Sunday, 28 October 2018




An kaiwa Yahudawa hari a wurin ibadar su a Amurka, an kashe da dama

Home An kaiwa Yahudawa hari a wurin ibadar su a Amurka, an kashe da dama

Anonymous

Ku Tura A Social Media


- Wani dan bindiga ya bude wuta a kan Yahudawa ma su bauta tare da kashe a kalla 4 da raunata wasu 12 kafin a kai ga kama shi

- Wasu rahotannin sun bayyana cewar adadin mutanen da su ka mutu kan iya kai wa 8

Wasu kafafen yada labarai a kasar Amurka sun bayyana wani mutum mai shekaru 46 da ake kira Rob Bowers a matsayin wanda ya kai harin


Wani dan bindiga ya bude wuta a kan Yahudawa ma su bauta tare da kashe a kalla 4 da raunata wasu 12 kafin a kai ga kama shi.

Rahotanni sun bayyana cewar dan bindigar na rera wakokin nuna kiyayyar Yahudawa lokacin da ya kai harin yau, Asabar, a birnin Pittsburgh.

Wasu rahotannin sun bayyana cewar adadin mutanen da su ka mutu kan iya kai wa 8.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi Alla-wadai da kai harin tare da nuna tsana kan Yahudawa.

An kaiwa Yahudawa hari a wurin ibadar su a Amurka, an kashe da dama
Wasu kafafen yada labarai a kasar

Amurka sun bayyana wani mutum mai shekaru 46 da ake kira Rob Bowers a matsayin wanda ya kai harin.

Wendell Hissrich, darektan kiyaye jama'a na garin Pittsburgh ya tabbatar da faruwar kai harin tare da bayyana cewar a kalla mutane 6 ne, hudu daga cikinsu jami'an'yan sanda, su ka samu raunuka.

A wani labarin na Legit.ng mai kama da wannan, kun ji cewar rahotanni sun bayyana cewar a kalla mutane biyu ne su ka rasa ransu bayan wani artabu tsakanin mabiya Shi'a da dakarun sojin Najeriya.

An samu hatsaniya tsakanin mabiya Shi'a da sojojin ne a unguwar Zuba da ke Abuja yayin da Shi'ar, daga Suleja, ke tattakin kwanaki uku (Arbaeen) zuwa Abuja.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar an samu hatsaniya ne bayan sojojin da ke aiki a kan hanyar shiga Abuja sun hana mabiya Shi'ar wucewa a daidai dutsen Zuma.

Hakann ya fusata mabiyan na Shi'a da har ta kai sun fara jifan sojojin da duwatsu, su kuma su ka bude ma su wuta, lamarin da ya kai ga asarar rayuka biyu.



Share this


Author: verified_user

0 Comments: