Showing posts with label Hausa News. Show all posts
Showing posts with label Hausa News. Show all posts

Monday, 24 December 2018

Thursday, 13 December 2018

Babu dan takarar da zai iya kayar da Buhari>>Honorabul Kazaure

Babu dan takarar da zai iya kayar da Buhari>>Honorabul Kazaure


Dan majalisar tarayya, Honorabul Muhammad Kazaure ya bayyana cewa babu dan takarar da zai iya kayar da shugaban kasa, Muhammafu Buhari a zaben 2019.


Kazaure ya bayyana hakane a ganawar da shugaba Buhari yayi da kungiyar magoya bayanshi inda yace, a kaf cikin 'yan takarar shugaban kasar da ake dasu babu wanda zai iya kayar da shugaba Buhari.
Yan Najeriya na kashe naira tiriliyan 1 kowace shekara wajen tafiya karatu kasashen waje>>Tsohon Shugaban Jami’a

Yan Najeriya na kashe naira tiriliyan 1 kowace shekara wajen tafiya karatu kasashen waje>>Tsohon Shugaban Jami’a


Shugaban Jami’ar Crawford, kuma tsohon Shugaban Jami’ar Lagos, Farfesa Oye Ibidapo-Obe, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na kashe akalla naira tiriliyan 1 duk shekara wajen tafiya karatun digiri kasashen waje.


Farfesan ya fadi haka ne jiya Laraba, a lokacin da ya ke jawabi a bikin yaye dalibai karo na 10 na Jami’ar Crawford da ke garin Igbesa, jihar Ogun.

Ya fallasa yadda ake kashe wadannan makudan kudade ne, daidai lokacin da majalam jami’o’in Najeriya ke ci gaba da gudanar da yajin aikin da suka fara tun daga ranar 4 Ga Nuwamba.

Daga nan ya ci gaba da nuna muhimmancin ci gaba da kafa jami’ao’i masu zaman kan su wadanda ba na gwamnati ba Najeriya.

Ya ce ta haka ne za su kara samun ingancin da za a rage karakainar neman karin ilmi a kasashen duniya, inda ake kwasar makudan kudade ana tafiya da sunan tafiya karin ilmi.

Premiumtimeshausa.

Wednesday, 12 December 2018

YAWAN SHEKARUN KO AURI-SAKIN?

YAWAN SHEKARUN KO AURI-SAKIN?


Labarin Magidanci a garin Lapai da ke jihar Neja, Yakubu Chanji, ya auri budurwa 'yar shekara 15. Ya zama babban labarin da ya janyo muhawara gami da cece-kuce. 


A ra'ayin wasu na ganin morewar budurwa ta auri saurayi da karfinsu ya zo daya zai nuna mata soyayya da wasanni. Amma Dan shekara 70 ya auri 'yar 15 tazarar shekaru 55 sun yi matukar yawa. A lokacin da mace ta kai 30 ne ta ke kan ganiyar bukatar kusancin da Namiji. Hakan na nufin a yayin da ta kara shekaru 15 tana 30 shi kuma yana 85, wanda kowa ya san Dan 80 ba mace ce a gaban sa ba. 

Yayin da masu goyon bayan lamarin ke ganin gara auren wuri da zinar wuri. 

Sai dai idan abinda Jaridar DAILY NIGERIAN suka ruwaito cewa, ana kiransa Chanji ne sakamakon auri-saki da ya ke yi. Wannan shine abin damuwar, domin rahoton ya kawo cewar wani ya ce "A iya sani na yayi aure kusan sha biyu wasu sun ce ashirin, shi dai ba ya zama da mace sai guda hudu, yana sakin wata zai karo wata".

In dai gaske ne haka ya ke, akwai babbar matsala dattijo mai shekaru 70 ya rika aure yana saki har ya zamana an masa lakabi da wannan halayya. A addinance Allah Ya la'anci Mace ko Namijin da suke aure kawai domin dandane. Ka auri mace idan ka gama jin dadin saduwa da ita ka saki ka auro wata. Ko mace ta rika aure tana danadana namiji ta fita ta auri wani don shima ta danadana shi. 

Auren wuri ya danganta da a ina ne kuma wanne gida ne. Kowa da Matar aurensa kamar yadda kowa ya san gidan da zai je neman aure da Inda ba zai je ba. 

Yarinya da ta yi biyayya ga Iyayenta ta auri mai shekaru 70 Allah Ya ba ta ladan hakuri da juriya na bin iyaye. Su kuma iyayen Allah Ya na kallon niyyar su ta yin hakan. Idan sun nufi Allah ne da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Allah Ya saka musu da mafi Alheri. Idan kuma sun bi son zuciya 'ya'ya amana ne daga Allah zai kuma tambaye su kiwon da Ya ba su ranar Alkiyama. 

Ga Malam Mai Chanji matukar da gaske haka ka ke ka ji tsoron Allah ka daina wannan mummunar Dabi'a. Allah ne kadai Ya san halin da iyaye ke shiga yayin da aka sako musu 'ya'ya. Da kuma su kansu matan halin da suke kasancewa a yayin zawarci. Musamman ma ga mazan da ke sakin mata su kuma ki daukar dawainiyar 'ya'yan su.
Daga Maje El-Hajeej Hotoro.

Tuesday, 11 December 2018

Cin amanar aure: An kunna faifan bidiyon matar aure da saurayinta a kotu

Cin amanar aure: An kunna faifan bidiyon matar aure da saurayinta a kotu


Wata shari'a a kotun jihar Legas dake zamanta a Ikeja ta dauki wani sabon salo bayan an nuna faifan bidiyon wata matar aure tare saurayinta suna lalata.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito labarin wata shari'a tsakanin wata matar aure da tsohon saurayinta mai 'ya'ya uku.

NAN ta rawaito cewar an nuna faifan bidiyon Peter Omokaro, tsohon saurayin matar aure, Titilayo Nosa-igiebor, a kotun domin kafa masu hujja a kan abinda suka aikata.

Faifan bidiyon mai tsawon fiye da sa'a guda ya nuna Omokaro da Titilayo kwance a kan gado suna hira kafin daga bisani su fara aikata lalatar da ta kai su dakin Otal din da suke.

Omokaro, mai shekaru 60 dake aikin banki, da Titilayo, 'yar kasuwa mai shekaru 33, sun tattauna ne a kan yadda Omokaro zai taimaketa ta samu rancen kudi a bankin da yake aiki.

Cin amanar aure: An kunna faifan bidiyon matar aure da saurayinta a kotu

Cin amanar aure: An kunna faifan bidiyon matar aure da saurayinta a kotu

Kazalika an ji lokacin da, a cikin faifan bidiyon, Omokaro, ke fadawa Titilayo cewar ba sai ta biya bashin da za a bata ba. Kazalika an gabatar da takardar yarjejeniyar da suka saka hannu kafin su fara aikata laifin da aka gurfanar da su dominsa.

Da take bayar da shaida, Titilayo ta shaidawa kotu cewar Omokaro bai bata bashin miliyan N15m din da suka amince a yarjejeniyar da suka kulla ba.

Titilayo ta kara da cewar akwai alakar kasuwanci tsakaninta Omokaro bayan kasancewar sa tsohon saurayinta.

Sai dai a nasa bangaren, Omokaro, ya musanta zargin Titilayo na cewar bai bata bashin ba kamar yadda suka amince, tare da bayyana cewar bai bata bashin a matsayin kyauta ba.

NAN ta rawaito cewar yanzu haka Omokaro da Titilayo sun amince su sulhunta kansu a wajen kotu.

Saturday, 8 December 2018

Mu na ba yara abinci mai nagarta da kayan makaranta da litattafai kyauta inji Gwamnan Kaduna

Mu na ba yara abinci mai nagarta da kayan makaranta da litattafai kyauta inji Gwamnan Kaduna




Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana irin muhimmin kokarin da Gwamnatin sa ta ke yi wajen inganta harkar ilmin Boko a fadin Jihar ta Kaduna tun da ya dare kan mulki a shekarar 2015.


Mu na ba yara abinci mai nagarta da kayan makaranta da litattafai kyauta inji Gwamnan Kaduna
Gwamna El-Rufai yace ya gyara harkar ilmi a Kaduna

Mai Girma Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa yana kashe kusan Naira Biliyan 3 a duk shekara wajen biyan kudin ‘Daliban da ke makarantun Gwamnati a fadin Jihar daga mataki na Firamare har zuwa karamin Sakandare.

Gwamnan ya bayyana wannan ne wajen wani taro da Kungiyar ZEDA ta shirya a fitacciyar Makarantar nan da ke cikin Garin Zariya watau Barewa College. Wannan ne karo na 26 da Kungiyar ZEDA ta shirya irin wannan babban taro.

Wani babban Jami’in Gwamnatin Jihar watau Alhaji Adamu Mansir, shi ne ya wakilci Gwamnan. Alhaji Mansir shi ne mai ba Gwamna El-Rufai shawara a kan harkoki na musamman da kuma abubuwan da su ka shafi mukarraban sa.

Gwamnan yace karatun mata ya zama kyauta a Jihar Kaduna har su kammala karatun Sakandare. Budu da kari kuma an inganta abincin da ake ba wadanda su ke makarantun kwana. Hadimin Gwamnan yace ba nan kadai ka tsaya ba.

Mansir ya bayyana cewa Gwamnatin Kaduna tana dinkawa ‘Dalibai kayan makaranta sannan kuma an rabawa wasun su na’urori na zamani domin inganta karatun su. Yanzu haka kuma an dauki Malaman Sakandare da-dama aiki.

A baya dai Gwamnan na Kaduna yayi wa Malamai sama da 21700 ritaya da karfi bayan sun fadi jarrabawar da aka gudanar. Gwamnan yace ta hakan ne za a samu kwararrun Malamai su na koyarwa a Jihar

Wednesday, 28 November 2018

Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari

Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari


- Kotun daukaka kara da ke Sokoto ta samu, Ciyaman din SUBEB, Murtala Adamu Jengebe da laifin karkatar da kudade

- Kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 41 sakamakon samunsa da aikata laifuka 7

 A baya, wata karamar kotu ta wanke shi daga zargin hakan yasa hukumar EFCC ta daukaka karar zuwa babban kotun da ke Sokoto

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Sokoto karkashin jagorancin mai shari'a Hannatu Sankey ta yankewa ciyaman din Hukumar Kula da Karatun Frimari na jihar (SUBEB), Murtala Adamu Jengebe hukuncin zaman gidan yari na shekaru 41.


Kotun ta yankewa Mr Jengebe hukuncin ne bayan ta same shi da laifuka bakwai cikin laifuka 10 da ake tuhumarsa da farko amma babban kotun tarayya na Gusau a jihar Zamfara ta wanke shi daga zargin.

Kotun daukaka karar tayi watsi da hukuncin da mai shari'a Habeeb Abiru na Kotun Tarayya na Gusau ya yi.

Kotun daukaka karar ta ce hukumar EFCC ta gabatar da hujjoji da suka gamsar da ita cewa ya aikata laifuka 7 cikin 10 da ake tuhumarsa da shi masu alaka da karkatar da kudade. An yanke masa hukuncin shekaru 5 a kowanne laifi guda sai dai za a lissafa shekarun zaman gidan yarin nasa a lokaci guda.

A ranar 12 ga watan Mayu, kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Gusau karkashin jagorancin mai shari'a Z.b. Abubakar ta wanke wanda ake tuhumar daga zargin aikata laifuka 10 masu alaka da karkatar da kudi.

Saboda rashin gamsuwa da hukuncin da karamar kotun tayi, hakan yasa hukumar EFCC ta daukaka karar zuwa kotun daukaka kara inda ta bukaci ayi watsi da hukuncin karamar kotun.

Sunday, 25 November 2018

Ku Kalli Hotunan Yawan Jama an Yakin Neman Zaben APC A Kano

Ku Kalli Hotunan Yawan Jama an Yakin Neman Zaben APC A Kano



Wadannan hotunan wani taron siyasa ne da aka yi a Kano inda wasu matasa 'yan Kwankwasiyya suka canja sheka daga PDP zuwa APC, me baiwa shugaban kasa shawara akan sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa wannan gwajine suka yi na gangamin yakin neman zaben shugaba Buhari da Ganduje.














Friday, 23 November 2018

An gano wata makabarta da ake binne layu a Kano

An gano wata makabarta da ake binne layu a Kano



Wasu masu kula da makabarta a jihar Kano sun tono wadansu layu da wadansu mutane ke binne wa a kaburbura a wata makabarta da ke jihar.

Wani wanda ya shafe shekara 13 yana aikin hakar kabari a makabartar Tukuntawa, Abu Gwadebe, ya shaida wa BBC yadda suke gano layun da ake binne wa a makabartar.

"Yawancin layun da abubuwan da ake binne wa a kaburburan suna dauke da wani turare wanda kunama da sauran kwari suke son kamshinsa. Saboda da haka idan muka zo da safe mu ka ga kwari ko kuda na kewaye wani wuri, to sai mu tono wurin." in ji Abu.

Uba Ibrahim shi ma ya shafe shekara 11 yana aiki a makabartar, amma shi kira ya yi ga gwamnatin da ta samar da fitilun lantarki da za su taimaka wajen rage aikata miyagun ayyuka a makabartar.

Wasu na danganta irin wadannan binne-binne a makabartu da tsafe-tsafe domin cimma wasu bukatu.

A kan samu karuwar irin wadannan al'adu ne lokacin da zabuka suka kawo jiki.

Thursday, 22 November 2018

Ango ya je daurin aurensa da harsashi a jikinsa

Ango ya je daurin aurensa da harsashi a jikinsa


'Yan sanda a kasar Indiya sun ce, wani ango ya sha rantsuwar aure duk da harbinsa da aka yi a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa inda za a daura aurensa a birnin Delhi na kasar.

Bayan harbin da wasu 'yan bindiga suka yi wa ango, an yi maza an garzaya da shi asibiti, amma sa'oi bayan an duba lafiyarsa ya ce a kai shi wajen daurin aurensa domin a kammala daurin auren, duk kuwa da kasancewar ba a cire harsashin da aka harbe shi ba a kafada.

Yanzu haka 'yan sanda sun bazama neman wasu mutum biyu da ake zargi.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da irin haka ta faru wato a bude wuta ko harbi a wajen taron daurin aure.

A shekarar watan Aprilun da ya wuce, an kashe wasu angwaye a lokacin bikinsu, sannan kuma a shekarar 2016 ma an kashe wasu angwayen.

'Yan sanda sun ce an harbi angon ne a lokacin da ya ke tare da rakiyar abokansa suna tafiya ana cashewa domin zuwa inda za a daura auren.

Likitoci dai sun tsayar da jinin da ke zuba daga jikin angon sakamakon harbin, amma kuma ba su kai ga cire harsashin ba saboda sai an yi babbar tiyata angon ya matsa zai tafi a daura aurensa.

Bayan kammala daura auren ne sai angon ya koma asibiti domin a cire masa harsashin.

BBChausa.

Wednesday, 21 November 2018

'Atiku fa karya yayiwa 'yan Najeriya shi ba maraya bane'>>Fadar shugaban kasa

'Atiku fa karya yayiwa 'yan Najeriya shi ba maraya bane'>>Fadar shugaban kasa


Fadar shugaban kasa ta hannun me baiwa shugaban kasar shawara akan akan kafafen sadarwa na zamani Lauretta Onochie ta karyata ikirarin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku abubakar da yayi na cewa ya taso a matsayin marayane kuma har tallar itace yayi.

Atiku ya bayyana hakane ranar Litinin a lokacin da yake kaddamar da yakin neman zaben shi.

Saidai da take mayar da martani akan wannan magana Onochie tace, kada fa 'yan Najeriya su yadda da maganar ta Atiku da yake cewa wai ya taso a matsayin maraya domin duk zugi ta malle ce.

Tace maraya shine wanda mahaifinshi da mahaifiyarshi suka mutu. Ta tunawa mutane da abinda Atikun ya rubuta a littafinshi me suna My Life a shekarar 2013 a shafi na 30 inda yace mahaifiyarshi ta rasu a shekarar 1984. Ta kara da cewa a lokacin Atikun yana da shekaru 38.

Kuma yakai shekarun da zai iya saiwa mahaifiyarshi gida.

Tace, menene amfanin yin irin wannan karyan? dan kawai a yaudari 'yan Najeriya dan samun tausayinsu? tace rashin girmamawane da kuma cin fuska ga 'yan Najeriya ace wani dan takara ya musu karya.

Tace yana tunanin ba zamu iya gano karyar da yayi bane? Tace tabbas zamu iya kuma shugaba Buhari ko mataimakinshi Osinbajo ba zasu taba yiwa 'yan Najeriya karyaba.
Yadda Aka Fanso Yan Tagwayen Da Akayi Garkuwa Da Su A Zamfara Da Kuma Darasin Da Muka Koya

Yadda Aka Fanso Yan Tagwayen Da Akayi Garkuwa Da Su A Zamfara Da Kuma Darasin Da Muka Koya




YADDA AKA FANSO 'YAN TAGWAYEN DA AKAYI GARKUWA DA SU A ZAMAFARA DA DARASIN DA ZAMU KOYA

Lokacin da Maigirma Sanata Kabiru Marafa ya bada tallafinshi Naira miliyon shida da sauran kudin da jama'ar Nigeria suka tallafa aka hada kudin ya kai Naira miliyon goma sha biyar, sai aka kira wadanda sukayi garkuwa da tagwayen aka sanar musu cewa kudin ya cika kamar yadda sukace a biyasu kafin su saki tagwayen, bayan an sanar da su cewa kudin ya cika sai sukace to a jirasu zasu kira don a kai musu kudin

Bayan kamar awa uku sai suka kira wayan Ibrahim mijin yayarsu wanda ake sasantawa da shi, sukace a dauko kudin azo wani gari da ake kira Gurbin-Burai inda kwanaki masu garkuwa da mutane sukayi kashe-kashe da kone-kone sukace idan an isa garin a kirasu, kafin su Ibrahim su isa garin masu garkuwa da tagwayen suna ta kiransu a waya cewa mai yasa har yanzu ba su iso ba? sun gaji da jira, su fa zasu kashe tagwayen suyi tafiyarsu sai dai azo a dauki gawarsu, Ibrahim dai yayi ta basu hakuri yana cewa mun kusan isowa

Bayan su Ibrahim sun isa garin na Gurbin-Burai suka kira masu garkuwan aka fada musu cewa sun iso garin, sai sukace to daga nan su biyo ta wani kauye da ake kira

Dumburum daga Dumburum daji za'a shiga, to su Ibrahim sai suka ajiye motarsu suka nemi mashina guda uku, sai masu garkuwan suka kira waya sukace ai mun ganku ko taho garin na Dumburum zamu fada muku hanyar da zakubi ta kawoku cikin jeji inda muke, jama'a kunga wannan ya nuna cewa akwai masu yiwa 'yan bindigar leken asiri ko ta ina a cikin wadannan garuruwa na Zamfara

Daga garin Dumburum su Ibrahim sunyi tafiya kamar tsawon kilo mita 15 a cikin jeji, suna cikin tafiya kawai sai suka fara ganin mutane da bindigogi suna ta bullowa wanda yawansu ya kai kusan mutum dari da hamsin, kuma kowa rike yake da bindiga kirar AK47 ana cewa su dakata a gurin, sai su Ibrahim suka dakata suka sauka daga kan mashina, da ma su uku ne, da shi Ibrahim mijin yayarsu, da wanda zai auri Hussaina, da babban yayansu, sai Ibrahim ya dauko kudin ya ajiye a gabansa wanda aka zuba kudin a cikin jaka guda biyu, 'yan bindigar sun gewayesu a tsakiyar jeji, bayan kamar mintuna biyu sai ga shugaban kuma ogan 'yan bindigar ya bullo tare da tawagarsa rike da manyan bindigogi tagwayen suna bayanshi

Haka shugaban barayin ya matso har kusa da Ibrahim inda kudin suke ajiye a cikin jaka a 'kasa, bai ce masa komai ba sai yayi umarni da wasu yaranshi guda biyu su bude jakan su kirga kudin, bayan sun kammala kirga kudin gaba daya ya cika miliyon 15, sai ogan yace a mayar da kudin cikin jaka a daure, da akayi haka, sai ogan barayin ya tsuguna a gaban kudin ya debi kasa da hannunshi ya watsa akan

jakakkunan kudin, sai ya mike tsaye ya hau kan jakakkunan kudin da kafafunshi, sai ya daga kanshi sama yana karanta wasu 'dalasimai irin na tsafi, yana tayi har kusan kamar mintuna 2 sai ya saukar da kanshi kasa, ya kuma sauka daga jakar kudin ya ja da baya, sai yayi umarni ga yaranshi da su dauki kudin, sai suka dauka, sai ya kalli Ibrahim yayi dariya sai yace sannunku da zuwa ashe kuna son kannenku

Sai Ibrahim ya amsa masa, sai yace ai ba wanda baya son kannenshi oga, daga nan sai yayi umarni da a kawo tagwayen ya mikasu ga Ibrahim yace su juya su tafi kar su kuskura su juya baya, Ibrahim yace mun gode oga, shine suka dauko tagwayen suka iso har kauyen Gurbin-Burai inda motarsu take, daga nan sai Ibrahim ya fara kiran waya suna sanar da 'yan uwa da wadanda suka tallafa cewa tagwayen sun kubuta lafiya

Jama'a wannan shine bayanin abinda ya faru game da yadda akaje aka karbo tagwayen.

Abinda bincikenmu ya tabbatar mana shi ne an jima ana bibiyar tagwayen domin ayi garkuwa da su, mutane da dama suna da hannu a cikin garkuwa da 'yan matan, wato nazarin da mukayi a kai shine wadannan masu aikata laifin garkuwa da mutane sun kawo wata sabuwar hanyar yin garkuwa da mutane ta hanyar bibiyar mutanen da suke mu'amala da dandalin sada zumunta na zamani musamman wadanda suke watsa hotunansu a social media, masu garkuwan suna la'akari da farin jinin wanda yake social media da yawan jama'ar da suke tare da shi wanda idan sunyi garkuwa da shi dole za'a biyasu kudi

Kunga wadannan tagwaye babban abinda yayi sanadiyyar jefa su cikin wannan bala'i shine saka hotunansu da suke yi a social media da irin yadda ake kambamasu, wadanda sukayi garkuwa da su sun dauki lokaci mai tsawo suna bin diddiginsu har zuwa ranar da tagwayen suka ziyarci garin Mahaifinsu domin su raba katin aurensu, garin kauye ne, a daren ranar da za'ayi garkuwa da su tun isarsu garin suke ta yawo, kuma duk inda suka wuce sai an nunasu, da dare yayi misalin karfe 11 da wasu mintuna akaje gidan kawarsu da suka sauka zasu kwana aka sacesu gaba daya, har da kanin mijin kawar tasu, da ita kawar tasu aka tafi dasu jeji

Muna nazarin ayyukan masu garkuwa da mutane da dabarunsu, mun sani cewa idan masu garkuwa da mutane sun kama mutum biyu ko sama da haka, to ba sa yarda su sake daya ko biyu su bar wani, a'a sai dai su sakesu gaba daya, to amma wannan sun kamasu gaba daya, sai suka saki tagwayen sauran kuma ba'a sakesu ba, wannan zai tabbatar maka da cewa masu garkuwan sunyi karfin da ya wuce tunanin duk wani mai tunani ko hasashe da nazari, kuma wannan babban kalubale ne ga gwamnatin Nigeria, mahukunta sai sunyi da gaske imba haka ba masifar zata mamaye jihohi da dama a Nigeria

Daga karshe ina kira ga 'yan mata da mazaje masu yada hotunansu a kafofin sada zumunta kuma suke da dunbin masoya da suyi taka tsantsan, sannan su kiyaye sirrin tsaron kawunansu, ku dena bayyana inda zakuje idan zakuyi tafiya, bayyanawan hatsari ne mai girma a irin wannan lokaci da muka tsinci kanmu, a dinga 6atar da kafa idan za'ayi tafiya ko za'a dawo daga tafiya

Muna rokon Allah Ya tsaremu daga dukkan sharri da makirci da mugun tarko.
Yaa Allah duk masu bibiyarmu da sharri Ko cutarwa Allah Ka mayar da sharrin da cutarwan zuwa kansu Amin

Friday, 16 November 2018

Kalli yanda gwamnan jihar Taraba yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi a makarantar yara masu nasaka>>Zai bigeka

Kalli yanda gwamnan jihar Taraba yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi a makarantar yara masu nasaka>>Zai bigeka


Gwamnan jihar Nasarawa, Umar Tanko Almakura kenan a wadannan hotunan inda yake tare da daliban makarantar yara masu fama da nakasa na jihar, ya ziyarci makarantarne dan yin murnar zagayowar ranar haihuwarshi inda ya cika shekaru 66.
Gwamnan yayi wasanni da daliban makarantar inda ya basu kayayyakin amfani irin su sanda ga makafi dadai sauransu.

Ya kuma tabbatar ma da daliban makarantar cewa makarantar zata ci gaba da gudana koda bayan ya sauka daga mulki.

Muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.






Kuyi subtriben din Chanel dinmu


Sunday, 28 October 2018

Ku Kalli yanda wata ta zana Atiku Abubakar

Ku Kalli yanda wata ta zana Atiku Abubakar


Wannan wata baiwar Allah ce da ta zana hoton dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar inda ta nuna goyon bayanta gareshi a zaben 2019.

Atikun ya gode mata ta dandalinshi na sada zumunta sannan kuma yace matasa irinta na son samun yanayin da zasu yi fice a duk sana'ar da suka zaba, ya kuma yi fatan cewa ta samu izinin yin zanen a bangon da ta yi amfani dashi.







'Yan bindiga sun sace wasu malaman addini 5 a Najeriya

'Yan bindiga sun sace wasu malaman addini 5 a Najeriya


Wasu da ake tunanin masu satar mutane ne dauke da muggan makamai sun sace wasu malaman addinin kirista biyar mata a karamar hukumar Issele-Uku, dake a jihar Delta dake a yankin kudu maso kudancin Najeriya.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, an dai sace matan ne suna kan hanyar su ta dawowa daga wurin bizne wani dan majami'ar su a kusa da hanyar jirgin kasan dake a unguwar Ika.

Legit.ng Hausa ta samu cewa 'yan bindigar sun tare motar da malaman addinin ke ciki ne sannan kuma suka yi ta harbe-harbe a sama wanda yayi sanadiyyar jikkata biyu daga cikin mutanen dake a motar kafin daga bisani su arce da biyar daga cikin su.

Kwamishinan 'yan sadan Najeriya a jihar dai Muhammad Mustafa ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan kuma ya bayar da tabbacin jami'an sa za su kubutar da su cikin kankanin lokaci.

Naij
Ga kadan daga cikin abubuwan da kuke amfani dasu kuma suna iya hana ku haihuwa a zamanin nan

Ga kadan daga cikin abubuwan da kuke amfani dasu kuma suna iya hana ku haihuwa a zamanin nan


- Ta maida hankali akan lafiyar mata da kuma basu kariya.

- Kaso 20 zuwa 25 suna fama da rashin haihuwa

- Ana matsantawa mata idan ya kasance cewa basa haihuwa



Hira da wata likita:

Kaso 20 zuwa 25 ne suke fama da rashin haihuwa a Nageriya. A wani bincike da WHO ta bayyana cewa yanayin ya kasu kashi biyu akwai Primary da Secondary.

Daga abubuwan da ka iya haifar da rashin haihuwa, harda qazanta, aiki da kwamfiyuta a cinya, ko waya a kusa da qugu, ko kuma zub da ciki ba bisa qa;ida ba.

Idan mutum ya kasance da primary tofah bazata taba haihuwa ba idan kuma secondary ne za'a iya samun da guda daya.

A yayin da mace ta samu da daya to fa zatayi kokarin kara samun daya.

A al'adun Nageriya ana mason aure yayi albarka don ganin ta haihu, idan kuma daya ne sai a dunga neman ta kara.

Da yawa suna tunanin yanda mata ke fama da matsalar rashin haihuwa,aduk sanda mace ta manyanta to kwayayen haihuwar ta sunayin rauni wanda hakan bazai basu damar karbar da ba.

Amma idan mace tanakan ganiyar ta zata iya daukar ciki a kowanne yanayi.

Naij
An kaiwa Yahudawa hari a wurin ibadar su a Amurka, an kashe da dama

An kaiwa Yahudawa hari a wurin ibadar su a Amurka, an kashe da dama



- Wani dan bindiga ya bude wuta a kan Yahudawa ma su bauta tare da kashe a kalla 4 da raunata wasu 12 kafin a kai ga kama shi

- Wasu rahotannin sun bayyana cewar adadin mutanen da su ka mutu kan iya kai wa 8

Wasu kafafen yada labarai a kasar Amurka sun bayyana wani mutum mai shekaru 46 da ake kira Rob Bowers a matsayin wanda ya kai harin


Wani dan bindiga ya bude wuta a kan Yahudawa ma su bauta tare da kashe a kalla 4 da raunata wasu 12 kafin a kai ga kama shi.

