Tare Da: Saddika Habib Abba 09097438402 habibsaddika@gmail.com
Daga Saddika Habib Abba
Suna: Sabuwar Rayuwa
Tsara labari: Malam Yusha’u
Furodusa: Ali Risuni
Bada umarni: MJ Big Man
Kamfani: Dukawa Film’s Producition
Jarumai: Abdul M Sharif, Asma’u Muh’d, Umar Y Malunfashi, Isa Bello Ja, Bashir Nayaya, Baballe Hayatu, Teema Makamashi, Saratu Gidado, Ahmad Tagge, da Muh’d Baba Hasin.
Sharhi: Saddika Habib Abba
A farkon fim din an nuna su Alh.Wada (Bashir Na Yaya) tare da Alh. Musa Mai Karo( Umar Malunfashi) da sauran mukarrabansu suna cikin wani kamfani wanda su costomet’s ne suna kawo wa kamfanin chemical suna saye saboda shi kamfanin suna sarrafa atamfofi da shaddodi ne. a lokacin wani mutumi ya fito ya fara karanto musu wata takarda tana kunshe da bayanin chemical din da Alh. Musa ya kawo musu shi kamfaninsu yake so kuma shi zai saya domin sun fi ganin kyansa da aukinsa saboda ya fi na Alh.Wada kyau saboda haka shi Alh.Wada sai dai ya yi hakuri don baza su sayi na sa ba, a gurin Alh. Wada ya mike yana fada yana nuna bacin ransa a fili da kuma nuna adawa ga Alh.Musa Mai Karo har Alh. Wada ya yi kikirarin sai ya ga bayan Alh. Musa suka watse suka bar wajen ran Alh.musa ya baci sosai sakamakon abinda ya faru.
Bayan Alh. Musa ya koma gida sai ya fara tunani yana ji ajikinsa wani abin zai faru sai ya dauki wata laya ya sakawa dansa guda daya da ya mallaka karami mai suna Mubarak a wuyansa sai matarsa ta tambayeshi menene hikimar hakan ya fadamata cewar wannan layar duk sirrikansa daya mallaka ne aciki yasan zai yi wa Mubarak amfani a gaba. bayan an yi haka a daren ranar sai Alh. Wada yazo da ‘yan iska suka kashe Alh. Musa tare da matarsa dansu Mubarak ya sha da kyar domin shi ficewa ya yi daga gidan yana ta tafiya har isa wani Kauyen Fulani Baffa ya tsinceshi (Isa Bello Ja) duk a galabaice ya kai shi gidansa gurin matarsa sakamakon basu taba haihuwa ba suka rikeshi tsakani da Allah har ya girma a gabansu, har ta kai wataran shima Mubarak yana cikin gona yana kiwo ya jiyo sautin karar mota an yi hatsari ya fita da gudu ya ceto ran wadda ta yi hatsarin mai suna Karima ya kawo ta rigarsu yana kulawa da ita har ta sami sauki har ya fara bata tarihin rayuwarsa cewar shima tsintacceni garin ba garinsu ba ne.
Karima ta kwadaitu akan ya bita birni domin nemo danginsa, marikin Mubarak Baffa ya amince Karima da Mubarak suka taho birni suka sauka a gidansu Karimar gaba ki dayansu a lokacin suka tarar mahaifin Karima yana jinyar shanyewar barin jiki ko magana ba ya yi, Mubarak yana ganinsa sai ya ga ashe Alh.Wada ne domin lokacin da ya cakawa mahaifinsa wuka bazai taba mantawa ba tun daga lokacin Mubarak ya fara kulla kullar yanda zai ga bayan Alh.Wada ya boye sirrin acikin zuciyarsa ba tare da ya bayyanawa kowa ba har sai lokacin da ya farka layar wuyansa ya ga ashe flash ne na computer Karima ta daukeshi suka je kafe domin suga me flash din yake dauke da shi suna zuwa suka sami Kabiru (Baballe Hayatu) suka yi gam da katar ashe ma shine sakataran Alh.Musa kafin ya rasu kuma babban amintaccensa ne hasali ma duk abinda yake cikin flash shine ya saka shi domin flash din yana dauke da duk takardun dukiyarda Alh. Musa ya mallaka Mubarak ya ji dadi sosai daga baya suka sake haduwa suka fara kulla ta yanda za’ayi su fito da dukiyar da Alh.Wada ya mamaye ta mahaifin Mubarak suka hada baki da wani lauya(Alasan kwalli) ya je gurin iyalin Alh.Wada ya shaida musu cewar duk dukiyarda Alh.Wada ya mallaka ba shin banki ne saboda haka za’a biya su Alh.Wada yana ji yana gani amma ba shida ikon magana sakamakon lalurar da ya ke ciki haka suka kwashe kaf dukiyarda ya mallaka hatta gidan da suke ciki duk aka tattara aka mikawa Mubarak hakkinsa Mubarak ya hada da dukiyarda mahaifinsa ya bar masa ya zama babban attajiri har ya sayi gidan da su Alh.Wada suke ciki saboda ya kara kuntatawa Alh.Wada kuma ya auri ‘yarsa Karima suka zauna tare acikin gidan a karshe har bakin ciki ya hallaka Alh.Wada shi kuwa Mubarak da Karima suka bude sabuwar rayuwa domin dama itama Karima tare da mahaifiyarta (Saratu Gidado) haushin abinda Alh.Wada yake yi suke ji saboda suma ba dadinsa suke ji ba.
A karshe Karima da Mubarak suka koma kauyen dan tsinke domin su saka halaccin da Baffa da matarsa suka yi musu sannan su ba su labarin duk abubuwan da suka faru sannan su daukesu su kawo su birni suma suji dadin rayuwarsu su dandali arziki.
Abubuwan Birgewa:
1- fim din ya sami kayan aiki masu kyau musamman camera ta daukar hoto.
2- Jaruman sun yi kokari gurin isar da sakon sannan kowannensu ya dace a gurbin da aka saka shi.
3- Labarin fim din ya tafi ya dire bai karye ba.
Kurakurai:
1-Mubarak karamin yaro ne mai kallo ya ga gidansu acikin birni yake kuma sai aka ga an tsince shi a wannan kauyen shin da kafa yazo ko kuma wani ne ya kawo shi? sannan menene silar ciwukan jikinsa duk ba’a bayyanawa mai kallo wannan ba.
2- An sami matsalar daukewar sauti a wasu hotuna na fim din.
3- Tun Mubarak yana yaro Kabiru yake a yanda ya ke kuma har ya girma tsahon shekaru ko dan yaya Kabiru bai canja ba shin shi Kabiru ba ya tsufa ne?
4- Acikin babban gari irin Kano yanda aka nuna a labarin ace har an kashe babban mutum irin Alh.Musa Mai Karo amma babu wani bincike da hukuma ta yi a haka abun ya tafi.
5- shin shi Alh.Musa ba shida kowa ne? sannan itama Matarsa bata da kowa ne har ayi musu irin wannan kisan ace babu wanda yazo sannan babu wanda ya nemi Mubarak ko bayan ya dawo shi kadai yake rayuwarsa?
6-Gurin da aka nuno Mubarak da Karima suna waka kwata-kwata bai kamata a nuno wani sashe na birni ba tunda ba’a birni suke ba.
7- Bai kamata ace daga zuwan Karima ba baffa yana tare da Mubarak tsahon shekaru amma lokaci daya ya amince Mubarak ya bita birni tunda baisan ko ita wacece ba idan so ya ke Mubarak ya bita yakamata ace ya bisu tunda rikon tsakani da Allah yake yi wa Mubarak.
8- Mai kallo ya ga Mubarak tsahon shekarunsa a kauye sutturar fulani yake sakawa tunda ba’a birni ya ke ba amma lokacin da Karima ta zo suna sallama zasu ta fi Birni sai aka ga Mubarak ya tsuke da kananan kaya itama Karima ta saka nata shin a ina suka sami wannan sutturar tunda ita Karima ma hatsari ta yi ba ta zo da komai ba.
Karkarewa:
Fim din ya yi kyau kuma ya yi ma’ana amma akwai abubuwan da ya kamata a budasu kuma a in gantasu ta yanda mai kallo zai gamsu sosai.
0 Comments:
Post a Comment