⏩ Sumbantar mace a baki yana da fa’ida matuka inji wani Shehin Malami
⏩ Sheikh Guruntum yace miyau na Budurwa yana dada kaifin kwakwalwa
⏩Mai bukatar haddar sa ta zauna da kyau ya yawaita sumbantar iyalin sa
Wani Malamin addinin Musulunci ya bayyana cewa miyaun bakin mace yana da matukar amfani musamman ga masu kokarin hadda.
Sheikh Ahmad Tijjanu Yusuf Guruntum wanda babban Shehin Malamin addinin Musuluni ne a Garin Bauchi a wani karatu da yayi ya bayyana cewa miyaun mace yana da amfani kwarai domin yana kara kaifin harda sosai.
A addinin Musulunci ma dai sumbantar iyali abu ne mai kyau inda wannan malamin ya bayyana wani babban fa’idar da ‘daliban ilmi ba su san shi ba. Malamin ya kafa hujja da wani hadisin Annabi a littafin Sahihul Bukhari.
Dama dai masana a kimiyya tuni sun ce sumbanta a baki yana taimakawa wajen maganin ciwon kai da rage ciwon hawan jini, haka kuma ana so mata masu al’ada su rika yawan sumbanta domin rage radadin al’adar.
Monday, 12 March 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
KOYAR DA KIMIYAR AURE Abubuwan Da ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE Zata Koyar Guda (41) - Sheikh Aminu Ibrahim DaurawaWannan makaranta ta ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE ta shi
Illolin Hassada Da Maganinta - Dr Jabir Sani Maihula1) Hassada shine mutum yaji zafin wata ni'ima da
KARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PANTAMI DA TA SA YAYI KUKA YA ZUBAR DA HAWAYEKARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PAN
Mazan Aure: Abubuwa Da Ke Rage Karfin NamijiMazan Aure: Abubuwa Da Ke Rage Karfin NamijiBinci
0 Comments:
Post a Comment