Rahotanni sun bayyana cewar dan bindigar na rera wakokin nuna kiyayyar Yahudawa lokacin da ya kai harin yau, Asabar, a birnin Pittsburgh.

Wasu rahotannin sun bayyana cewar adadin mutanen da su ka mutu kan iya kai wa 8.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi Alla-wadai da kai harin tare da nuna tsana kan Yahudawa.

An kaiwa Yahudawa hari a wurin ibadar su a Amurka, an kashe da dama
Wasu kafafen yada labarai a kasar

Amurka sun bayyana wani mutum mai shekaru 46 da ake kira Rob Bowers a matsayin wanda ya kai harin.

Wendell Hissrich, darektan kiyaye jama'a na garin Pittsburgh ya tabbatar da faruwar kai harin tare da bayyana cewar a kalla mutane 6 ne, hudu daga cikinsu jami'an'yan sanda, su ka samu raunuka.

A wani labarin na Legit.ng mai kama da wannan, kun ji cewar rahotanni sun bayyana cewar a kalla mutane biyu ne su ka rasa ransu bayan wani artabu tsakanin mabiya Shi'a da dakarun sojin Najeriya.

An samu hatsaniya tsakanin mabiya Shi'a da sojojin ne a unguwar Zuba da ke Abuja yayin da Shi'ar, daga Suleja, ke tattakin kwanaki uku (Arbaeen) zuwa Abuja.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar an samu hatsaniya ne bayan sojojin da ke aiki a kan hanyar shiga Abuja sun hana mabiya Shi'ar wucewa a daidai dutsen Zuma.

Hakann ya fusata mabiyan na Shi'a da har ta kai sun fara jifan sojojin da duwatsu, su kuma su ka bude ma su wuta, lamarin da ya kai ga asarar rayuka biyu.



Saturday, 27 October 2018

Yan Bindiga Sun Sace Yan Mata Tagwaye Da Ake Shirin Bikin Su

Yan Bindiga Sun Sace Yan Mata Tagwaye Da Ake Shirin Bikin Su


An sace wasu ‘yan mata tagwaye lokacin da suke kan hanyarsu ta kai wa ‘yan uwa da abokan arziki ankon bikinsu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Mataimakin Shugaban karamar hukumar Zurmi Abubakar Muhammad ya ce tagwayen wadanda ake shirye-shiryen aurensu suna cikin mutane bakwai da aka sace a garin Dauran da ke jihar Zamfara.
“A tsakanin ranakun Asabar zuwa Lahadi ne aka sace mutanen bakwai – wato maza hudu, mata uku.


“Nan kusa gare mu ma an sace namiji guda, mace guda wato nan Birnin Tsaba ke nan,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “A garin Moriki an ma an dauki mutum uku da wadansu da aka sace ciki har da wani kansila.”

Har ila yau ya ce an yi magana da masu garkuwa da mutanen kuma sun bukaci a “biya su naira miliyan 100 kafin su sako ‘yan tagwayen.”

Daga nan ya bukaci da a kawo musu dauki don kawo karshen matsalar.
Zamfara tana daya daga cikin jihohin arewacin kasar da ke fama da matsalar tsaro.

BBC HAUSA

Thursday, 25 October 2018

Kalli yanda makiyaya suka cika birnin Madrid na kasar Sifaniya da dabbobinsu a wani bikin da aka yi

Kalli yanda makiyaya suka cika birnin Madrid na kasar Sifaniya da dabbobinsu a wani bikin da aka yi


Wadannan hotunan wasu makiyayane da suka shiga birnin Madrid na kasar Andulus, sun shiga garinne a matsayin wani biki da ake yi duk shekara na tunawa da hijirar da makiyaya ke yi da dabbobinsu a zamanin da kamin kasar ta ci gaba haka.

Makiyayan da suka fito daga yankunan karkara sun bi hanyoyin da iyaye da kakanni suka bi a da na cikin birnin yayin wannan hijira da suke yi da dabbobin nasu a shekarun baya.

Jama'ar gari sun fito suna kallo don nishadi.

Buzzfeed.