Showing posts with label Naija News. Show all posts
Showing posts with label Naija News. Show all posts

Sunday, 13 January 2019

NEWS:- Yanda Wani Mai Gida Ya Kashe Matarshi Da Dan Uwanshi Da Yakama Suna Lalata

NEWS:- Yanda Wani Mai Gida Ya Kashe Matarshi Da Dan Uwanshi Da Yakama Suna Lalata

tw
Cin amana abune me matukar
bata rai da karya zuciyar
wanda akawa, musamman
idan cin amanar aurece ko
kuma tsakanin masoya kuma
ace da wanda baka tsammanine, hakane ta faru da
wani magidanci inda ya kama
kaninshi da matarshi turmi da
tabarya.
Oleg Kirkunov dan kasar Rasha
me shekaru 54 ya gayyaci dan uwanshi, Evgeny me shekaru
65 gidanshi inda suka ci abincin
dare aka yi zumunci, saboda
dare yayi sai dan uwan me
gidan yace zai kwana kamin da
safe ya wuce, kamar yanda The Sun UK ta ruwaito.
Tsakar dare Oleg ya irin juya
dinnan sai baiga matarshi kusa
dashi ba, sai ya tashi ya tafi
nemanta, yana tsakar gida sai
ya jiyo motsi/nishi a wani daki, ya karasa, ai kuwa sai yaga
abinda bai yi tsammani ba,
matarshi ce da dan uwanshi
suke lalata.
Dama mafaraucine, sai kawai
ya dauko bindigarshi ta farauta ya kakkabe, ya dirkawa
matarshi harsashi a kai, dan
uwan nashima da yaga haka
sai yayi sauri ya saka kaya dan
ya tsere, aikuwa shima be
barshi ba, ya dirka mishi harsashi, nan duk su biyun suka
Tafi a mace.
Oleg na gama harbe su sai ya
dauki waya ya kira 'yan sanda
yace musu ga abinda ya aikata,
nan aka zo aka tafi dashi. Rahotanni sun bayyana cewa,
za'a ajiyeshi nan zuwa watanni kamin a gama bincike
dan yanke mai hukunci.
Saidai wani abin ban mamaki
da ya faru shine, mutane da dama a shafukan sadarwa na
yanar gizo sun jinjinawa
magidancin da wannan kisan
da yawa matarshi da dan
uwanshi inda suka rika kiranshi
da gwarzo. Wasu ma sunce ko da sune
abinda zasu aikata kenan, basu
damu da zaman gidan yari ba.

Wednesday, 26 December 2018

NEWS:- Dattawan Jihar Kano Sun Bukaci Yan Sanda Su Binciki Gwamna Ganduje.

NEWS:- Dattawan Jihar Kano Sun Bukaci Yan Sanda Su Binciki Gwamna Ganduje.


Kimanin makonni biyu bayan da babbar kotun Kano ta haramtawa Majalisar dokokin Jihar bincikar faifen bidiyon dake zargin gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hancin dala miliyan biyar, dattawan Kano sunce akwai bukatar gwamnan ya yiwa al'umar jihar bayani da zai gamsar da su game da zargin.

Hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da jama'a ke korafi kan yadda dattawan na Kano suka ki cewa uffan tun bayan da Jaridar Daily Nigeria ta fara kwarmata zargin karbar rashawar akan gwamna Ganduje.

Daya daga cikin dattawan Jihar Kano, Alhaji Gidado Mukhtar, yace abu na farko da ya sa dattawan ba su yi magana ba shine domin maganar tana gaban kotu, da bisa doka bai kamata a saurara, na biyu kuma magana irin wannan idan ta taso ya mata a tsaya a ga inda ta gangara kafin aga mene ne a ciki.

Gidado yakara da cewa tunda kotu tayi hukunci ‘yan sanda suna da hakki da kuma damar su bincika wannan zargi da ake yiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yanzu suna sauraron ‘yan sanda su yi aikin daya kamata wajen bincikar wannan zargin karbar cin hancin.
PLEASE KUDINGA SHARING POSTING DINMU A FACEBOOK DA WHATSAPP 

Sunday, 23 December 2018

NEWS:- Yakamata EFCC Ta Binciki Ganduje - Inji Hajiya Naja'atu

NEWS:- Yakamata EFCC Ta Binciki Ganduje - Inji Hajiya Naja'atu

tw
Maciji Duk Maciji Ne Kuma Kunama Duk
Kunama Ce - Naja'atu
Hajiya Naja'atu ta ce ba daidai ba ne
hukumar EFCC ta juya baya a kan batun
bidiyon Ganduje, don kuwa ita da 'yan
sanda suna da ikon su yi bincike don tabbatarwa ko wanke zargin da ake yi.
Ta ce ita ba ta yarda ba satar da dukiyar
jama'a ba, ko daga wacce jam'iyya yake.
"Maciji duk maciji ne, kowanne ne daga
PDP yake ko daga APC, zai yi sara ne ya
cutar da mutane. Azzalumi, azzalumi ne. Kunama ce idan za ta harbe ki, ko wacce
irin tuta ta dauka, sunanta kunama. Kisa
za ta yi!
Ni a ce an bar wani saboda kawai yana
APC, ni wannan ban yarda da shi ba.
Saboda an zalunci, zalunci ne."
please Ku tura zuwa sauran Groups

