Showing posts with label FATAWA. Show all posts
Showing posts with label FATAWA. Show all posts

Saturday, 9 June 2018

KARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PANTAMI DA TA SA YAYI KUKA YA ZUBAR DA HAWAYE

KARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PANTAMI DA TA SA YAYI KUKA YA ZUBAR DA HAWAYE

KARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PANTAMI DA TA SA YAYI KUKA YA ZUBAR DA HAWAYE

A tafsirin Al-Qur'ani Maigirma wanda Babban Malaminmu Ash-sheikh Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami yake gabatarwa a darasin jiya Talata 20 ga watan Ramadan, wani bawan Allah ya rubuto takarda yake rokon Malam akan ya yiwa 'dan uwansa nasiha sakamakon bijirewa mahaifiyarsa da yayi har yace babu shi babu ita, kuma sunyi iya kokarin da zasuyi domin yaje ya baiwa mahaifiyarsa hakuri amma yaki
Da malam ya tashi gabatar masa da nasiha sai ya fara da cewa ashe har ana iya yin fada da iyaye a kaurace musu?

Babbar magana!, bil hakki ni dai tun da muka shiga Ramadan ban taba jin wata fitina da ta kai wannan girma ba ace mutum da iyayensa yayi fada har an rokeshi don ya basu hakuri amma yaki
Daga nan Malam ya kawo bayanan ayoyin Qur'ani da Hadisai na Annabi (saw) wanda suke nuni da falalar yiwa iyaye biyayya musamman mahaifiya, sannan ya kawo wata kissa wacce daga karshe sai da Malam ya fashe da kuka
Kissar itace kamar haka:

A zamanin sahabbai wani mutum ne yana neman budurwa sai ya kasheta saboda taki aurensa, sai yazo wajen Ibnu Abbas (ra) sai yace masa nayi zunubi maigirma, ban san me zanyi Allah ya gafarta min ba, ban san me zanyi ba a rayuwata na shiga damuwa
Sai Ibnu Abbas ya tambayeshi mai ya faru gareka? Sai yace wallahi budurwa nake nema taki aure na sai na kashe ta, Ibnu Abbas yace Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un haka ka aikata? yace eh!, yanzu don Allah yaya za'ayi Allah Ya yafe min?
Tambayar farko da Ibnu Abbas ya masa shine shin mahaifiyarka tana raye? sai mutumin yace masa a'a bata raye, sai Ibnu Abbas yayi shiru, bayan tsawon lokaci sai yace to kaje kayi ta tuba kayi ayyukan alheri.

Sai daliban Ibnu Abbas sukace masa me yasa ka tambayeshi ko mahaifiyarsa na raye kuma da yace bata raye sai kayi shiru?
Sai Ibnu Abbas yace Wallahi ban san wani aiki na nagarta da mutum zaiyi ya nemi gafarar Allah Ya yafe masa ba kamar BIYAYYA ZUWA GA MAHAIFIYA, yace ban san wani aikin dake kaffara na zunnubai a duniya ba kamar biyayyan da mutum yake yiwa Mahaifiyarsa.." daga nan wajen ne sai Malam Isah Ali Pantami ya fashe da kuka har ma ya kasa cigaba da bayanin kawai sai ya umarci Alarammansa Malam Abdullahi Abba Zaria ya karanto ayoyin Qur'ani.

Ni kuma nace Malam Ya tuna da tashi mahaifiyar wacce Allah Yayiwa rasuwa watannin baya shi yasa yake kuka, ga wani kuma tashi mahaifiyar tana raye amma yayi fushi da ita (Allah Ya sauwake)
Wanda yake da bukatar karatun ya nemi tafsirin Qur'ani na ranar 20 ga watan Ramadan wanda ya gabata jiya talata
Gaskiya duk wanda Mahaifiyarshi take raye ashe yana da wata babban alfarma wanda zai iya gyara lahirarsa da ita.

Mu kyautatawa iyayenmu da suke raye domin mu gama da duniya lafiya mu kuma hadu da Allah lafiya
Allah Ka shiryar damu ka bamu ikon kyautatawa iyayenmu, wadanda suka rasa nasu iyayen Allah Ka jikansu Ka basu Aljannah don RahamarKa Amin
Sarauniya.

Monday, 21 May 2018

Mazan Aure: Abubuwa Da Ke Rage Karfin Namiji

Mazan Aure: Abubuwa Da Ke Rage Karfin Namiji

Mazan Aure: Abubuwa Da Ke Rage Karfin Namiji

Binciken masana sun bayyana cewa wasu abubuwa da dama da kan rage karfin namiji daga cikin su akwai na’ukan abinci wadanda ke raunana karfin namiji wanda kuma ya zama wajibi duk wani magidanci ya rika Kiyaye wa don samun natsuwa da kima a idon iyali.

Shin ka taba samu kanka cikin wani yanayi na rashin jin sha’awar jima’i ko kuma kasa tabuka wani abu bayan samun biyan bukata, duk wannan zai iya kasancewa daga abincin da ka ci ne.

(1) Duk wani nau’in abinci wanda ke sa kiba, to yana raunana karfin gaban namiji misali nau’ukan abincin da ake soyawa da man gyada.

(2) Nau’ukan lemun kwalba da wadanda ake jikawa a ruwa da suka kunshi sikari ( Sugar) kamar su ‘ Soda’ da ice cream da sauransu duk suna tasiri wajen rage karfin namiji yayin jima’i.

(3) Duk wani nau’in abinci wanda aka sarrafa shi daga ainihin yadda yake a da kamar shinkafa da Alkama. Binciken masanan ya nuna cewa ya kamata magidanta su mayar da hankali wajen cin kayan marmari da na lambu.

Sunday, 8 April 2018

KOYAR DA KIMIYAR AURE Abubuwan Da ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE Zata Koyar  Guda (41) - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

KOYAR DA KIMIYAR AURE Abubuwan Da ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE Zata Koyar Guda (41) - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa



Wannan makaranta ta ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE ta shirya tsaf domin koyar da kimiyar zamantakewar aure, ga bangarori guda uku na maza mata
Zawarawa maza da mata 
Samari da Yammata
Mazan aure da matan su. 
Domin kara inganta rayuwa ta maaurata wadannan kwasa kwashe sun hada
1- Manufar yin aure
2 Hikimar yin aure
3 Falalar yin Aure
4-Hukuncin yin aure
5 - Yadda ake neman aure
6 - Irin matar da ake so a aura
7- Irin mijin da ake so a aura
8- Yadda ake zuwa zance da yadda ake yi
9_ Yadda ake bincike kafin aure da abubuwan ake bincikawa guda biyar
10- Mata guda 42 da suka haramta mutum ya aure su saboda nasaba ko shan nono ko surukuta.
11 Rukunan Daurin aure.
12 - Sadaki da hukunce hukuncin sa
13 Wanene Waliyyi da sharuddan zama Waliyyi da kashe kashen waliyyai na aure
14 Sigar daurin aure da yadda ake yin ta.
15 - Shedun aure da siffofinsu.
16- Sanya sharudda a cikin aure.
17 - Yadda ake bukukuwan aure a musulunci, da aladun da suka shigo cikin aure marasa kyau. 
18- Yadda ake walima da shagalin aure.
19- Ladubban tarewar amarya da Ango.
20 Hakkokin mata akan miji
21 Hakkokin miji akan mata.
22 Ladubban kwanciyar aure
23 Abubuwan da suke kara soyayya tsakanin maaurata.
24 Yadda ake gyara matsalolin aure idan sun taso.kafin akai ga saki 
25 Abubuwan da suke kawo albarka a gidan aure
26 Abubuwan da suka halatta, da wadanda suka haramta tsakanin maaurata a lokacin da mace take al'ada
27 Abubuwan da suke kawo mutuwar aure
28 Hukuncin hana daukar ciki, ko zubar da ciki, da Tsarin iyali a musulunci.
29 Sharuddan da mutum, zai cika kafin ya kara aure.
30 Wanda ya kasa daukan nauyin iyalinsa. 
31 Hukuncin wanda ya kauracewa iyalinsa. bisa zalunci ko larura ko horo. da sanin lokacin da shari'a ta iyakan ce. 

32 Mutuwar aure, da hukunce hukuncan sa,
33 Hakkokin matar da aka saka, 
34 Wa yake da hakkin rike yaya bayan mutuwar aure? 
35 - Yadda ake kul'i (mace ta nemi rabuwa) da abubuwan da suke jawo shi. 
36- Hukuncin komai bayan saki. 
37- Idda da hukuncin ta a musulunci 
38 - Hukuncin Ila'i Rashin kusantar iyali da rantsuwa ko saka sharadi. 
39-  Hukuncin Zihari kamanta jikin mahaifiyar sa da matarsa. Ko sauran mahramansa. 
40 Hukuncin lia'ni idan mutum yana zargin matarsa da zina. 
Reno da tarbiyya tun daga daukar ciki har zuwa haihuwa da yaye, 
Hakkokin yaya akan iyaye da hakkokin iyaye akan yaya. 
41 Yadda ake Takaba idan. Miji ya mutu.
Illolin Hassada Da Maganinta - Dr Jabir Sani Maihula

Illolin Hassada Da Maganinta - Dr Jabir Sani Maihula


1) Hassada shine mutum yaji zafin wata ni'ima da Allah yayiwa wani bawan sa, koda baiyi fatar gushewar ni'imar ba. [Ibn Taymiyya da wasu malamai]
2) Hassada halin yahudawa ce [ Qur'an 2: 109, 4:54, 48:15]
3) Hassada tana kama wanda akayiwa ita, komai imanin sa; ta kama Annabi Yusuf (A.S), kuma Allah ya umurci Annabi (S.A.W) daya nemi tasri daga sharrin mai hassada [Qur'an 113:5].

4) Karanta azkar na safe da yamma, da karanta Fatiha, da karshen suratul Bakara, da ayatul Kursiy da suratul Falaq da Nas ya na kariya da ga hassada da bala'oi [hadissai da yawa]
5) Boye ni'ima ga wadan da ka ke tsammanin zasuyi ma hassada yana kareka daga hasada ya yardar Allah [quran 12:5].

6) Annabi (S.A.W.) yahana hasada, cikin hadissai dayawa cikin su akwai [ Muslim 2559]
7) Mai hassada yana fada ne da Allah, domin Allah shi yake yin ni'ima ga wanda yaga dama, kuma Allah shiyafi sanin wanda ya cancanta. [Malamai]
8) Mai hassada kullum yana cikin bakin ciki da bacin rai wanda ba lada akai [ laa tahzan, A'ed alQarny].

9) Hadisin da ya shahara na "Hasada tana cin ayyukkan..." bai inganta ba.
10) Allah yayi mana tsari daga hassada, yasa kada muyiwa wani, kuma ya tsare mu daga masu yi mana.

Monday, 12 March 2018

Yawun Bakin Budurwa  Yana Kara Karfin Hadda Al-kur'ani inji Sheikh Ahmad  Tijjani Yusuf Guruntum

Yawun Bakin Budurwa Yana Kara Karfin Hadda Al-kur'ani inji Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

 Sumbantar mace a baki yana da fa’ida matuka inji wani Shehin Malami

 Sheikh Guruntum yace miyau na Budurwa yana dada kaifin kwakwalwa

⏩Mai bukatar haddar sa ta zauna da kyau ya yawaita sumbantar iyalin sa

Wani Malamin addinin Musulunci ya bayyana cewa miyaun bakin mace yana da matukar amfani musamman ga masu kokarin hadda.



Sheikh Ahmad Tijjanu Yusuf Guruntum wanda babban Shehin Malamin addinin Musuluni ne a Garin Bauchi a wani karatu da yayi ya bayyana cewa miyaun mace yana da amfani kwarai domin yana kara kaifin harda sosai.


A addinin Musulunci ma dai sumbantar iyali abu ne mai kyau inda wannan malamin ya bayyana wani babban fa’idar da ‘daliban ilmi ba su san shi ba. Malamin ya kafa hujja da wani hadisin Annabi a littafin Sahihul Bukhari.

Dama dai masana a kimiyya tuni sun ce sumbanta a baki yana taimakawa wajen maganin ciwon kai da rage ciwon hawan jini, haka kuma ana so mata masu al’ada su rika yawan sumbanta domin rage radadin al’adar.