Wednesday, 12 June 2019




Zawarci babbar musifa ce Inji tsohuwar jarumar Hausa film Hafsat Shehu.

Home Zawarci babbar musifa ce Inji tsohuwar jarumar Hausa film Hafsat Shehu.

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Zawarci babbar musifa ce Inji tsohuwar jarumar Hausa film Hafsat Shehu.
Tsohuwar jarumar Kannywood, Hafsat Shehu ta yi tsokaci akan halin da mata kan shiga idan aka ce suna zawarci.

Hafsat wacce ta kasance mata ga marigayi jarumin Kannywood Ahmed S Nuhu ta bayyana cewa zawarci bala’i da musifa ce domin a cewarta da zaran an kira mace da Bazawara toh shakka babu darajarta da kimarta na raguwa a idanun mutane.
Jarumar tace ya kai har idan aka ce mace bazawara ce sai ka ga kowa yana kaffa-kaffa da ita.
Ta kuma bayyana cewa zaman zawarci na da daci, kuna da kuma cin rai domin a cewarta akwai abubuwan bacin rai a tattare da shi.
Shafin Mikiya na Facebook ya ruwaito inda jarumar ke cewa: “Hakika zawarci bala’i ne, idan mace tana zawarci ta kan shiga halin Ni yasu, darajarta da kimarta raguwa suke, duk inda kace bazawara ce mace to sai kaga ana kaffa-kaffa da ita.
“Zaman zawarci yana da daci da kuna da kuma cin rai, akwai abubuwa da yawa na bacinn rai wanda bazan iya fada ba.”
Mijin jarumar na farko, Ahmed S Nuhu ya rasu ne yan shekarun baya da suka gabata a hanyarsa ta zuwa wajen diramar Sallah da masana'antar kan shirya. Tun bayan rasuwarsa jarumar bata kuma dawowa harkar fim ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: