Showing posts with label Kannywood. Show all posts
Showing posts with label Kannywood. Show all posts

Wednesday, 12 June 2019

Zawarci babbar musifa ce Inji tsohuwar jarumar Hausa film Hafsat Shehu.

Zawarci babbar musifa ce Inji tsohuwar jarumar Hausa film Hafsat Shehu.

Zawarci babbar musifa ce Inji tsohuwar jarumar Hausa film Hafsat Shehu.
Tsohuwar jarumar Kannywood, Hafsat Shehu ta yi tsokaci akan halin da mata kan shiga idan aka ce suna zawarci.

Hafsat wacce ta kasance mata ga marigayi jarumin Kannywood Ahmed S Nuhu ta bayyana cewa zawarci bala’i da musifa ce domin a cewarta da zaran an kira mace da Bazawara toh shakka babu darajarta da kimarta na raguwa a idanun mutane.
Jarumar tace ya kai har idan aka ce mace bazawara ce sai ka ga kowa yana kaffa-kaffa da ita.
Ta kuma bayyana cewa zaman zawarci na da daci, kuna da kuma cin rai domin a cewarta akwai abubuwan bacin rai a tattare da shi.
Shafin Mikiya na Facebook ya ruwaito inda jarumar ke cewa: “Hakika zawarci bala’i ne, idan mace tana zawarci ta kan shiga halin Ni yasu, darajarta da kimarta raguwa suke, duk inda kace bazawara ce mace to sai kaga ana kaffa-kaffa da ita.
“Zaman zawarci yana da daci da kuna da kuma cin rai, akwai abubuwa da yawa na bacinn rai wanda bazan iya fada ba.”
Mijin jarumar na farko, Ahmed S Nuhu ya rasu ne yan shekarun baya da suka gabata a hanyarsa ta zuwa wajen diramar Sallah da masana'antar kan shirya. Tun bayan rasuwarsa jarumar bata kuma dawowa harkar fim ba.

Tuesday, 11 June 2019

Rigima Ta Barke Tsakanin Teema Makamashi DaTsohuwar Jarumar Kannywood Fati Muhd Akan Wani Wai Shi Dino Malaye.

Rigima Ta Barke Tsakanin Teema Makamashi DaTsohuwar Jarumar Kannywood Fati Muhd Akan Wani Wai Shi Dino Malaye.

Rigima Ta Barke Tsakanin Teema Makamashi DaTsohuwar Jarumar Kannywood Fati Muhd Akan Wani Wai Shi Dino Malaye.

Abinda ya hada da jaruma teema makamashi shine domin tayi masa waka itama fati muhd sai tayi mashi shikenan sai abin ya bata ma teema makamashi rai saboda meyasa tuntuni batayi masa sai da ita tayi sannan ba,a dade ba teema makamashi tayi mata wani martani a shafinta na instagram inda ta daura wani hotonta ita da shi Dino malaye a kasa sai ta saka inda kina tunanin soyayya dashi ne toh kima bari kuma wai idan saboda nayi masa waka ne kema kika yi masa to kin samu matsala saboda idan kika ce duk abinda nayi sai kinyi kina cikin wahala wallahi inji teema makamashi take fadama fati muhd amma haryanzu bata maida mata martani bah.

Tuesday, 4 June 2019

Saratu Gidado Na Nema Wa Tsohuwar Jaruma Bilkin R.K. Agajin Gaggawa.

Saratu Gidado Na Nema Wa Tsohuwar Jaruma Bilkin R.K. Agajin Gaggawa.

Saratu Gidado Na Nema Wa Tsohuwar Jaruma Bilkin R.K. Agajin Gaggawa.

Post by <> samaila umar lameedo

Ga abin da fitacciyar jaruma Hajiya Saratu Gidado (Daso) ta rubuta:
"Wannan baiwar Allah da mu ka yi hotuna da ita sunan ta BILKIN R.K.
Tsohuwar jarumar films din Hausa ce. Ta yi zamani da su Hindatu Bashir da marigayiya Biba. Ta bada gudunmawa sosai don ci-gaban films.
Ta na fama da ciwon sabara da ciwon kirji da "low blood". Ta rame sosai. Ba ta da mai taimako sai Allah. Ga ta marainiya kuma ba ta da d'a, ga shekaru sun hau mata.
Wanda Allah ya nufa ya na iya taimaka mata da kudin magani ko kayan abinci.
Ga lambar wayar ta nan 08036144627 mai so ya yi magana da ita.
Ko kuma ta bank details di na:
Saratu Gidado
Zenith Bank
1003795458
Ita ta ba ni izini in sanar wa jama'a ko za a dace.
Allah ya bada ikon taimakawa."👏
Sources:Fim magazine

Friday, 31 May 2019

Thursday, 23 May 2019

Friday, 17 May 2019

Adam A Zango Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Nake Auri saki .

