Showing posts with label Labarun duniya. Show all posts
Showing posts with label Labarun duniya. Show all posts

Friday, 12 October 2018

Yanzu-Yanzu: Buhari ya sake kwato Naira biliyan 4, dala miliyan 7 daga hannun barayin gwamnati

Yanzu-Yanzu: Buhari ya sake kwato Naira biliyan 4, dala miliyan 7 daga hannun barayin gwamnati

Kwamitin nan na musamman da Shugaba Buhari ya kafa domin kwato kadarorin gwamnati dake a hannun ma'aikatan gwamnati ya ce ya samu nasarar kwato akalla Naira biliyan 4, dala miliyan 7 daga hannun barayin gwamnati. 



Shugaban kwamitin da aka dorawa alhakin kwato kadarorin, Mista Okoi Obono-Obla shine ya sanar da hakan ga manema labarai a ofishin sa a garin Abuja. 


A cewar sa, kimanin dalar Amurka miliyan 7 ce aka samu a cikin wani asusun ajiya na bankin Heritage da wani tsohon jami'in gwamnati ya boye wadanda kuma kudin na haram ne. Ya kara da cewa sauran kudaden suma an gano su ne a sauran bankunan kasar wanda tuni har an soma bin hanyar da ta dace wajen maida su inda ya kamata. A wani labarin kuma, Sarkin masarautar Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi kaca-kaca da gwamnonin Arewacin Najeriya game da daukar dukiyar al'umma da sukeyi suna anfani da ita wajen biyawa wasu tsiraru kujerar Makka duk shekara. 

Sarkin yayi wannan tsokacin ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron bita na lalubo hanyoyin da za'a rage yawan yaran da basu zuwa makaranta a yankin na Arewacin Najeriya da aka kammala a ranar Alhamis.
Labarai › Ziyarar Da Na Kaiwa Obasonjo Koyarwar Manzon Allah Ne — Sheik Gumi

Labarai › Ziyarar Da Na Kaiwa Obasonjo Koyarwar Manzon Allah Ne — Sheik Gumi



Malamin addinin Musuluncin nan mazauni Kaduna, Sheik Ahmad Gumi ya yi karin haske kan ziyarar da ya kaiwa Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasonjo inda ya nuna cewa ziyarar na daga irin koyarwar Manzon Allah.

Sheik Gumi ya ce Manzon Allah ya taba cewa yana matukar maraba da duk wata gayyata na yin sulhu ko da tsakanin wanda ba Musulmi ba ne. Ya kara da cewa idan har shugabanni na cikin zaman lafiya, to ana sa ran kasa ma za ta kasance cikin zaman lafiya.

Ya ce ya zama dole ya je domin ganin an wanzar da zaman lafiya a fadin kasar. Ya jadadda cewa shi bai ce a zabi wani ba kawai sulhu ya je. 

Malamin ya kara da cewa ko gobe aka kira shi yin sulhu zai je. Ya jadadda cewa masu fadin cewa an bashi dala, kage ne cewa babu wanda ya bashi kudi shi saboda Allah yayi. Ga cikakken biyon bayanin nasa a kasa: 


Thursday, 11 October 2018

Sanannan Malamin Addinin Musulunci Sheik Gumi da Bishop Kuka,Oyedepo,Atiku Da Obasanjo Sun Shiga Wata Ganawar Sirri

Sanannan Malamin Addinin Musulunci Sheik Gumi da Bishop Kuka,Oyedepo,Atiku Da Obasanjo Sun Shiga Wata Ganawar Sirri

Shugaban Chocin Living Faith Church Worldwide, Bishop David Oyedepo da Shugaban Roman Catholic Diocese ta Sokoto, Bishop Matthew Hassan Kukah , da sanannen malamin addinin Islama na Kaduna Dr. Gumi sun shiga wata ganawar sirri da tsohon shugaba  kasa Olusegun Obasanjo da dan takarar jamiyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar 
Ana ganawar sirrin ne a Gidan tsohon Shugaban kasa Chief OLusegun Obasanjo dake Abeokuta.
Dan takarar shugabancin kasa a karkashin PDP Alhaji Atiku Abubakar ya hallara gun taron karfe 1:07pm inhda ya wuce kai tsaye zuwa inda ake tattaunawa a  Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL), Oke-Mosan.
Ragowar mutanen da suka shiga tattaunawar sun hada da Tsohon Gwamnan Ogun , RIvers Gbenga Daniel da Liyel Imoke , se  Senator Ben Bruce among others.
Har yanzu suna cikin tattaunawa yayinda ake hada wannan rahoton.

Saturday, 6 October 2018

India :- Sharhin film din "Bajrangi Bhaijan"

India :- Sharhin film din "Bajrangi Bhaijan"


SHARHIN FIM DIN “BAJRANGI BHAIJAN”
Film ne da ya fita a ranar Edi-karama, Kabir khan shine wadda ya bada umarni wannan film.
Wadda suka fito a wannan film akwai Jarumi Salman khan, Kareena kapoor a cikakkun jarumai, wadda suka taimaka musu akwai Nawazuddin Siddiqui, Harshali Malhotra.
Film din mai dauke da mintuna 159, dai-dai 2:39 awa, Pritam shine wadda ya rera wakokin film din, a yaren Hindu akayishi inda akai translation da turanci.

A kashe masa kudi kusan 90crore (US$ 14 miliyan) , shi kuma ya kawo kusan 626crore (US$95 miliyan) , fassarar Bajrangi Bhaijaan shine ‘Dan uwa Bajrangi’.
Film ne da akai akan wata yarinya mai kimanin shekaru shida, ta gamu da tsautsayi, bayan ta kuskure a India akan hanyarsu ta tafiya da mahaifiyar wani yayi kokarin maidata garinsu Pakistan.
Mutanen kauyen Sultanpur sun taru suna kallon wasan Cricket tsakanin India da kasarsu Pakistan a tv , a cikinsu akwai wata mata mai ciki, bayan Shahid Afridi ya lashe wasan wannan mata ta haihu, Dan haka wannan mata ta sawa Yar ta suna Shahida
Yayinda takai shekara shida, watarana ta kuskure ta fada rami yayinda take kokarin tsaida abin wasanta, mahaifanta sunyi kokarin Neman ta, yayinda aka ganta da kyar
Bayan fadawa ramin da tayi sai taza ma bata iya magana, ma’ana dai baza ta iya cewa komai ba, mahaifiyarta ta damu sosai, don haka tayi niyyar kai ta Delhi (India) wajen wani mai magani ko za’a dace bakinta ya bude…..

Tuesday, 18 September 2018

wata sabuwa :- Wani Balarabe Ya Yi Tattaki Daga Kasar Moroko Akan Keke Zuwa Abuja

wata sabuwa :- Wani Balarabe Ya Yi Tattaki Daga Kasar Moroko Akan Keke Zuwa Abuja


Balaraben me suna Yasinu Riskalai ya tabbatar da cewa ya fito ne zagayen kasa kuma daga nan Abuja zai wuce kasar Kamarun.

Kuma yana zagayen ne domin akwai wasu abubuwa a cikin kasa da yake bincike akansu.


Sannan a jikin keken akwai wasu akwatuna masu dauke da alamomi na daukar sauti hadi da abinci da dai sauran su kamar yadda ya shaidawa jama'a.


Yanzu haka dai Malam Yasinu Riskalai yana cikin garin Shanga zuwa Yawuri na masarautar garin Yawuri dake jihar Kebbi.

Hoto Sani Musa Saminaka
Daga Real Sani Twoeffect Yawuri

Monday, 17 September 2018

Kalli wasu kyawawan Hotunan wasu ma Aurata

Kalli wasu kyawawan Hotunan wasu ma Aurata


Kalli wasu kyawawan Hotunan wasu ma Aurata A gaskiya gwanin Shaawa,

Wadannan Hotunan dai sun saka CEO na shafin ArewaTop and ArewaMini shaawar yin Aure nan bada jimawa.

Ga saurar hotunan kamar haka :-








Tuesday, 11 September 2018

Shugaba Buhari :- Za mu ci gaba da tatse dukiyar al'umma a hannun barayin gwamnati

Shugaba Buhari :- Za mu ci gaba da tatse dukiyar al'umma a hannun barayin gwamnati


 A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta dukufa gami da tashi tsayi irin na tsayuwar daka wajen tatse dukkanin wata dukiyar al'ummar kasar nan daga hannun barayin gwamnati.


A yayin bayyana wannan lamari na tatso dukiyar al'umma a matsayin wani tafarki na yakar cin hanci da rashawa, shugaba Buhari ya kuma yi kira ga majalisar dokoki ta tarayya akan daukar matakan shigar da sabuwar dokar hukuncin miyagun laifuka a kasar nan. Yake cewa, muddin wannan sabuwar doka ta samu shiga a kasar nan za ta kawo wani yanayi na juyin juya hali da zai saukaka tatso dukiyar al'umma daga hannun barayin gwamnati. Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatinsa ta Villa yayin karbar rahoton binciken kwamitin mutum uku da ya kafa masu kididdiga kan tatso dukiyar gwamnati da al'ummar kasar nan.

Shugaban kasar a ranar 22 ga Nuwamban 2017, ya assasasa wannan kwamitin na mutum uku da ya hadar da; Mist Olufemi Lijadu, Mrs. Gloria Chinyere Bibigha da kuma Mista Muhammad Nami.

NAIJ.com ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya sahalewa wannan kwamiti kan gudanar da duk wata kididdiga da binciken dukiya a cibiyoyi da ma'aikatun gwamnatin tarayya tun daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 22 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.


A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta dukufa gami da tashi tsayi irin na tsayuwar daka wajen tatse dukkanin wata dukiyar al'ummar kasar nan daga hannun barayin gwamnati. A yayin bayyana wannan lamari na tatso dukiyar al'umma a matsayin wani tafarki na yakar cin hanci da rashawa, shugaba Buhari ya kuma yi kira ga majalisar dokoki ta tarayya akan daukar matakan shigar da sabuwar dokar hukuncin miyagun laifuka a kasar nan. Yake cewa, muddin wannan sabuwar doka ta samu shiga a kasar nan za ta kawo wani yanayi na juyin juya hali da zai saukaka tatso dukiyar al'umma daga hannun barayin gwamnati. Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatinsa ta Villa yayin karbar rahoton binciken kwamitin mutum uku da ya kafa masu kididdiga kan tatso dukiyar gwamnati da al'ummar kasar nan. Za mu ci gaba da tatse dukiyar al'umma a hannun barayin gwamnati - Buhari Source: Twitter Shugaban kasar a ranar 22 ga Nuwamban 2017, ya assasasa wannan kwamitin na mutum uku da ya hadar da; Mist Olufemi Lijadu, Mrs. Gloria Chinyere Bibigha da kuma Mista Muhammad Nami. NAIJ.com ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya sahalewa wannan kwamiti kan gudanar da duk wata kididdiga da binciken dukiya a cibiyoyi da ma'aikatun gwamnatin tarayya tun daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 22 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata. KARANTA KUMA: Atiku ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari kan watsi da sauya fasalin kasa a jihar Kano Kawowa yanzu shugaba Buhari bai bayyana sakamakon binciken da wannan kwamitin ya gudanar, sai dai ya sha alwashi na dabbaka duk wani mataki da hukunce-hukuncen da suka dace a kai. Kazalika shugaban kasar ya bayyana rashawa a matsayin wata mummunar barazana ga tsaro gami da tattalin arzikin kasar nan tare da shan alwashi kan cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen wannan barazana a kasar nan. 

Thursday, 6 September 2018

Tuna-baya: Lokacin da Buhari ya jinjinawa tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso

Tuna-baya: Lokacin da Buhari ya jinjinawa tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso

Wani tsohon bidiyo ya zo hannun mu inda aka ji yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya rika tofawa tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso albarka a baya inda har ya nemi Allah ya sakawa Gwamnan da alheri. 



Magoya bayan Kwankwaso sun tuno da irin yabon da Shugaba Buhari da kan sa ya rika yi wa tsohon Gwamnan na Kano. Shugaba Buhari ya yabawa kokarin da Kwankwaso yayi wajen gina gidaje da kuma tituna da gadoji a Kano. Bayan nan Shugaba Buhari, ya kuma jinjinawa kokarin da Kwankwaso yayi wajen gyara harkar ilmi a Jihar Kano. Buhari ya yabawa Jami’o’in da Gwamnatin Injiniya Kwankwaso ta gina a lokacin mulkin sa a 1999 da kuma 2011. 

Buhari a wancan lokacin yake cewa duk wanda ya san Jihar Kano, lallai ta canza a lokacin Kwankwaso. Shugaba Buhari ya kara da cewa Injiniya Rabiu Kwankwaso ya nuna tattali wajen rikon Jihar Kano don haka sai dai a yaba masa.

Wednesday, 5 September 2018

APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari 2019

APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari 2019


Kasa da makonni uku kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress ( APC ), mambobin jam’iyyar babin jihar Sokoto sun tsayar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takaran da suke so ya samu tikitin jam’iyyar.
Haka zalika, jam’iyyar ta nuna amincewarta ga shugaban kungiyar sanatocin arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sannan sun bayyana shi a matsayin shugaba guda a jihar.
Wannan hukunci na daga cikin matsayar da suka tsaya kai a karshen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Sokoto a ranar Talata, 5 ga watan Satumba wadda ya samu halartan shugabannin jam’iyyar a jihar, da masu ruwa da tsaki jam’iyyar.


Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto ne ya jagoranci ganawar wadda aka gudanar cikin sirri, inda ya bayyana Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a matsayin uban jam’iyya nagari aa jihar.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban kasa na 2019.
Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.
Jam’iyyar a tsarin gudanarwan ta tace za’a samar da dan takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct” kenan a turance.

Friday, 31 August 2018

Thursday, 16 August 2018

Labarai :- An nada jarumi Ali Nuhu jakadan yaki da shan kwayoyi

Labarai :- An nada jarumi Ali Nuhu jakadan yaki da shan kwayoyi

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa jarumin dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood da kuma na Kudu, Ali Nuhu ya samu babban matsayi. 



An dai nada jarumin ne a matsayin Jakadan yaki da shan miyagun kwayoyi a karkashin gidauniyar “Big Church Foundation”

An nada jarumi Ali Nuhu jakadan yaki da shan miyagun kwayoyi Wannan dai ba shine karo na farko da jarumin ke samun irin wannan daukaka ba sakamakon tarin masoya da yake da shi. 

Ali Nuhu dai ya kasance daya daga cikin manyan jaruman fim din Hausa da zamaninsu ya haska a baya kuma yake kan haskawa, tauraron jarumin na haskawa tun zamanin da ya shiga masana’antar har izuwa yau. 

Saturday, 28 July 2018

Labarai :- Sarki Ali Nuhu ya bawa gwamna Ganduje kyautar lambar yabo, duba hoto

Labarai :- Sarki Ali Nuhu ya bawa gwamna Ganduje kyautar lambar yabo, duba hoto

Fitaccen jarumin wasannin shirin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya gabatar da kyautar lambar yabo ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahu Umar Ganduje

Ali Nuhu ya mika kyautar ne ga gwamna Ganduje da yammacin yau, Asabar, a fadar gwamnatin jihar Kano yayin gabatar da wani shirin wasan Hausa, MUTUM DA ADDININ SA, da aka shirya domin karfafa gwuiwa da ilimantar da jama’a a kan hakuri da juriyar zama da wadanda ba addininsu daya ba. 


A wani labarin na naij.com kun ji cewar shugaba Buhari ya bukaci magoya bayansa da su sassauta da yi masa yakin neman zaben shekarar 2019 domin yin hakan sabawa dokar hukmar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ne.

A jawabin da mai ba shi shawara a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya fitar a yau, Asabar, Buhari ya bukaci magoya bayansa da su yi hakuri da yi masa kamfen har sai lokacin da doka ta yarda a fara yakin neman zabe tare da shawartarsu das u cigaba da tallata aiyuka da nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Thursday, 5 July 2018

Labaran duniya :- Shugaban Kasa Muhammad bubari Ya Nada Dr Bashar Aliyu Umar A Matsayin NCRI

Labaran duniya :- Shugaban Kasa Muhammad bubari Ya Nada Dr Bashar Aliyu Umar A Matsayin NCRI


Labarai Gwamnatin tarayya ta nada Dakta Aliyu Umar, a matsayin diraktan ma’aikatar binciken irin abinci na kasa da ke Badeggi, jihar Neja. Wannan labara ya samu ne a wasikar da diraktan harkokin jama’a na ma’aikatar noma da raya karkara, Mrs A. C Bawa a madadin ministan noma, Cif Audu Ogbeh. Wani sashen wasikar tace: 
Wannan nadi zai fara aiki ranan 2 ga watan Yuili kuma zai iya zama a kujerar har na tsawon shekaru 10 muddin baka isa shekarun ritaya ba bisa ga dokokin ma’aikatar.” 
An nada Dakta Aliyu Umar ne bayan mutuwan tsohon shugaban cibiyar, Dr Samuel Agboireso, a ranan 7 ga watan Yuni, 2018.

 An haifi Dakta Aliyu Umar a shekarar 1963 kuma ya fara aiki a ma’aikatar ne tun a matsayin karamin ma’aikaci har ya zama diraktan binciken waje. 

Ya rike kujeran shugaban reshen Uyo, Akwa Ibom da Amakama, jihar Abiya a shekarun baya. Ya samu kwalin doktoransa a ilimin kimiyar kasan noma daga jami’ar fasaha na Minna wato FUT Minna.