Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana irin muhimmin kokarin da Gwamnatin sa ta ke yi wajen inganta harkar ilmin Boko a fadin Jihar ta Kaduna tun da ya dare kan mulki a shekarar 2015.
Mu na ba yara abinci mai nagarta da kayan makaranta da litattafai kyauta inji Gwamnan Kaduna
Gwamna El-Rufai yace ya gyara harkar ilmi a Kaduna
Mai Girma Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa yana kashe kusan Naira Biliyan 3 a duk shekara wajen biyan kudin ‘Daliban da ke makarantun Gwamnati a fadin Jihar daga mataki na Firamare har zuwa karamin Sakandare.
Gwamnan ya bayyana wannan ne wajen wani taro da Kungiyar ZEDA ta shirya a fitacciyar Makarantar nan da ke cikin Garin Zariya watau Barewa College. Wannan ne karo na 26 da Kungiyar ZEDA ta shirya irin wannan babban taro.
Wani babban Jami’in Gwamnatin Jihar watau Alhaji Adamu Mansir, shi ne ya wakilci Gwamnan. Alhaji Mansir shi ne mai ba Gwamna El-Rufai shawara a kan harkoki na musamman da kuma abubuwan da su ka shafi mukarraban sa.
Gwamnan yace karatun mata ya zama kyauta a Jihar Kaduna har su kammala karatun Sakandare. Budu da kari kuma an inganta abincin da ake ba wadanda su ke makarantun kwana. Hadimin Gwamnan yace ba nan kadai ka tsaya ba.
Mansir ya bayyana cewa Gwamnatin Kaduna tana dinkawa ‘Dalibai kayan makaranta sannan kuma an rabawa wasun su na’urori na zamani domin inganta karatun su. Yanzu haka kuma an dauki Malaman Sakandare da-dama aiki.
A baya dai Gwamnan na Kaduna yayi wa Malamai sama da 21700 ritaya da karfi bayan sun fadi jarrabawar da aka gudanar. Gwamnan yace ta hakan ne za a samu kwararrun Malamai su na koyarwa a Jihar
0 Comments:
Post a Comment