Showing posts with label Kiwon Lafiya. Show all posts
Showing posts with label Kiwon Lafiya. Show all posts

Friday, 5 October 2018

KIWON LAFIYA Amfanin Tumfafiya A Jikin Dan’adam

KIWON LAFIYA Amfanin Tumfafiya A Jikin Dan’adam


Tumfafiya wata bishiya ce mai matsakaicin tsayi da ke girma a Yammaci da Gabacin Afrika da kuma wasu sassa na Kudancin Asiya. Haka kuma ana samun tumfafiya a kasar Indiya. Ta kuma kasance daya daga cikin bishiyoyin da cibiyar koyar da hada magani da ke a kasar ta India waton (All India Institute Of Medical Sciences) sun yi nazari na musamman ga wasu muhimman sinadiran da ke kumshe a cikin ganyen tumfafiya inda suka tabbatar da cewa wadannan sinadiran suna maganin gudawa.

A dalilin hakane masana maganin tsirran itatuwa na kasar Indiya waton Ayurbedic pharmacopoeia suka yi umurni amfani da saiwar da kuma ganye ko kunnuwan tunfafiya a magance asma da daukewar sheda da kuma sauran cututtukan da ake dangantawa da cututtukan huhu.

A kasar Hausa, masu maganin gargajiya na amfani da ruwan tumfafiya don warkar da wasu cututtukan fata kamar makero. Inda ake aske gashin kai ko kuma duk inda makeron yake a jiki sai a karkare gurin da makeron yake har sai gurin ya yi jini sai a tarfa wadannan ruwan na tumfafiya kan makeron, za a dunga wanke wajen a kullum ana sanya ruwan tumfafiya a sama har sanda ciwon ya warke.

Tunmfafiya na maganin dafi kamar na maciji da cizon kunama. Ana amfani da saiwar tumfafiya bayan an konata sai a gauraya garinta da na danyen mai a shafa kan inda cizon ko harbin yake.

A kasar India, suna amfani da furen tumfafiya ga masu farfadiya da kuma ciwon kurkunu. Ana amfani da kunnuwan tumfafiya a maida basir mai tsiro. Za a nemi kunnuwan tumfafiya kamar kwara biyu ko uku haka sai a dan kara su ga zafin wuta kadan sai a danne dubura da su in sha Allahu nan take duburar za ta koma.

Ana tarfa ruwan tumfafiya kamar digo biyu a cikin kunnen dake ciwo za a yi haka sau daya zuwa biyu. Amma idan kunnen na ruwa to sai a tafasa itatuwan tumfafiyar misalin kofi daya sai a rinka wanke kunnen dake ciwo da su.

Tumfafiya na maganin dan kanoma wanda ya tsananta, shawara, ciwon ciki, yawan ciwon kai na ba gaira ba dalili, tarin nimoniya da kuma cutar kuturta.

Ana kona saiwar tumfafiya a maida su gari sai a hada da dan karamin cokali na garin lalle a daura a kan ciwon kafa ko hannu ko yatsan da ya kumbura ko ya ja ruwa kamar ciwon dan kankare ko wanda ake tunanin na kambun baka ne. Wannan kumshin zai zuke dafin ciwon a cikin karamin lokaci.

Ana amfani da tumfafiya a kona jinnun da aka turowa mutum ta hanyar sihiri. A nan za a nemi garin ganyen kaikayi koma kan mashekiya sai a nemi furen tumfafiya a shanya idan ya bushe sai a dake a gauraya su waje daya a nemi allo babba a rubuta abun da ya sauwaka daga ayoyin Alkur’ani mai girma sai a wanke a tafasa a sha tun da safe kamin a karya. Wallahi sihirin ko wane iri ne zai karye nan take.

Ana sirrin layar zana ta musamman da kaucen tumfafiya saidai a gaskiya wannan tamkar sihiri ne ba zamu fadi wannan sirrin ba. Saboda lahaninsa.

Ana zubar da ciki nan take lokacin da aka yi amfani da tumfafiya. Shima wannan ba zamu fadi yanda ake yin sa ba. Saboda lahaninsa da kuma damar da wasu za su samu ta aikata abin da bai dace ba.

Ana tafasa kunnuwan tumfafiya a tunga wanka da ruwan tun da safe dan maganin matsanancin ciwon gabobi da kuma jiyojin jiki.

Ana busar da furen tumfafiya sai a dake ya koma gari a rinka sha a cikin ruwan zafi duk lokacin da za a kwanta domin magance mutuwar zakari.

