.

3.TALLA :- Wasu kuwa yawon
tallace-tallace
ne yake sawa suke fadawa harkar
karuwanci,
sai ka ga mutum yaci abinci ya
bada fiye da kudin abincin da yaci.

Daga
nan ne
sai ka ga
mutum ya yaudare ta da wannan
kudin.

4. AUREN DOLE :- Wasu kuma
zaka samu Iyayensu kanyi masu
auren dole da wanda
basa so sai ka samu sun gudu
daga gidan
Aurensu sun shiga karuwanci.

5.TALAUCI :- Wasu ko Talauci ne
sai sun fita
anyi amfani dasu suke samun
abinda zasu ci
Abinci, amma idan hakan kurum
suka nemi a taimaka masu babu me
taimaka
masu.

6. FYADE :- Wasu kuwa tun suna
Yara akan
samu wasu Mutanen banza ko a
gidan da ake
rikonsu, su lalata su.

7. ƘAWAYEN
BANZA :- Zaka
samu mafiya
yawan ƙawayen kan jasu wajen
samari sai
su bada hadin kai dan kar a
kirawo su da Tsamaye.

8. IYAYE MASU
KWADAYI :-
Wasu Iyayensu kansaka su a
hanyar karuwanci, saboda
kwadayin abin duniya, suko yiwa
yarsu Aure
idan ta samu Miji saboda talaka ne,
saboda
tana bin samari tana kawo musu
kudi kadan
kenan daga cikin.

9. YAUDARA SAMARI :-
Sai ka
samu Yarinya
tabawa saurayi dama 100 bisa 100
a zuwan
zai Aure yana amfani da wannan
damar yana amfani da ita daga karshe sai
dai
kurum taji
yayi Aure.

Allah ya rufa mana Asiri
Allah ya kara Shirya mana Zuri'ar
mu ya kuma
tsaremu daga aikin dana sani Amin.

KARANTA YANZU KAJI: KO ME YASA MATA KE NEMAN 'YAN UWAN SU MATA DOMIN YIN MADIGO???

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Saturday, 15 September 2018

KARANTA CIKAKKEN LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN - LABARIN SOYAYYAR DA YA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI

KARANTA CIKAKKEN LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN - LABARIN SOYAYYAR DA YA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI

MASU NEMAN SHAFIN MURYAR HAUSA24 TA KAWO MUSU LABARIN MAJNUNU
LAILA TO GASHI NAN....

Nasan kun daɗe kuna jin Labaran Soyayya Amma na
Tabbata baku taɓa cin karo da irin wannan ba....

 Waye
majnun lailah?

Wani mutumne da aka yi a daular banu umaiyya
abisa zancemafi inganci. Sunansa shine "Qais Bn
Mulawwah" daga "kabilar Banu Amir",

Qais balaraben ƙauyene, ya taso tare da ‘yar gidan
kawunsa mai suna "LAILA BNT MAHDI IBN SA’D"
Amfi sanin Laila da sunan "Laila Aamiriya", tare suka
taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka
girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin
balagha.

A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci
suka gama bayyana ajikin Laila sai "Qais" ya ruɗe
soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya
tashi.

Domin a wannan lokacin ne "Qais" ya Lura da irin
kyawun dirin da Allah ya yiwa abokiyarsa "Laila", a
kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi
take yi a cikin zuciyar "Qais", a cikin wannan yanayi
ne "Qais" ya shiga rera mata waƙoƙin soyayya kala-
kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi
mahaifin "Laila" ya nemi da "Qais" ya fito dan
maganar aure, saboda nuna soyayya da ƙauna sai
da Qais ya bayar da raƙuma hamsin a gidansu
"Laila" a matsayin kudin aure.

Ana haka sai ga wani mutum da ake kira "WIRD BN
MUHAMMAD" wani dan hamshaƙin attajiri ne daga
cikin ‘ya’yayen masarautar "Banu Umaiyya", katsahan
yayi ido hudu da "Laila" a wata rana a cikin wani
Lambu tana kiwon dabobinta.

Daga wannan rana Soyayyar "Laila" ta hana Wird ya
yi bacci a wannan dare!

Cikin yan kwanaki kadan
Iyayen "Wird" suka sauka a gidan su "Laila" dan
neman aurenta ga ɗansu "Wird".

A wannan rana da Iyayan "Wird" suka je ga mahaifin
"Laila" sai da suka ajiye masa Manyan Raƙuma
guda ɗari (100) a matsayin kuɗin aure, wato ribi
biyu akan abinda "Qais" ya bayar!

Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin
kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna
kwadayi da son abin duniya.

Bayan haka ne
Mahaifin "Laila" ya kira‘yarsa "Laila" cikin ɗaki yanai
mata huɗubar cewar ga mai kudi ɗan masu mulki
shi zai aurawa ita!

Babbar Magana! Laila taƙi amincewa da maganar
mahaifinta a karon farko, amma sai ya yi mata
barazanar cewar zai yanka ta idan har bata amince
da auren "Wird" ba!

Kwatsam sai aka wayi gari "Qais" ya ji gari ya ɗauka
da kace nace ɗin an yiwa masoyiyarsa "Laila" aure,
da "Wird".

