Showing posts with label Naija News. Show all posts
Showing posts with label Naija News. Show all posts

Sunday, 13 January 2019

NEWS:- Yanda Wani Mai Gida Ya Kashe Matarshi Da Dan Uwanshi Da Yakama Suna Lalata

NEWS:- Yanda Wani Mai Gida Ya Kashe Matarshi Da Dan Uwanshi Da Yakama Suna Lalata

tw
Cin amana abune me matukar
bata rai da karya zuciyar
wanda akawa, musamman
idan cin amanar aurece ko
kuma tsakanin masoya kuma
ace da wanda baka tsammanine, hakane ta faru da
wani magidanci inda ya kama
kaninshi da matarshi turmi da
tabarya.
Oleg Kirkunov dan kasar Rasha
me shekaru 54 ya gayyaci dan uwanshi, Evgeny me shekaru
65 gidanshi inda suka ci abincin
dare aka yi zumunci, saboda
dare yayi sai dan uwan me
gidan yace zai kwana kamin da
safe ya wuce, kamar yanda The Sun UK ta ruwaito.
Tsakar dare Oleg ya irin juya
dinnan sai baiga matarshi kusa
dashi ba, sai ya tashi ya tafi
nemanta, yana tsakar gida sai
ya jiyo motsi/nishi a wani daki, ya karasa, ai kuwa sai yaga
abinda bai yi tsammani ba,
matarshi ce da dan uwanshi
suke lalata.
Dama mafaraucine, sai kawai
ya dauko bindigarshi ta farauta ya kakkabe, ya dirkawa
matarshi harsashi a kai, dan
uwan nashima da yaga haka
sai yayi sauri ya saka kaya dan
ya tsere, aikuwa shima be
barshi ba, ya dirka mishi harsashi, nan duk su biyun suka
Tafi a mace.
Oleg na gama harbe su sai ya
dauki waya ya kira 'yan sanda
yace musu ga abinda ya aikata,
nan aka zo aka tafi dashi. Rahotanni sun bayyana cewa,
za'a ajiyeshi nan zuwa watanni kamin a gama bincike
dan yanke mai hukunci.
Saidai wani abin ban mamaki
da ya faru shine, mutane da dama a shafukan sadarwa na
yanar gizo sun jinjinawa
magidancin da wannan kisan
da yawa matarshi da dan
uwanshi inda suka rika kiranshi
da gwarzo. Wasu ma sunce ko da sune
abinda zasu aikata kenan, basu
damu da zaman gidan yari ba.

Wednesday, 26 December 2018

NEWS:- Dattawan Jihar Kano Sun Bukaci Yan Sanda Su Binciki Gwamna Ganduje.

NEWS:- Dattawan Jihar Kano Sun Bukaci Yan Sanda Su Binciki Gwamna Ganduje.


Kimanin makonni biyu bayan da babbar kotun Kano ta haramtawa Majalisar dokokin Jihar bincikar faifen bidiyon dake zargin gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hancin dala miliyan biyar, dattawan Kano sunce akwai bukatar gwamnan ya yiwa al'umar jihar bayani da zai gamsar da su game da zargin.

Hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da jama'a ke korafi kan yadda dattawan na Kano suka ki cewa uffan tun bayan da Jaridar Daily Nigeria ta fara kwarmata zargin karbar rashawar akan gwamna Ganduje.

Daya daga cikin dattawan Jihar Kano, Alhaji Gidado Mukhtar, yace abu na farko da ya sa dattawan ba su yi magana ba shine domin maganar tana gaban kotu, da bisa doka bai kamata a saurara, na biyu kuma magana irin wannan idan ta taso ya mata a tsaya a ga inda ta gangara kafin aga mene ne a ciki.

Gidado yakara da cewa tunda kotu tayi hukunci ‘yan sanda suna da hakki da kuma damar su bincika wannan zargi da ake yiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yanzu suna sauraron ‘yan sanda su yi aikin daya kamata wajen bincikar wannan zargin karbar cin hancin.
PLEASE KUDINGA SHARING POSTING DINMU A FACEBOOK DA WHATSAPP 

Sunday, 23 December 2018

NEWS:- Yakamata EFCC Ta Binciki Ganduje - Inji Hajiya Naja'atu

NEWS:- Yakamata EFCC Ta Binciki Ganduje - Inji Hajiya Naja'atu

tw
Maciji Duk Maciji Ne Kuma Kunama Duk
Kunama Ce - Naja'atu
Hajiya Naja'atu ta ce ba daidai ba ne
hukumar EFCC ta juya baya a kan batun
bidiyon Ganduje, don kuwa ita da 'yan
sanda suna da ikon su yi bincike don tabbatarwa ko wanke zargin da ake yi.
Ta ce ita ba ta yarda ba satar da dukiyar
jama'a ba, ko daga wacce jam'iyya yake.
"Maciji duk maciji ne, kowanne ne daga
PDP yake ko daga APC, zai yi sara ne ya
cutar da mutane. Azzalumi, azzalumi ne. Kunama ce idan za ta harbe ki, ko wacce
irin tuta ta dauka, sunanta kunama. Kisa
za ta yi!
Ni a ce an bar wani saboda kawai yana
APC, ni wannan ban yarda da shi ba.
Saboda an zalunci, zalunci ne."
please Ku tura zuwa sauran Groups

Friday, 21 December 2018

NEWS:- sheikh Dahiru Bauchi Yayiwa Atiku Addu'a

NEWS:- sheikh Dahiru Bauchi Yayiwa Atiku Addu'a


                      

Sheikh Dahiru Bauchi Yayi Wa Atiku Abubakar Addu’a
Babban Shaihin Darikar Tijjaniyah A Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Yayi Addu’a Ga Dan Takarar Kujerar Shugabancin Najeriya Karkashin PDP Alhaji Atiku Abubakar, A Ziyara Ta Musanman Da Dan Siyasar Ya Kaiwa Malamin A Gidanshi Dake Bauchi

Tuesday, 18 December 2018

Kalli Yanda Yan Hisba Suka Tarwasa Auren Yan Madigo A Jahar Kano

Kalli Yanda Yan Hisba Suka Tarwasa Auren Yan Madigo A Jahar Kano

tw
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama
mata akalla 11 a Sabon Gari dake karamar
hukumar Fagge bisa zargin shirya
shagalin auren madigo, kamar yadda
jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito. Jami’in sintiri na Hukumar Hisbah Nasiru
Ibrahim ya bayyana cewa, sun samu
bayanan sirri na cewa, Safiyya Yobe ce za
ta auri Fatima Gezawa yayin shagalin.
Wanda hakan ya sa suka kai sumame
gami da cafke Mata 11 ciki har da ANGUWA (Wacce zata yi auren) da
AMARYA (Wacce za a aura). Sai dai daya daga cikin matan da aka
kama Fati Jaririyar Zuciya ta bayyana
cewa, sun shirya wannan shagali ne
domin taya AMARYA Fatima Gezawa ba
ta mukamin mataimakiyar shugabar
gidan rawa, wanda ANGUWA Safiyya Yobe ce shugaba. A Afirilun 2007, an samu makamancin
wannan sumame a jihar Kano inda aka
zargi wata ‘Aunty Maiduguri’ da laifin
AUREN MATA hudu (4) yayin shirya
shagalin tarawa wata Kilaki kudi da za
ta auri Namiji.
DANNA HOTON DAKE KASA DAN KALLON SAURAN HOTON,
please Ku tura zuwa sauran Groups

Tuesday, 16 October 2018

Gwamnati ta yi tir da kisan ma’aikaciyar ‘Red Cross’ Hauwa Liman da Boko Haram suka yi

Gwamnati ta yi tir da kisan ma’aikaciyar ‘Red Cross’ Hauwa Liman da Boko Haram suka yi

Gwamnatin Najeriya ta yi tir da kisan ma’aikaciyar Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC) Hauwa Liman da Boko Haram suka yi a yau Litini.

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya sanar da haka a Abuja inda ya jajanta wa iyaye da yan ‘uwan Hauwa Liman.


Ya kuma mika godiyarsa ga gwamnatocin duniya kan saka bakin da suka yi don ganin a ceto wadannan ma’aikata da Boko Haram suka kama.

” Gwamnatin Najeriya ta yi iya kokarin ta wajen ganin Boko Haram sun sako wadannan mutane da suka kama sai dai hakan bai haifar mana da da mai ido ba.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne Boko Haram ta fitar da sanarwar cewa cikin awa 24 za su kara bindige ma’aikaciyar Red Cross daga cikin wadanda suka kama.

Shugaban Kungiyar mai kula da ayyuka a yankin Tafkin Chadi, Mamadou Sow ya ce Boko Haram sun kama Hauwa Mohammed , Alice Loksha da Saifura Khorsa a watan Maris. Inda bayan watanni shida da kama su Boko Haram suka kashe Saifura cikin Satumba.

” Boko haram sun kama ma’aikatan ICRC ne yayin da suke aikin bada agaji a sansanin gudun hijira da ke Rann, sannan sune kuma ke tsare da Leah Sharibu’’.

A dalilin haka Sow ya roki Gwamnatin Tarayya da masu fada aji da su sa baki domin ceto sauran da ke hannu Boko Haram.

Sai dai duk wannan roke roken bai haifar wa kasa da ICRC da da mai ido ba domin Boko Haram sun bindige Hauwa Liman.
Premiumtimeshausa

Monday, 15 October 2018