Adam A Zango Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Nake Auri saki .

Adam A Zango Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Nake Auri saki .

Fitaccen jarumin nan na dandalin shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango wanda aka fi sani da Prince Zango ya bayyana dalilin da ya sa yake yawan auran mata kuma daga bisani ya rabu da su. Jarumin ya bayyana cewa ba wai baya iya zama da mace bane, sai dai
ba zan iya fada muku abin da ya hada shi da matata ta farko, da matata ta biyu da kuma matata ta uku ba.
Allah yana hada mata, mace da namiji. Allah ya halicci mata domin su kasance ni’ima a garemu maza. Don mu Allah ya halicce su.
Adam ya kuma bayyana cewa Allah ya rigada ya tsara ma mutum kaddararsa da abunda zai faru da shi tun kan a haifasa har izuwa ranar da zai amsa kiran mahallicinsa.
Dan wasan ya bayyana hakan ne a hira da yayi da shafin BBC Hausa inda yake cewa:
Allah Ubangiji ya rubuta wa mutum abin da zai faru da shi tun daga farkon haihuwarsa har zuwa ranar mutuwarsa.
Kuma wannan kaddarar da Allah yayi mun itace tawa, saboda ni , Allah yana gani, Allah ya ba ni komai da na roke shi, amma ban da mace wanda nake zaman aure da su.
“Sannan kuma ina so na gayawa mutane wani abu cewa, duk mutin da ya kasance zai yi aure ya rabu da mace, ya kara yi kuma ya kara rabuwa da ita, toh ya kamata su gane cewa wannan mutumin ba mazinaci ba ne. Saboda ni Adamu Zango Allah ya ba ni, duk duniya a cikin masana’antar Kannywood, babu wanda mata ke so iri na. Toh me zan yi da aure.
Rigima Ta barke tsakanin mawaki Naziru Ahmad da jarumar Fim Hadiza Aliyu Gabon.

Rigima Ta barke tsakanin mawaki Naziru Ahmad da jarumar Fim Hadiza Aliyu Gabon.

Rigima Ta barke tsakanin mawaki Naziru Ahmad da jarumar Fim Hadiza Aliyu Gabon.

Rigima Ta Barke Tsakanin Naziru Da Gabon.

Naziru Ahmad sarkin wakar sarkin Kano yayi wani shagube kan masu kyauta suna yadawa a kafafen sada zumunta na zamani inda yake cewa “Yin hakan bai kamata ba saboda cin fuska ne ga wanda kake bawa sadakar kuma kana yada shi.
Ba tare da jimawa ba ita ma jaruma Hadiza Aliyu Gabon ta maida martani inda take cewa Ya kamata ayi kyauta a bayyana domin wasu suyi koyi da taimakawa marasa karfi.


Kotu ta bada dama kwamishinan yan sanda da ya kamo hadiza Gabon.

Kotu ta bada dama kwamishinan yan sanda da ya kamo hadiza Gabon.

Kotu ta bada dama kwamishinan yan sanda da ya kamo hadiza Gabon.

A yaune Alhamis mai shari'a muntari dandago na kotun magistrate court 15 dake zamanta nomansland ya bawa komishinan yan sanda na jihar kano umarni ya kamo shahararriyar jarumar wasan Hausa hadiza Gabon sabida taki amsa kiran kotun.
Mustapha na buriska shine ya shigar da karar jarumar yana zarginta da cewa tanayi masa barazana da rayuwa ya yanke shawarar maka ta kai tsaye zuwa kotu saboda saboda yana tsoron idan ya kaiwa hukumar yan sanda bazata tuhme ta ba kasancewar yadda jarumar takeda mu'amala da wasu daga cikin jami'an yan sanda da kuma manyan yan siyasa dama masu kudi a fadin kasar nan.
Mai shari'ar ya bada umarnin hakan saboda bijirewa gayyatar da kotu ta 1 tayi mata kuma ya kara da cewa idan kwaminshinan yan sanda ya kamata ya tabbatar an binciketa akan lainfin da mai karar ya shigar kafin a damkata ga hannun kotun suma suyi nasu hukuncin.

Thursday, 16 May 2019

Sunday, 12 May 2019

Kalli Wasu Hotunan Rahama Sadau Wanda Suka Janyo Mata Cece Kuce.

Kalli Wasu Hotunan Rahama Sadau Wanda Suka Janyo Mata Cece Kuce.

Kalli Wasu Hotunan Rahama Sadau Wanda Suka Janyo Mata Cece Kuce.

Kamar Yanda Aka Saba, Yanzun Ma Jaruma Rahama Sadau Ta Sake Sakan Wasu Sabbin Zafafan Hotunanta Tare Da Wani Wanda Sunansa Ba Bai Bayyana Ba.. Sannan Wasu Hotunan Kuma Ta DauKa, Tare Da Kanninta .