Saturday, 6 October 2018




India :- Sharhin film din "Bajrangi Bhaijan"

Home India :- Sharhin film din "Bajrangi Bhaijan"

Anonymous

Ku Tura A Social Media

SHARHIN FIM DIN “BAJRANGI BHAIJAN”
Film ne da ya fita a ranar Edi-karama, Kabir khan shine wadda ya bada umarni wannan film.
Wadda suka fito a wannan film akwai Jarumi Salman khan, Kareena kapoor a cikakkun jarumai, wadda suka taimaka musu akwai Nawazuddin Siddiqui, Harshali Malhotra.
Film din mai dauke da mintuna 159, dai-dai 2:39 awa, Pritam shine wadda ya rera wakokin film din, a yaren Hindu akayishi inda akai translation da turanci.

A kashe masa kudi kusan 90crore (US$ 14 miliyan) , shi kuma ya kawo kusan 626crore (US$95 miliyan) , fassarar Bajrangi Bhaijaan shine ‘Dan uwa Bajrangi’.
Film ne da akai akan wata yarinya mai kimanin shekaru shida, ta gamu da tsautsayi, bayan ta kuskure a India akan hanyarsu ta tafiya da mahaifiyar wani yayi kokarin maidata garinsu Pakistan.
Mutanen kauyen Sultanpur sun taru suna kallon wasan Cricket tsakanin India da kasarsu Pakistan a tv , a cikinsu akwai wata mata mai ciki, bayan Shahid Afridi ya lashe wasan wannan mata ta haihu, Dan haka wannan mata ta sawa Yar ta suna Shahida
Yayinda takai shekara shida, watarana ta kuskure ta fada rami yayinda take kokarin tsaida abin wasanta, mahaifanta sunyi kokarin Neman ta, yayinda aka ganta da kyar
Bayan fadawa ramin da tayi sai taza ma bata iya magana, ma’ana dai baza ta iya cewa komai ba, mahaifiyarta ta damu sosai, don haka tayi niyyar kai ta Delhi (India) wajen wani mai magani ko za’a dace bakinta ya bude…..

Share this


Author: verified_user

0 Comments: