Sunday, 13 January 2019




NEWS:- Yanda Wani Mai Gida Ya Kashe Matarshi Da Dan Uwanshi Da Yakama Suna Lalata

Home NEWS:- Yanda Wani Mai Gida Ya Kashe Matarshi Da Dan Uwanshi Da Yakama Suna Lalata

Anonymous

Ku Tura A Social Media
tw
Cin amana abune me matukar
bata rai da karya zuciyar
wanda akawa, musamman
idan cin amanar aurece ko
kuma tsakanin masoya kuma
ace da wanda baka tsammanine, hakane ta faru da
wani magidanci inda ya kama
kaninshi da matarshi turmi da
tabarya.
Oleg Kirkunov dan kasar Rasha
me shekaru 54 ya gayyaci dan uwanshi, Evgeny me shekaru
65 gidanshi inda suka ci abincin
dare aka yi zumunci, saboda
dare yayi sai dan uwan me
gidan yace zai kwana kamin da
safe ya wuce, kamar yanda The Sun UK ta ruwaito.
Tsakar dare Oleg ya irin juya
dinnan sai baiga matarshi kusa
dashi ba, sai ya tashi ya tafi
nemanta, yana tsakar gida sai
ya jiyo motsi/nishi a wani daki, ya karasa, ai kuwa sai yaga
abinda bai yi tsammani ba,
matarshi ce da dan uwanshi
suke lalata.
Dama mafaraucine, sai kawai
ya dauko bindigarshi ta farauta ya kakkabe, ya dirkawa
matarshi harsashi a kai, dan
uwan nashima da yaga haka
sai yayi sauri ya saka kaya dan
ya tsere, aikuwa shima be
barshi ba, ya dirka mishi harsashi, nan duk su biyun suka
Tafi a mace.
Oleg na gama harbe su sai ya
dauki waya ya kira 'yan sanda
yace musu ga abinda ya aikata,
nan aka zo aka tafi dashi. Rahotanni sun bayyana cewa,
za'a ajiyeshi nan zuwa watanni kamin a gama bincike
dan yanke mai hukunci.
Saidai wani abin ban mamaki
da ya faru shine, mutane da dama a shafukan sadarwa na
yanar gizo sun jinjinawa
magidancin da wannan kisan
da yawa matarshi da dan
uwanshi inda suka rika kiranshi
da gwarzo. Wasu ma sunce ko da sune
abinda zasu aikata kenan, basu
damu da zaman gidan yari ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: