Showing posts with label Nishadi. Show all posts
Showing posts with label Nishadi. Show all posts

Monday, 31 December 2018

ALAMOMIN DA ZAKA GANE BUDURWA TAFI SONKA CIKIN SAMARIN TA

ALAMOMIN DA ZAKA GANE BUDURWA TAFI SONKA CIKIN SAMARIN TA

Yan samari yau kuna tare da ni zan danyi muku taqaitaccen bayani akan wannan ALAMOMIN.

kamar yadda kuka sani yan mata na tara samari kamar guda 4 ko 5 kowanne kuma ta ware masa lokutan hira kuma kowa yasan bashi kadai yakazuwa ba.
INKASAMU KANKA A IRIN WANNAN HALIN TO GA KADAN DAGA YADDA ZAKA GANE TAFI SONKA AKAN SAURAN


1 Yikokari kabata zobanka, inda baka bataba tare dafadamata mahimmancinsa agunka danunamata bukatunka na tarikeshi amana.
MATUQAR TANA SONKA SOSAI ZAKAGA TANA SASHI A MAFIYA LOKUTANTA MUSAMMAN MA SADDA ZAKA ZO GUNTA,
zatana baka labri ai anyi anyi tabayar taki bayarwa koda yabata zatafada.

2 Bata gajiya dakai
idan mafiya yawan lokutan da kakezuwa kaga bata gajiya dakai batafiya yima korafi ba, kamar kanta naciwo, ko bacci takeji da sauransu wato irin karyarnan ta yanmata in sunwa samari 2 alkawari suzo zance gunsu ko ansami clishing.

3 TABAka LOKUTA FIYE DA NA SAURA:
yana daga alamar budurwa tafi sonka acikin samarinta taba ka lokuta dayawa fiye da na sauransu MUSALI IN TABAWA KOWA 1,KO 2 A SATI TO KAI 3 KO 4,KOMA DUK SADDA KACEMATA SAI YAUSHE TACEMA GOBE .

4 TANA SALLAMAR SAURAYI SABO DAKAI:
musali in tana hira da wani da kaje zakaga ta sallame shi ta dawo gareka bada bata lokaciba.

5 BATA ZUWA GUN WANI SAURAYIN HIRA SAI DA IZININKA KO KA TILASTAMATA.
musali inkuna zance da ita WANI YAZO hira gunta zakaga bata son zuwa sai ka tilastama koma ta tambayeka izini ,kuma tacema DAN ALLAH KARKATAFI SALLAMAR SA ZATAYI,koda taje zakaga hankalinta a kanka .

6ZAKAJI SUNANKA YAFITASHI A GUN QAWAYENTA: kawayenta sune nakusa da ita sunfi kowa sanin watafi so DANHAKA ZAKAJI SUNA DANGANTAKA DA ITA SOSAI FIYE DA SAURAN SAMARIN.

7 ZAKAGA TANA BAKA KULAWA TA SOYAYYA FIYE DA SAURAN :
kamar aikoma da sakonni musamman in kana turamata kaima yawaita kiranka nuna tausayinta agareka, ,chatin dakai sosai.fadama kalaman soyayya

8 GIRMAMA LOKUTAN ZUWANKA:
musali intasan zakazo zatayima wanka, zakasameta da fara ah,da annashuwa.kula da kiranka a waya,fitowa da wuri da ka aika dan aike a mafiya lokuta

9 yawan fadama GASKIYA a al amuranta da wasu surrukanta.

Friday, 28 December 2018

AMARCI A KASAR HAUSA

AMARCI A KASAR HAUSA

An yi wata kyakkyawar budurwa da ke zaune a daya daga cikin jihohin Arewa mai suna Salma (ba sunanta na gaskiya ba).  Salma ta kasnace yarinya ce mai natsuwa da yin biyayya ga iyayenta daidai gwargwado.  Sunan mahaifinta Alhaji Balarabe yayin da mahaifiyarta kuma Hajiya Maryam.  Alhaji Balarabe mutum ne mai dukiya daidai gwargwado, domin hamsakin dan kasuwa ne.  Ya yi karatun zamani, amma bai taba yin aikin gwamnati ba, sai ya tsunduma cikin harkokin kasuwanci.  Kafin kankanen lokaci Allah Ya azurta shi, inda ya mallaki kadarori masu yawa da suka hada da manyan shaguna da gidaje da motocin dakon kaya da na sufuri da kuma motocin shiga.  Ya dauki ma’aikata da dama da ke cin abinci a karkashinsa.

ADVERTISEMENT

Mutum ne mai son taimakon al’umma, don haka jama’a ke tururuwa zuwa gidansa don neman taimako. Kuma daidai gwargwado yakan taimaka wa al’umma, hakan ta sa jama’a ke yawan yi masa addu’a da fatan alheri.

Alhaji Balarabe ya dade bai samu haihuwa ba, ya kwashe shekaru masu yawa kafin ya samu haihuwar ’ya da ya sanya mata suna Salma.

Iyayen Salma sun nuna mata gata wajen sanya ta a makaranta har ta yi karatun jami’a.

Salma ta shaku da mahaifinta Alhaji Balarabe, don haka ba ta boye masa komai, duk abin da ya shige mata duhu takan same shi don ya ba ta shawarar da ta dace ko ya dora ta a kan hanya.   Hasali ma yadda Salma ta shaku da mahaifinta Alhaji Balarabe, ba ta shaku da mahaifiyarta Hajiya Maryam ba.

Salma ba ta taba bata wa mahaifinta rai a kan wani abu ba, saboda irin biyayyar da take yi masa.  Hasali ma Alhaji Balarabe yakan yi alfahari da irin biyayyar da ’yarsa Salma take yi masa, inda a kullum yake yi mata addu’a da kuma fatan alheri.

Mu kwana nan

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883


Sunday, 23 December 2018

DALILIN DA YASA NASAYI GASHIN ALI NUHU NAIRA DUBU DARI BIYAR

DALILIN DA YASA NASAYI GASHIN ALI NUHU NAIRA DUBU DARI BIYAR

Fitaccen furodusa a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Alhaji Mustapha Ahmad wanda aka fi sani da Alhaji Sheshe ya ce ya biya shahararren jarumi, Ali Nuhu Naira dubu 500 ne don ya aske gashin kansa saboda rawar da jarumin zai taka a fim dinsa mai suna ‘Kazamin Shiri’ tana bukatar jarumin sai ya aske gashin kansa don fim din ya samu karbuwa a wurin masu kallo.

 Furodusan ya ce babu jarumin da ya dace ya fito a fim din fiye da Ali Nuhu, kuma ana bukatar da sai ya yi aski, shi ya sa ya biya kudin don jarumin ya aske gashin kansa.

Duk wanda ya san Ali Nuhu ko yake kallon fina-finansa fiye da shekara 10 ya san shi da wani salon aski da ake kira ‘FKD’, duk irin fim din da zai fito jarumin ba ya yarda ya asken gashin kansa.

 
Idan ba a manta ba ko fim din Barde da ya fito wanda ake bukatar ya yi askin kwal-kwabo ma bai yi askin ba, face an kira wani mai yi wa ’yan fina-finan Kudancin kasar nan kwalliya da ake kira Akeem, inda ya yi dabarar da ta nuna kamar an yi wa Ali Nuhu aski kwal-kwabo.

Ya ce, “Saboda yanayin fim din Ali Nuhu talaka ne, kuma a yanayin rayuwarmu ba za ka taba ganin talaka da askin ’yan gayu ba, don haka labarin yana bukatar ganin abu a zahiri ne, sannan rol din shi ya kira shi ya sa na ga ya dace in sayi gashin kan nasa ya yi mini aski.”

“Kuma na ji dadi da ya amince da hakan, domin a wasu lokuta ya ki yarda ya yi askin don da wadansu sun nemi ba shi kudi.”

A yanzu dai tuni aka fara daukar fim din ‘Kazamin Shiri’ a Kano, inda za a shafe kwana 10 ana daukarsa.

Jaruman cikin shirin fim din sun hada da Ali Nuhu da Aminu Shariff (Momo) da Rabi’u Rikadawa da Fati Washa da Bilkisu Shema da Inteesar el-Fallata da Hajara Usman da sauransu.

Ibrahim Birniwa ne ya tsara labarin, Alhaji Sheshe ya shirya shi, inda Sunusi Oscar 442 ya ba da umarni.

Source Jaridar Aminiya

Saturday, 22 December 2018

Wednesday, 5 December 2018

Sarkin Kano M. Sanusi tare da Fashola

Sarkin Kano M. Sanusi tare da Fashola

Me martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II kenan tare da ministan wuta, ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola a lokacin da yakaimai ziyarar bangirma.