Nasan da yawan ku  zaku tambayi wakilin shafin Muryar Hausa24 ko Wanne irin hali "Qais" zai kasance a wannan ranar?

Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira daga
idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin
ciki gami da bacin Rai da takaici, zubar da hawaye
babu dare babu rana, suka kasance tare da "Qais" a
matsayin abokai na din-din-din!

Waƙe-waƙen soyayya sune zancensa, bashi da
abokin hira sai waƙar da yake yiwa "laila" ga kadan
daga irin abinda yake cewa:

zuwa ga Allah nake kai kukan son "laila"
kamar yadda maraya yake kai kukan maraicinsa
zuwa a Allah.

Mara yanda da kafasa ta karye gashi kuma dangi
sun gujeshe "Lallai" rasa iyaye abune mai girman
gaske.

Haka "Qais" da aka yiwa lakabi da “Majnunu lailah”
yake bin kwararo kwararo da saman manyan
duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawa
Laila wadannan baituka masu motsa zuciya bai
gushe ba harsai da akayi masa laƙabi da “majnunu
laila”.!

Duk da cewa itama Laila tana matukar son
"Qais" (majnun) amma kuma hakan baya hanata ta
wahalar dashi, a wasu lokutan ma harda yi masa
wulaƙanci, baya ga yin amfani da mallakeshi da tayi
wajen azabtar dashi, dama haka sha’anin mata yake
shi yasa majnun awani baiti yace:

“Nace da wani babban malami da na gamu dashi a
makka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar
dani, azamanin da take jiji da kai (saboda ina
sonta) shin hakan da take ba laifi bane?”

Sai Malamin ya fadawa "Qais" cewa: “Wallahi da
sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita
hadu da bala’i”.

Daga nan "Qais" yace, sai na kasa mallakar idona
sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jiƙa min
aljihun rigata, sai nace, Allah ya yafe mata laifinta
duk da yake a duniya dan kadanne samunta.

"Qais" ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan
hali har sai da ya samu taɓin hankali.

Domin ya
kasance idan yaga yara suna wasan ƙasa yakan
zauna tare dasu ya taro kasa ya rinƙa gina gida irin
wanda yara suke yi da kasa yana cewa cikin waƙa:
“abokaina kuzo kuga gidana nida laila”....!

A yayinda al-amari ya tsananta sai mutane suka
baiwa mahaifin "Majnun" wato "Qais" shawara da ya
daukeshi ya kaishi ka’aba (Ɗakin Allah) ya umarce
shi da ya roƙi Allah ya cire masa son Laila!

Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je
ɗakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama
tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila...

Sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka
daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da
nake yiwa "Laila" ba.

A taƙaice haka "majnun" ya rayu cikin wannan yanayi
na abin tausayi!
Ita kuwa "Laila" tuni wanda ya aureta ya ɗauke ta daga
kasar Saudiyya ga baki ɗaya zuwa kasar Iraqi.

Haka itama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi

abinka da ‘ya mace mai rauni sai da rashin ganin
"Qais" ya haddasa mata ciwon zuciya .

Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda
tsananin soyayyar "Qais Majnun"!

Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin masoyinta
Allah ya karbi rayuwarta!

A lokacin da "Majnun" yaji labarin rasuwarta sai da
yaje har ƙasar Iraqi ya nemi inda take, da inda aka
binne ta, a maƙabartar da aka binne "laila" a dai-dai
gindin kabarinta ya tare.!

Bashi da aiki sai kuka da waƙoƙin soyayya a
gareta.

Wata rana da safe sai masu wucewa suka hangoshi
(Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan kabarinta, ko da
aka zo akaduba sai aka tarar Allah ya yi masa
cikawa!

Allahu akbar

Wannan shine Qarshen hikayar "LAILA MAJNUN" kunjifa yadda akeyin soyayya ruwa-ruwan ta.

Rubutawa Tafarkin Tsira Tace rubutu da tsarawa tare da Hotuna wakilin shafin Muryar Hausa24 .

Haka fa Allah yake jarabtar wasu da soyayya..

Ya Allah kada ka jarabcemu da soyayyar da bazamu iyaba.

KU SAURARA KUJI LABARAI 3 MASU BAN MAMAKI

Duk wanda bai taɓa karanta labarin Romeo da Juliet
ba lallai akwai sauransa ga sanin tarihin soyayyar
artabu, kisisina da sanin kololuwar sadaukarwar
masoya.

Wanda kuma ya ji labarin soyayyar Sarki Shah
Jahan da matarsa Mumtaz Mahal, tare da ginin
soyayya mafi tarihi da tsada ‘Taj Mahal’ ya dan san
wani abu kadan fiye da wanda bai san ko kaɗan ba.

Wanda ya san tarihin soyayya, da sauran labarun
soyayya, amma kuma bai taba fadawa tsaka mai
wuya ba saboda soyayya, kamar Sanawiyya ibn
ustaraz Tabbas bai san komai a Soyayya Ba.

Mutane nawa ke Da bukatar Sonjin Waɗannan

LABARAN SOYAYYA 3 NAN MASU BAN MAMAKI...

Idan kana/kina so ku hanzarta aiko mana da saƙo a email ɗin mu kamar haka Muryarhausa24@gmail.com

Tace rubutu da tsarawa wakilin shafin Muryar Hausa24 .

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki 

Mungode