Saturday, 11 August 2018




Ahmad Musa ya samu kyakkyawar tarba daga larabawan kasar Saudiyya

Home Ahmad Musa ya samu kyakkyawar tarba daga larabawan kasar Saudiyya

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya watau Super Eagles mai suna Ahmad Musa ya bayyana matukar jin dadin sa da irin kyakkyawar tarbar da ya samu daga larabawan Saudiyya.
Idan ba'a manta ba fitaccen dan kwallon dai mai shekaru 25 a duniya ya sauya kungiyar kwallon sa ne ta Leicester City ya zuwa kungiyar kwallon Al-Nassr dake a kasar ta Saudiyya.

NAIJ.com ta samu cewa sai da jim kadan da saukar sa a kasar ta Saudiyya ne sai kawai cincirindon masoya kwallo musamman ma na sabuwar kungiyar ta sa suka zagaye shi suna murnar komawar tasa.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa fitaccen dan wasan tauraruwar sa ta haska sosai a gasar cin kofin duniya da ya gabata a kasar Rasha inda ya samu zura kwallaye biyu ringis a lokacin da Najeriya ta kara da kasar Iceland.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: