Showing posts with label labarin wasanni. Show all posts
Showing posts with label labarin wasanni. Show all posts

Tuesday, 6 July 2021

SADIO MANE YAYI BAYANI MAI MATUQAR JAN HANKALI..

SADIO MANE YAYI BAYANI MAI MATUQAR JAN HANKALI..

Sadio mane dan wasan kungiyar kwallon kafa ta liverpool dake england kuma haifaffen kasar SANEGAL,,,Cikin bayanin da yafitar shahararren Dan wasan gaba a qungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar England, 
Dan wasan yayi bayanin cewar baya daga cikin tsarinsa na siyan motoci masu tsada ko manyan wayoyin hannu, a'a shidai burin Dan wasan shine ganin cewar yan uwasan dake kasarsa sunkwanta adakunansu cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin bayan sunci abinci.
 Haka zalika basu da shayin zuwa asibitoci Dan Neman magani. Bugu da qari Dan wasan yace yanason ganin fanni. Koyo da koyarwa akasarsa yana tafiya Dede da zamani ma'ana ansami kyakkyawan tsarin koyarwa hadi da kayan koyo nazamani.

  Dan wasan baitsaya nanba yace yadda sauran yan uwansa yan wasa suke kashe kudadensu wajen sayen many an motoci na alfarma gami da Mayan more rayuwa baiga laifinsuba dalili kusa kudinsu ne. Kuma kowa yana da hangar da yaga yafi dacewa yakashe kudinsa, kuma sun cancanta suyi hakan domin kuwa guminsune. Ma ana halal dinsune. Tokuwa shima yana da hanyar kashe nasa kudaden. Hakannema yaga yadace da yaringa taimakawa yan uwansa marassashi. Ta hanyoyi daban daban..

Wednesday, 26 December 2018

Karanta Kaji: Ko Ka San ’Yan Wasan Da Babu Kamarsu A Gasar Firimiyar Ingila?

Karanta Kaji: Ko Ka San ’Yan Wasan Da Babu Kamarsu A Gasar Firimiyar Ingila?

Hukumar dake kula da buga gasar cin kofin ajin firimiya ta kasar Ingila ta fitar da sunayen zakakuran ‘yan wasa guda 10 a gasar ta firimiya da babu kamarsu a gasar da ake fafatawa a wannan kakar.



Ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasanne duba da auna irin kokari da gudun mawa da kowanne ya yi wa kungiyar sa kawo yanzu da akayi rabi a gasar bayan kowacce kungiya ta buga wasanni 18. Saidai kungiyoyin kwallon kafa guda 2 sune sukafi mamaya wato kungiyar Liverpool da takwarrata ta Manchester City don ko wacce kungiya akwai ‘yan wasan ta guda 3 acikin guda 10 da aka fitar.

Ga jerin sunayen ‘yan wasan daga mai jan ragamar na 1 kenan har zuwa na 10:

Mohammed Salah (Liverpool). Eden Hazard (Chelsea). Raheem Starling (Manchester City). Harry Kane (Tottenham). Virgil Van Dink (Liverpool). Ederson (Manchester City). Sergio Aguero (Manchester City). James Milner (Liverpool). Pieree-Emerick Aubameyang (Arsenal). Wilfried Zaha (Crystal Palace).

Har ila yau, idan an kammala buga gasar, hukumar ta FA zata sake fitar da sunayen ‘yan wasanda babu kamarsu a gaba daya gasar da aka buga kuma yawanci kungiyar data lashe gasar ‘yan wasanta suna fin yawa.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: LEADERSHIP A YAU

Sunday, 18 November 2018

Ahmed Musa Yayi Murna Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasa Nigeria

Ahmed Musa Yayi Murna Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasa Nigeria

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya ce ya yi matukar murnar lashe gasar gwarzon dan wasan kwallon kafar Najeriya na 2018.


A sakon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Asabar, dan wasan na kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudiyya, ya ce lashe wannan gasa "ya sa na kaskantar da kaina."

"Godiya ga abokan wasana wadanda suka sanya nake inganta wasana da kuma godiya ga dukkan mutanen da suka taimaka min," in ji dan wasan.




Ahmed Musa ya doke dan wasan baya na Super Eagles Kenneth Omeruo da 'yar wasan Super Falcons Rasheedat Ajibade wadanda suka shiga gasar.

An sanya sunan kwallon da Ahmed Musa ya zura a wasan Najeriya da Iceland na gasar cin kofin duniya na 2018 a matsayin kwallon da ta fi kayatarwa.

Dan wasan shi ne dan Najeriya na farko da ya zura kwallo fiye da sau daya a gasar cin kofin duniya ta FIFA.
BBChausa.

Wednesday, 14 November 2018

Fellainai ya aske sumarshi saboda shirin zagayowar ranar haihuwarshi

Fellainai ya aske sumarshi saboda shirin zagayowar ranar haihuwarshi


Tauraron dan kwallon Manchester United, Maroaune Fellaini da ya saba barin suma buzubuzu ya aske ta a shirin yin murnar zagayowar ranar haihuwarshi da yake yi.

A gobene Fellaini zai cika shekaru 31 kuma ya saka wannan hoton nashi na kasa inda ya bayyan cewa yayi aski dan zagayowar ranar haihuwar tashi.

Saturday, 20 October 2018

Ronaldo zai bar Juventus zuwa wata kungiya

Ronaldo zai bar Juventus zuwa wata kungiya

Ronaldo zai bar Juventus zuwa wata kungiya


Kwanannan ne Ronaldo ya bar Real Madrid zuwa Juventus inda ya fara taka leda yanda ya kamata, duk da dai yanzu anata badakalar fyade da wata 'yar kasar Amurka tace ya mata, an ruwaito Ronaldo na da shirin barin Juve din.

Shafinnan na kasar Sifaniya daya saba kwarmato labaran sayar da 'yan wasa kuma mafi yawanci sukan zama gaskiya watau Don Balon ya kwarmato cewa tauraron dan kwallon Ronaldo zai sake tsayawa kakar wasa daya a Juventus.

Amma daga nan zai koma kungiyar kasar Amurka ta MLS Orlando da wasa inda zasu biyashi albashin miliyan 50 duk kakar wasa na tsawon shekaru 2 idan dai hakan ta tabbata to Ronaldon zai zama dan wasan da yafi kowane dan wasa karbar Albashi a Duniya.

Shafin ya kuma ruwaiyo cewa Ronaldon na da burin sayen hannin jari a kungiyar ta MLS bayan yayi ritaya.
Barcelona ta musanta rahotannin shirin maido da Neymar

Barcelona ta musanta rahotannin shirin maido da Neymar

Barcelona ta musanta rahotannin shirin maido da Neymar


Mataimakin shugaban Barcelona Jordi Cardoner, ya ce kungiyar bata da wani shiri ko niyyar sake maido da dan wasanta Neymar da ya sauya sheka zuwa PSG a watan Yuli na shekarar 2017.

Cardoner yana mayar da martani ne kan rahoton da wasu kafafen yada labaran Spain suka rawaito dake nuna cewa, Barcelona ta soma shirin ganin da sake maido da Neymar da ta saidawa kungiyar PSG kan farashi mafi tsada a duniyar kwallon kafa na euro miliyan 222.

A cewar mataimakin shugaban na Barcelona, babu koda jami’I daya daga cikin shugabannin kungiyar da ya taba gabatar da tayi maido da tsohon dan was an nasu, ko kuma tattauna kan batun.
Bayan shafe shekaru hudu tare da Barcelona, Neymar ya taka rawa a nasarorin da kungiyar ta samu wajen lashe kofin gasar La Liga 2 da kofin zakarun nahiyar Turai a 2015.
RFIhausa.

Tuesday, 25 September 2018

Karanta Kaji Yadda akai ya zama Gwarzon duniya: Modric ya kawo karshen Ronaldo da Messi

Karanta Kaji Yadda akai ya zama Gwarzon duniya: Modric ya kawo karshen Ronaldo da Messi

Dan wasan Real Madrid Luca Modrci ya lashe kyautar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya da take bai wa gwarzon dan kwallon duniya na shekara a wani biki da ya gudana a birnin London, abin da ya kawo karshen kane-kanen da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka yi wajen lashe kyautar a tsakaninsu cikin tsawon shekaru.


Modric ya doke Ronaldo na Juventus da Mohamed Salah na Liverpool wajen lashe wannan gagarumar kyautar a bana.

Dan wasan mai shekaru 33 ya lashe kofin zakarun nahiyar Turai karo na uku a jere a kungiyarsa ta Real Madrid, sannan ya jagoranci kasarsa ta Croatia har zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Rasha.

Ronaldo bai samu damar halartar bikin karramawar ba, yayin da har ila yau Mohamed Salah ya doke shi wajen lashe kyautar Puskas da ake bai wa dan wasan da ya jefa kwallo mafi kyawun ciyuwa a raga.

Ko da dai wasu na ci gaba da jinjina wa Ronaldo kan kwallon da ya jefa ragar Juventus a bara a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, wadda ta kai ga magoya bayan Juventus a Turin mikewa tsaye don girmama shi.

Wani abu da ke ci gaba da dagula tunanin magoya bayan Salah shi ne yadda aka cire sunansa daga cikin jerin ‘yan wasan FIFA 11 da suka fi iya taka leda duk da cewa yana cikin ‘ya wasa 3 ta suka yi takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan bana.

JERIN 'YAN WASAN FIFA 11 NA BANA

David de Gea ( Manchester United )

Dani Alves (Paris Saint-Germain)

Raphael Varane ( Real Madrid )

Sergio Ramos (Real Madrid)

Marcelo (Real Madrid)

Luka Modric (Real Madrid)

N'Golo Kante ( Chelsea )

Eden Hazard (Chelsea)

Lionel Messi ( Barcelona )

Kylian Mbappe (Paris Saint-Germain)

Cristiano Ronaldo ( Juventus )

A bangaren guda an zabi Kocin tawagar Faransa, Didier Deschamp a matsayin gwarzon mai horarwa na shekara, yayin da 'yar wasan Brazil da ke taka leda a Orlando Pride, watO Marta ta lashe kyautar ta FIFA a bangaren mata.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: RFI HAUSA