Ana amfani da kunnuwan tumfafiya dan dawo da jinin al’adan daya dauke na tsawon lokaci. Ana turara kunnuwan tinfafiya dan warkar da asma da ciwon kai na gaban goshi.

A kan sanya ruwa a cikin kwallo 7 na diyan tumfafiya sai a bar ruwan sai sun kwana uku a ciki sai a juye ruwan a rubuta surar karfe a wanke a tarfa zuma cokali biyu a sha kamin a ci komai. Maganin sara na karfe kamar takobi ko wuka da rauni ko kariya mai tsanani ga jiki.

Ana amfani da ruwan tumfafiya wajen ciwon hakori. A nan ana diga ruwan tumfafiya a hakorin da ke ciwo.

Mata masu neman tagomashi ga mazajensu sai su nemi busashen garin tumfafiya sai su hada da garin lalle da kuma garin ganyen bishiyar birana. Sai dai kuma bishiyar tumfafiyar tana da ban tsoro musamman da dare inda takan canza bishiya ce da iskoki ke fakewa a gunta. Dan haka sai a san yanda aka tinkaren ta. Amma tana da fa’idodi da dama. Duk da yake ba kowane irin ilmi ya dace mu fayyace ba. Saboda fadar wani ilmi zai zamo illa. Da fatar duk abin da muka fada a kan kuskure za a gafarce mu.

Daga leadership

Sunday, 2 September 2018

Kiwon Lafiya Amfanin Man Ridi A Jikin Dan’adam

Kiwon Lafiya Amfanin Man Ridi A Jikin Dan’adam



Man Ridi yana daya daga cikin iri-irin Man da aka sani, an dai dade ana amfani da man ridi wajen yin magungunan gargajiya, bincike ya nuna ana amafani da man ridi tun wajen shekaru dubu da suka wuce domin kariya daga cututtuka da suka shafi abubuwan da kan iya kawo cutar fatar jiki ko kuma cutauttuka da suka yi karfi kamar su ciwon suga, hawan jini da sauransu. A wani Bincike da aka yi a makarantar Maharishi International College Fairfield Lowa a kasar Amurika an gano cewa dalibai na yin amfani da man ridi wajen wanke baki domin ba su kariya ta musamman wajen kare cutar dake fito wa a dasashin mutum wanda kansa gurin ya yi ta zafi har ya janyo asarar hakora.
Amfanin man ridi bai tsaya a nan ba domin ana amfani da shi wajen wanke kai don kashe kwarkwata ko amosanin kai. Ana kuma shafawa yara man ridi a jikisu don gyaran fatar jiki.

Ga Dai Wasu Cututtuka Da Man Ridi Ke Warkarwa

– Gyara fata da inganta lafiyar ta.

– Kara girman gashi da launin bakinsa.

– Kariya daga ciwon-daji.

– Gyara fatar jarirai da sanya su natsuwa a bacci.

– Hana rubewar hakori, kogon hakori da sauransu.

– Kariya daga ciwon asma da cututtukan numfasa.
– Rage hawan jini.

– Rage yawan sinadarin “Cholesterol”.

– Kariya daga ciwon suga.

– Inganta lafiyar kwakwalwa da sauransu.

-Domin samun lafiyayyar fata kuma, ana hada Man Zaitun da Man Ridi a mayar da shi abin shafawa a wata daya fatar jikin mutum za ta yi kyau kuma ta samu kariya daga cututtukan fata.

-Ciwon mara, ana shan cokali 2 safe da rana da kuma dare dan maganin ciwon mara.

– Ciwon cikin da baya jin magani da kuraje musamman na kazwa, a samu sabulun Zaitun a rika wanka da ita idan aka bushe sai a shafa man ridi a kalla a yi haka sau 2 a rana tsawon sati daya.

– Ciwon sikila, ana hada man ridi da Zuma a rika bawa mai matsalar yana shan cokali biyu safe da rana da dare har tsawon wata 2.

-Basir mai tsiro, a samu sassaken bagaruwa da ‘ya’yan ta a tafasa da ruwa idan suka tafasa in sun rage zafi sai a zauna cikin ruwan tsawon minti 15, idan aka fita a shafa man ridi a yi haka sau 2 ko wace rana tsawon kwana 10.

-Ashma, a rika shan cokali 2 safe da rana tsawon sati 3.

-Ulcer, a samu man ridi a hada da madara a rika sha da safe kafin a ci komai haka da dare bayan an ci komai sai a sha awa daya kafin a kwanta.

-Kumburin Jiki, ana shafa man ridi duk bayan an yi wanka da kuma in za a kwanta bacci.

–Soshe-soshe saboda yawaitar majina ko mataccen jin, sai a saka cokali 2 duk lokacin da za a ci abinci sannan kuma a shafe jiki da shi amma wajen shafawar dole sai an hada da man Zaitun.

-Ciwon mara lokacin fara al’ada, ana hada cokali daya na garin ridi da cokali daya na man Ridi da madarar gari a sha sau 3 kullum In sha Allahu za a samu sauki.

-Wanda yake da hawan jini ko matccen jini da sauransu sai ya rinka amfani da man ridi safe da yamma.

-Ri-ga-kafin hawan jini da shan inna, wanda ya dauki man ridi a matsayin abokin rayuwarsa wato kullum zai yi amfani dashi koda cokali daya ne zai samu kariya daga wadannan cututtuka kuma koda wace irin matsala ya samu kansa ciki.

Dimbin Amfanin Aduwa Ga Jikin Dan’adam

Zaman birni ya yi tasiri ko ya bata wannan al’umma fiye da yadda ake zato.

Ko shakka babu a wannan lokaci yara da dama ba su san mecece aduwa ba, ballantana su san cewa tana da matukar amfani wajen lafiyar dan’Adam.

Baya ga shan aduwa da muke yi saboda dan zakin da take da shi, tana da kuma amfani a jikin bil Adama.

Kadan daga cikin amfanin ta, kamar yadda masana suka yi bincike a kai sun tabbatar da cewa tana maganin shawara, tsutsar ciki, gyambon ciki, farfadiya, ciwon asma, zawayi, attini da dai sauran su.

Ana samun bishiyar aduwa a kasashen Afrika da Indiya da wasu kasashen kudancin Asiya da kuma na Larabawa.

Mutanen Habasha na kiran aduwa da Kudkuda, larabawa na kiran ta da Zachun, Indiya na kiran ta Enguwa yayin da mutanen Swahili na gabashin Afrika ke kiranta Mjunju.

Man Aduwa

-Idan aka matse kwallon aduwa, ana iya samun man girki da ya kai kashi 45 cikin dari, wannan mai na kwallon aduwa na da matukar amfani idan ana dafa abinci da shi.

Yana kuma taimakawa wajen magance yawan kitse dake kawo toshewar hanyoyin jini da Asma da sauran cututtukan da muka ambata a baya.

-Asma, ana iya nika kwallon aduwa a mayar da shi gari sai a rika dibar garin kimanin cokali goma ana zubawa a ruwa kimanin cikin kofi guda, ana sha da safe har na tsawon kwanaki goma.

-Tsutsar ciki, a nan busar da kwallon aduwa ake yi a daka shi har sai ya zama gari sannan a rika zubawa a kunun gero ana sha lokaci bayan lokaci. In Allah ya yarda za a rabu da tsutsar cikin kowace iri ce dake cikin hanjin mutum ko kuma yara.

-Gyambo, a bangaren masu fama da gyambo kuma sai su samo ganyen aduwa dakakke ko kuma a daka shi a danyensa a rika wanke gyambon da shi, cikin dan kankanin lokaci in sha Allahu gyambon zai kame ko ya bushe ba tare da wani bata lokaci ba.

-Ciwon fatar jiki, a nan kuma sai a samu man da aka fitar daga jikin ‘ya’yan aduwa a rika shafawa a jiki baki daya, yana maganin kurajen jiki sosai, kazalika yana maganin sanyin kashi.

– Fitsarin jini, a kan daka bawon aduwa har sai ya zama gari, sannan a sanya a cikin ruwan da yara kan yi wanka da shi, misali kamar kududdufi domin kashe kwayoyin dake haddasa fitsarin jini da sauran wasu kwayoyin cututtuka irin su kurkunu da sauran su.

Sai dai kuma wannan yana iya kashe kifaye da su dodon kodi dake cikin ruwan ko kududdufin.

-Tinjere, bayan an dafa bawon itacen aduwa, ana shan sa ne kadan-kadan don kuwa yana maganin cutar tinjere kwarai da gaske.

-Kunburin sawu ko na jiki, domin maganin wannan cuta ta kumburin sawu ko jiki, sai a dafa saiwar aduwa a cikin miya a rika sha.

Kazalika yana maganin ciwon ciki.