Showing posts with label Hausa News. Show all posts
Showing posts with label Hausa News. Show all posts

Monday, 24 December 2018

Thursday, 13 December 2018

Babu dan takarar da zai iya kayar da Buhari>>Honorabul Kazaure

Babu dan takarar da zai iya kayar da Buhari>>Honorabul Kazaure


Dan majalisar tarayya, Honorabul Muhammad Kazaure ya bayyana cewa babu dan takarar da zai iya kayar da shugaban kasa, Muhammafu Buhari a zaben 2019.


Kazaure ya bayyana hakane a ganawar da shugaba Buhari yayi da kungiyar magoya bayanshi inda yace, a kaf cikin 'yan takarar shugaban kasar da ake dasu babu wanda zai iya kayar da shugaba Buhari.
Yan Najeriya na kashe naira tiriliyan 1 kowace shekara wajen tafiya karatu kasashen waje>>Tsohon Shugaban Jami’a

Yan Najeriya na kashe naira tiriliyan 1 kowace shekara wajen tafiya karatu kasashen waje>>Tsohon Shugaban Jami’a


Shugaban Jami’ar Crawford, kuma tsohon Shugaban Jami’ar Lagos, Farfesa Oye Ibidapo-Obe, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na kashe akalla naira tiriliyan 1 duk shekara wajen tafiya karatun digiri kasashen waje.


Farfesan ya fadi haka ne jiya Laraba, a lokacin da ya ke jawabi a bikin yaye dalibai karo na 10 na Jami’ar Crawford da ke garin Igbesa, jihar Ogun.

Ya fallasa yadda ake kashe wadannan makudan kudade ne, daidai lokacin da majalam jami’o’in Najeriya ke ci gaba da gudanar da yajin aikin da suka fara tun daga ranar 4 Ga Nuwamba.

Daga nan ya ci gaba da nuna muhimmancin ci gaba da kafa jami’ao’i masu zaman kan su wadanda ba na gwamnati ba Najeriya.

Ya ce ta haka ne za su kara samun ingancin da za a rage karakainar neman karin ilmi a kasashen duniya, inda ake kwasar makudan kudade ana tafiya da sunan tafiya karin ilmi.

Premiumtimeshausa.

Wednesday, 12 December 2018

YAWAN SHEKARUN KO AURI-SAKIN?

YAWAN SHEKARUN KO AURI-SAKIN?


Labarin Magidanci a garin Lapai da ke jihar Neja, Yakubu Chanji, ya auri budurwa 'yar shekara 15. Ya zama babban labarin da ya janyo muhawara gami da cece-kuce. 


A ra'ayin wasu na ganin morewar budurwa ta auri saurayi da karfinsu ya zo daya zai nuna mata soyayya da wasanni. Amma Dan shekara 70 ya auri 'yar 15 tazarar shekaru 55 sun yi matukar yawa. A lokacin da mace ta kai 30 ne ta ke kan ganiyar bukatar kusancin da Namiji. Hakan na nufin a yayin da ta kara shekaru 15 tana 30 shi kuma yana 85, wanda kowa ya san Dan 80 ba mace ce a gaban sa ba. 

Yayin da masu goyon bayan lamarin ke ganin gara auren wuri da zinar wuri. 

Sai dai idan abinda Jaridar DAILY NIGERIAN suka ruwaito cewa, ana kiransa Chanji ne sakamakon auri-saki da ya ke yi. Wannan shine abin damuwar, domin rahoton ya kawo cewar wani ya ce "A iya sani na yayi aure kusan sha biyu wasu sun ce ashirin, shi dai ba ya zama da mace sai guda hudu, yana sakin wata zai karo wata".

In dai gaske ne haka ya ke, akwai babbar matsala dattijo mai shekaru 70 ya rika aure yana saki har ya zamana an masa lakabi da wannan halayya. A addinance Allah Ya la'anci Mace ko Namijin da suke aure kawai domin dandane. Ka auri mace idan ka gama jin dadin saduwa da ita ka saki ka auro wata. Ko mace ta rika aure tana danadana namiji ta fita ta auri wani don shima ta danadana shi. 

Auren wuri ya danganta da a ina ne kuma wanne gida ne. Kowa da Matar aurensa kamar yadda kowa ya san gidan da zai je neman aure da Inda ba zai je ba. 

Yarinya da ta yi biyayya ga Iyayenta ta auri mai shekaru 70 Allah Ya ba ta ladan hakuri da juriya na bin iyaye. Su kuma iyayen Allah Ya na kallon niyyar su ta yin hakan. Idan sun nufi Allah ne da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Allah Ya saka musu da mafi Alheri. Idan kuma sun bi son zuciya 'ya'ya amana ne daga Allah zai kuma tambaye su kiwon da Ya ba su ranar Alkiyama. 

Ga Malam Mai Chanji matukar da gaske haka ka ke ka ji tsoron Allah ka daina wannan mummunar Dabi'a. Allah ne kadai Ya san halin da iyaye ke shiga yayin da aka sako musu 'ya'ya. Da kuma su kansu matan halin da suke kasancewa a yayin zawarci. Musamman ma ga mazan da ke sakin mata su kuma ki daukar dawainiyar 'ya'yan su.
Daga Maje El-Hajeej Hotoro.

Tuesday, 11 December 2018

Cin amanar aure: An kunna faifan bidiyon matar aure da saurayinta a kotu

Cin amanar aure: An kunna faifan bidiyon matar aure da saurayinta a kotu


Wata shari'a a kotun jihar Legas dake zamanta a Ikeja ta dauki wani sabon salo bayan an nuna faifan bidiyon wata matar aure tare saurayinta suna lalata.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito labarin wata shari'a tsakanin wata matar aure da tsohon saurayinta mai 'ya'ya uku.

NAN ta rawaito cewar an nuna faifan bidiyon Peter Omokaro, tsohon saurayin matar aure, Titilayo Nosa-igiebor, a kotun domin kafa masu hujja a kan abinda suka aikata.

Faifan bidiyon mai tsawon fiye da sa'a guda ya nuna Omokaro da Titilayo kwance a kan gado suna hira kafin daga bisani su fara aikata lalatar da ta kai su dakin Otal din da suke.

Omokaro, mai shekaru 60 dake aikin banki, da Titilayo, 'yar kasuwa mai shekaru 33, sun tattauna ne a kan yadda Omokaro zai taimaketa ta samu rancen kudi a bankin da yake aiki.

Cin amanar aure: An kunna faifan bidiyon matar aure da saurayinta a kotu

Cin amanar aure: An kunna faifan bidiyon matar aure da saurayinta a kotu

Kazalika an ji lokacin da, a cikin faifan bidiyon, Omokaro, ke fadawa Titilayo cewar ba sai ta biya bashin da za a bata ba. Kazalika an gabatar da takardar yarjejeniyar da suka saka hannu kafin su fara aikata laifin da aka gurfanar da su dominsa.

Da take bayar da shaida, Titilayo ta shaidawa kotu cewar Omokaro bai bata bashin miliyan N15m din da suka amince a yarjejeniyar da suka kulla ba.

Titilayo ta kara da cewar akwai alakar kasuwanci tsakaninta Omokaro bayan kasancewar sa tsohon saurayinta.

Sai dai a nasa bangaren, Omokaro, ya musanta zargin Titilayo na cewar bai bata bashin ba kamar yadda suka amince, tare da bayyana cewar bai bata bashin a matsayin kyauta ba.

NAN ta rawaito cewar yanzu haka Omokaro da Titilayo sun amince su sulhunta kansu a wajen kotu.

Saturday, 8 December 2018

Mu na ba yara abinci mai nagarta da kayan makaranta da litattafai kyauta inji Gwamnan Kaduna

Mu na ba yara abinci mai nagarta da kayan makaranta da litattafai kyauta inji Gwamnan Kaduna




Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana irin muhimmin kokarin da Gwamnatin sa ta ke yi wajen inganta harkar ilmin Boko a fadin Jihar ta Kaduna tun da ya dare kan mulki a shekarar 2015.


Mu na ba yara abinci mai nagarta da kayan makaranta da litattafai kyauta inji Gwamnan Kaduna
Gwamna El-Rufai yace ya gyara harkar ilmi a Kaduna

Mai Girma Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa yana kashe kusan Naira Biliyan 3 a duk shekara wajen biyan kudin ‘Daliban da ke makarantun Gwamnati a fadin Jihar daga mataki na Firamare har zuwa karamin Sakandare.

Gwamnan ya bayyana wannan ne wajen wani taro da Kungiyar ZEDA ta shirya a fitacciyar Makarantar nan da ke cikin Garin Zariya watau Barewa College. Wannan ne karo na 26 da Kungiyar ZEDA ta shirya irin wannan babban taro.

Wani babban Jami’in Gwamnatin Jihar watau Alhaji Adamu Mansir, shi ne ya wakilci Gwamnan. Alhaji Mansir shi ne mai ba Gwamna El-Rufai shawara a kan harkoki na musamman da kuma abubuwan da su ka shafi mukarraban sa.

Gwamnan yace karatun mata ya zama kyauta a Jihar Kaduna har su kammala karatun Sakandare. Budu da kari kuma an inganta abincin da ake ba wadanda su ke makarantun kwana. Hadimin Gwamnan yace ba nan kadai ka tsaya ba.

Mansir ya bayyana cewa Gwamnatin Kaduna tana dinkawa ‘Dalibai kayan makaranta sannan kuma an rabawa wasun su na’urori na zamani domin inganta karatun su. Yanzu haka kuma an dauki Malaman Sakandare da-dama aiki.

A baya dai Gwamnan na Kaduna yayi wa Malamai sama da 21700 ritaya da karfi bayan sun fadi jarrabawar da aka gudanar. Gwamnan yace ta hakan ne za a samu kwararrun Malamai su na koyarwa a Jihar

Wednesday, 28 November 2018

Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari

Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari


- Kotun daukaka kara da ke Sokoto ta samu, Ciyaman din SUBEB, Murtala Adamu Jengebe da laifin karkatar da kudade

- Kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 41 sakamakon samunsa da aikata laifuka 7

 A baya, wata karamar kotu ta wanke shi daga zargin hakan yasa hukumar EFCC ta daukaka karar zuwa babban kotun da ke Sokoto

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Sokoto karkashin jagorancin mai shari'a Hannatu Sankey ta yankewa ciyaman din Hukumar Kula da Karatun Frimari na jihar (SUBEB), Murtala Adamu Jengebe hukuncin zaman gidan yari na shekaru 41.


Kotun ta yankewa Mr Jengebe hukuncin ne bayan ta same shi da laifuka bakwai cikin laifuka 10 da ake tuhumarsa da farko amma babban kotun tarayya na Gusau a jihar Zamfara ta wanke shi daga zargin.

Kotun daukaka karar tayi watsi da hukuncin da mai shari'a Habeeb Abiru na Kotun Tarayya na Gusau ya yi.

Kotun daukaka karar ta ce hukumar EFCC ta gabatar da hujjoji da suka gamsar da ita cewa ya aikata laifuka 7 cikin 10 da ake tuhumarsa da shi masu alaka da karkatar da kudade. An yanke masa hukuncin shekaru 5 a kowanne laifi guda sai dai za a lissafa shekarun zaman gidan yarin nasa a lokaci guda.

A ranar 12 ga watan Mayu, kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Gusau karkashin jagorancin mai shari'a Z.b. Abubakar ta wanke wanda ake tuhumar daga zargin aikata laifuka 10 masu alaka da karkatar da kudi.

Saboda rashin gamsuwa da hukuncin da karamar kotun tayi, hakan yasa hukumar EFCC ta daukaka karar zuwa kotun daukaka kara inda ta bukaci ayi watsi da hukuncin karamar kotun.