Friday, 21 December 2018

NEWS:- sheikh Dahiru Bauchi Yayiwa Atiku Addu'a

NEWS:- sheikh Dahiru Bauchi Yayiwa Atiku Addu'a


                      

Sheikh Dahiru Bauchi Yayi Wa Atiku Abubakar Addu’a
Babban Shaihin Darikar Tijjaniyah A Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Yayi Addu’a Ga Dan Takarar Kujerar Shugabancin Najeriya Karkashin PDP Alhaji Atiku Abubakar, A Ziyara Ta Musanman Da Dan Siyasar Ya Kaiwa Malamin A Gidanshi Dake Bauchi

Tuesday, 18 December 2018

Kalli Yanda Yan Hisba Suka Tarwasa Auren Yan Madigo A Jahar Kano

Kalli Yanda Yan Hisba Suka Tarwasa Auren Yan Madigo A Jahar Kano

tw
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama
mata akalla 11 a Sabon Gari dake karamar
hukumar Fagge bisa zargin shirya
shagalin auren madigo, kamar yadda
jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito. Jami’in sintiri na Hukumar Hisbah Nasiru
Ibrahim ya bayyana cewa, sun samu
bayanan sirri na cewa, Safiyya Yobe ce za
ta auri Fatima Gezawa yayin shagalin.
Wanda hakan ya sa suka kai sumame
gami da cafke Mata 11 ciki har da ANGUWA (Wacce zata yi auren) da
AMARYA (Wacce za a aura). Sai dai daya daga cikin matan da aka
kama Fati Jaririyar Zuciya ta bayyana
cewa, sun shirya wannan shagali ne
domin taya AMARYA Fatima Gezawa ba
ta mukamin mataimakiyar shugabar
gidan rawa, wanda ANGUWA Safiyya Yobe ce shugaba. A Afirilun 2007, an samu makamancin
wannan sumame a jihar Kano inda aka
zargi wata ‘Aunty Maiduguri’ da laifin
AUREN MATA hudu (4) yayin shirya
shagalin tarawa wata Kilaki kudi da za
ta auri Namiji.
DANNA HOTON DAKE KASA DAN KALLON SAURAN HOTON,
please Ku tura zuwa sauran Groups

Tuesday, 16 October 2018

Gwamnati ta yi tir da kisan ma’aikaciyar ‘Red Cross’ Hauwa Liman da Boko Haram suka yi

Gwamnati ta yi tir da kisan ma’aikaciyar ‘Red Cross’ Hauwa Liman da Boko Haram suka yi

Gwamnatin Najeriya ta yi tir da kisan ma’aikaciyar Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC) Hauwa Liman da Boko Haram suka yi a yau Litini.

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya sanar da haka a Abuja inda ya jajanta wa iyaye da yan ‘uwan Hauwa Liman.


Ya kuma mika godiyarsa ga gwamnatocin duniya kan saka bakin da suka yi don ganin a ceto wadannan ma’aikata da Boko Haram suka kama.

” Gwamnatin Najeriya ta yi iya kokarin ta wajen ganin Boko Haram sun sako wadannan mutane da suka kama sai dai hakan bai haifar mana da da mai ido ba.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne Boko Haram ta fitar da sanarwar cewa cikin awa 24 za su kara bindige ma’aikaciyar Red Cross daga cikin wadanda suka kama.

Shugaban Kungiyar mai kula da ayyuka a yankin Tafkin Chadi, Mamadou Sow ya ce Boko Haram sun kama Hauwa Mohammed , Alice Loksha da Saifura Khorsa a watan Maris. Inda bayan watanni shida da kama su Boko Haram suka kashe Saifura cikin Satumba.

” Boko haram sun kama ma’aikatan ICRC ne yayin da suke aikin bada agaji a sansanin gudun hijira da ke Rann, sannan sune kuma ke tsare da Leah Sharibu’’.

A dalilin haka Sow ya roki Gwamnatin Tarayya da masu fada aji da su sa baki domin ceto sauran da ke hannu Boko Haram.

Sai dai duk wannan roke roken bai haifar wa kasa da ICRC da da mai ido ba domin Boko Haram sun bindige Hauwa Liman.
Premiumtimeshausa

Monday, 15 October 2018

Saturday, 11 August 2018

Ahmad Musa ya samu kyakkyawar tarba daga larabawan kasar Saudiyya

Ahmad Musa ya samu kyakkyawar tarba daga larabawan kasar Saudiyya

Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya watau Super Eagles mai suna Ahmad Musa ya bayyana matukar jin dadin sa da irin kyakkyawar tarbar da ya samu daga larabawan Saudiyya.
Idan ba'a manta ba fitaccen dan kwallon dai mai shekaru 25 a duniya ya sauya kungiyar kwallon sa ne ta Leicester City ya zuwa kungiyar kwallon Al-Nassr dake a kasar ta Saudiyya.

NAIJ.com ta samu cewa sai da jim kadan da saukar sa a kasar ta Saudiyya ne sai kawai cincirindon masoya kwallo musamman ma na sabuwar kungiyar ta sa suka zagaye shi suna murnar komawar tasa.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa fitaccen dan wasan tauraruwar sa ta haska sosai a gasar cin kofin duniya da ya gabata a kasar Rasha inda ya samu zura kwallaye biyu ringis a lokacin da Najeriya ta kara da kasar Iceland.

Monday, 30 July 2018

Mairama Indimi da Angonta Mustafa Masango sunyi aure na biyu na farar riga a kasar Faransa

Mairama Indimi da Angonta Mustafa Masango sunyi aure na biyu na farar riga a kasar Faransa

Amarya, 'yar gidan attajirin dan kasuwarnan dake garin Maiduguri, Mairama Indimi da Angonta, Mustafa Marcus Masango sunyi aure na biyu na farar riga a kasar Faransa, ranar Asabar din data gabata.


A watan Disambar shekarar 2017 data gabatane aka daurawa masoyan biyu aure bisa tsari irin na addinin musulunci aka kuma gudanar da shagulgula irin na al'ada.





Sunday, 22 July 2018

An dawo da ‘yan Najeriya da suka makale a Rasha bayan da sukaje kallon gasar kofin Duniya

An dawo da ‘yan Najeriya da suka makale a Rasha bayan da sukaje kallon gasar kofin Duniya

An dawo da 'Yan Najeriya 155 da suka makale a Rasha bayan kammala gasar cin kofin duniya.


A ranar juma'a da dare ne jirgin da ya kwaso su ya sauka Abuja.

Ministan harakokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama wanda ya tarbe su bayan isowarsu Abuja, ya ce gwamnati ta yi shatar jirgi ne domin dawo da su gida.

Mista Onyeama wanda ya wallafa hotunan isowar 'yan Najeriyar a shafinsa na Twitter ya ce shugaba Buhari ne ya bukaci a gaggauta dawo da su daga Rasha.

'Yan Najeriyar wadanda suka tafi domin domin marawa Super Eagles baya a wasannin gasar cin kofin duniya sun makale ne a Rasha saboda matsalar kudi.

Wasunsu sun tare ne a ofishin jekadancin Najeriya bayan sun makale a Rasha.

Gwamnati Najeriya na zargin kamfanonin da suka yi dillacin tafiya da su ne suka soke tikitin dawo wa da su ba tare da sun sanar da su ba.

Ministan ya ce ofishin jekadancin Najeriya ne ya dauki nauyin kula da wurin kwanansu da kuma abinci a Moscow kafin a dawo da su.
BBCHausa.

Saturday, 14 July 2018

Thursday, 28 June 2018

Karanta kuji  Sakon Ummi Zeze Zuwa ga yan Nigeria

Karanta kuji Sakon Ummi Zeze Zuwa ga yan Nigeria

tw
Ga Sakon Tsohuwar Jarumar Fim
Ummi Zeezee Zuwa Ga Yan Nigeria Ta
Rubuta Wannan Sakon A Shafin
Instagram Dinta ""Salam dear nigerians ,wasu suna
amfani da sunana a face book
sunamin karya iri iri da kuma bata
suna a gareni Wanda ina kyautata
zaton masoyan APC ne.hakan ya samo
asaline domin sunsan bana shiri da boss dinsu Mr president.last week sun
hada hotona Dana wani gardin banza
a daji wai yana lalata dani sukaga
hoton baiyi tasiri ba domin Allah ba
azzalumin bawansa bane baya kuma
kama bawa da laifin da bai aikata ba.to da suka ga hotona da suka hada
da gardi Wanda kuke cewa timaya ne
baiyi tasiri ba sai kuma suka dawo
suka ce wai ni yar shi'A ce,shima suka
ga baiyi tasiri ba da suka dangan tani
da shi'A.sai kuma yau suka sake cewa wai na fita daga shi'A har na dawo
ina addu'a Allah ya dauwa Mar da "sir
zazzaky " a gidan yari .to karya ake
min ni Sam banyi maganah akan sir
zazzaky cewar Allah ya dauwa Mar
dashi a gidan yari ba domin ni ina tsananin girmama sir zazzaky saboda
sunansa daya Dana mahaifina kuma
ni aduniya duk mai sunan mahaifina
to ina daraji shi saboda duk mai
sunan kallon uba nake masa a
sakamakon kaunar da nakewa babana sosai.dan haka karya akemin . Kuma ku masu son batamin suna ina
son ku sani cewa annabi Muhammad
s.a.w.yace :in duniya zata taru bata
ISA ta daurawa bawa abunda Allah
bai dauramasa ba na masifa ko alkairi
haka kuma yace in da duniya zata taru bata ISA ta daukewa bawa
abunda Allah ya daurawa bawansa
na masifa ko alkairi.dan haka na
dogara ga Allah kuma zai kare ni a
bisa sharrin da kukemin iri iri akan
buhari.sannan naji kunce na tuba wai na dena adawa da buhari ko ?to
shima karya kukemin.ni yanzu ma na
fara adawa dashi indai akan siyasa
ne ,nagode. daga ummi ibrahim(zeezee)""
source @sadikblog

Tuesday, 1 May 2018

Na auri Buduruwa mai Tarbiya Kuma  a gida mai Tarbiya Inji - Idris wanda ya Auri Fatima Ganduje

Na auri Buduruwa mai Tarbiya Kuma a gida mai Tarbiya Inji - Idris wanda ya Auri Fatima Ganduje

tw
image ©

Dan gwamnan jihar Oyo, Angon Fatima
Abdullahi Umar Ganduje ya kare
matarshi yayin da wani yace mai ya auri
mara tarbiyya daga gidan da babu
tarbiyya, Idris ya baiwa wanda ya
gayamishi wannan magana amsa da cewa shigar da matar tashi tayi tayi kyau
kuma ta mai. Ya tambayi wanda yayi maganar cewa '
Kai gidan da ka fito akwai tarbiyya?'. A karshe Idris ya bayyana cewa ya auri
budurwa mafi kyawun/tarbiyya daga
arewa.

Wednesday, 28 February 2018

Hotunan Zuwan Yusuf Buhari Gida Najeriya daga Jinya a Kasar Jamus

Hotunan Zuwan Yusuf Buhari Gida Najeriya daga Jinya a Kasar Jamus

tw
image ©
Hotunan Dan Shugaban Kasa Najeriya Yusuf Buhari Yayin Hadarin Dayayi a Babur a kwanakin Baya Yagama Jinyarshi ne a Kasar Jamus yaji rauni a cikin kwakwalwarshi a halin yanxu de yusuf yasamu sauki
muna fatan Allah yarufa asiri nangaba Munayi masa fatan Alheri allah yakara lpy amin...
Please Share our post to another Social Media
tw
tw
tw

Sunday, 25 February 2018

Yadda Wani Katon banza Ya Auri Kanwarsa Ta jini

Yadda Wani Katon banza Ya Auri Kanwarsa Ta jini

Wani lamari mai cike da daure kai ya auku a jihar Anambara dake yankin kudu maso gabashin kasar nan inda muka samu labarin cewa wani malamin lissafi a makarantar sakandare a karamar hukumar Aguata mai suna Chiadikobi Ezeibekwe, ya auri kanwar sa ta jini. Kamar dai yadda muka samu shine
kanwar ta sa da ya aura tana da shekara
17 ne a duniya kuma Mista Chiadikobi
Ezeibekwe ya bayyana cewa Allah ne ya
kaddara zai auri kanwar ta sa inda ya
kuma ce shi bai yi nadamar aikata hakan ba domin kuma ko a cikin addinin
kiristanci ba bu inda aka haramta hakan.
tw
image ©
NAIJ.com ta samu cewa sai dai daga
baya mafusatan matasa a garin da
lamarin ya auku sun tayar da tarzoma
tare da kona cocin da aka daura auren. A wani labari kuma, Wani gungun
al'umma mabiya addinin kirista dake a
yankin arewacin Najeriya karkashin
inuwar kungiyar Kiristoci da kuma
fastoci 'yan asalin arewacin Najeriya din
watau Arewa Christians and Indigenous Pastors Association a turance sun yi kira
ga daukacin al'ummar duniya da su
taimaka su tsame su daga mulkin
shugaba Buhari. Wasu daga cikin manyan shugabanni da
kuma hukumonin duniyar da kungiyar ta
rubutawa takarda sun hada tarayyar
Afirka, gamayyar kasashen turai da
kuma kasashe renon Ingila.